← Book details Ana Dara Ga Dare Yayi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 237 OF 337

Sashe 237

Ana Dara Ga Dare Yayi Part 1 Complete Hausa Novel · about 11 min read

ZAINAB IDRIS MAKAWA

ANA DARA GA , , , , , , , ,

8️⃣0️⃣ BY, , , , , , , , , , , ,

ZAINAB IDRIS MAKAWA, , , , , , , , , , ,

BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM AL WAHID , , , , , , , , ,

ONLINE PAID NOVEL YAR UWA KI BIYA KI KARANTA A CIKIN SALAMA BA TARE DA HAKKIN KOWA BA DON BIYA KI TURA DARI BIYAR 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK 08036959257

ALLAH SARKI AI RAINA BAYA BACI YANZU DON KIN FITAR DON NASAN AKWAI RANAN HADUWA SEE U👋👋👋👋

Da yamman ranan muka koma gidan mu duk da aiken da daddy yayowa yaya Abubakar wurin mu cewa yana son ya gana damu a ranan hakan baisa mun je gunshi ba.
Don umma ta hana muje a cewan ta me zai fada muna kuma yanzu bayan baiso haka ya kasance da muba ya boyewa yan uwa baiyanan mu don rufuwar asirinshi shi.
Gashi tun faruwan hakan gaba daya ya Abubakar ya sauya kallo daya zakai mai ga duk wanda ya sanshi ka gane cewa yana cikin wani halin damuwa a zuciyar shi .
Don ya fada hasken nan nasa na gado ya dan dushe yayi baki ga gashi daya bari kadan a fuskan shi ko kana magana dashi sai ya tafi tunane ya barka nan.
Rashin zuwa dani aiki ranan yasa oga yaji halin da nake ciki inda sukai mai dan bayani briefly yasa yaji tausayin mu a zuciyar shi.
A can ma dai gidan Alh nuhu da suka kwaso shi daga asibiti cewan shi ciwonshi ai bana asibiti bane yasa suka dawo gida kowa na zuwa wurin malamai da bokaye ana karbowa ana dura mashi ko a shafeshi ko a turara mai yaki yayi ta tari.
Yau ko da uwargidan shi ta shiga dakin don duba halin da yake ciki don sunje sallah sai samun shi tayi ya falka yana bin ko ina da kallo na dakin.
Yana ganin ta yaso ya yun kura ya tashi a cikin mamaki sai kuma ya kasa don jikin da sauran nauyi a lokacin sai binta ya kamayi da kallo.
Juyawa tayi a guje ta fita a kofan falon ta tsaya tana fadi cikin daga murya tana fadi ku fito Alh ya tashi Alh ya bude idon shi.
Ai a guje kowa ke fitowa daga dakin shi zuwa wajen su har yaran dake wajen suka cika dakin lokaci guda ana faman mashi sannu da jikin kowa da mamaki a zuciyar shi.
Waya aka fara bugawa yan uwa da abokan arziki cewa Alh ya falka nan aka shiga shati fadi cewa maganin da akayi mai na karshe ne ya karbeshi.
Sai zuwan Alh gyade ne zancen ya canza don yana shigowa dakin dan uwan nasa dake makil da mutane ya tsaya a kofa yana fadin .
Ehh lalai kuwa ya tabbata yarinyar nan manyace ta gaske ashe don gashi ya tabbata a zahiri mun sheda .
Haka yasa kowa na dakin yake binshi da kallon mamaki karara a fuskan shi yaci gaba da fadin cewan da tayi muje ai ya tashi ko zancen gashi ya tabbata.
Haka baffa buhari daya iso shima cewa yayi tabbas babu sarki sai Allah Annabin mu Annabi mohammadu manzon shine .
Lalai Allah da Annabin shi suyi gaskiya koce babu Aljani a duniyan nan yai karya wallahi yanzu zancen yarinyar nan ya tabbata gaskiya ashe ko gaba da gaban ta a cikin wani aikin ke nan.
Nan kuma zance ya fara tashi kus kus a cikin yan uwa da abokan arziki an dai samu ya tashi har yai wanka yaci abinci sosai saidai jikin nasa da ba karfi har lokacin.
Sai lokacin ya samu zama da yan uwan shi har aminan shi biyu da matan shi yana tambayan su abinda ke faruwa suka fara fada mai abinda suka sani ya faru.
Har zuwa irin rikicin gida da nazo akayi dani da kuma zancen zaman su dani a safiyan jiya din da komai dana fada masu a falin mijin gwaggo hari har cewan nice sabbabin rike masa kafafun shi gyaden.
Shiru Allah Nuhu yayi yana sauraron abinda kowan su ke fadi a lokacin har suka gama yace akwai aiki a gaban mu sosai ke nan saidai nan na sheda yarinyar nan bata tunkaromu ba saida ta shirya muna tsab kafin tazo garemu.
Sai kuma ya murmusa kafin yace waini ce karamar yarinya a yanzu take shirin challanges dina don tana takama da guntun sihirin ta ko ?
Alh nidai tunda kaga haka wallahi abi abin nan a sannu uwargidan ta fada ya hararo ta don sai lokacin suka kulla da cewa ai suna kusa irin wanan zancen ba ayin shi a gaban mata.
Juyowa yayi cikin su a fusace yana fadin ku me kukeyi a nan da zakuzo ku wani zauna muna muna magana kan abinda mu ya shafa.
Biyun kan mikewa sukayi sai uwargidan ne da hjy salma a zaune da take binshi da wani irin kallon tsana da Allah waddan halin ka.
Can ta mike tana fadin lalaikan kai ya shafa Alh don ka shafa muna kashin kaji a jiki duk inda muka bi da yaran mu sai an nuna mu a matsayin naka yanzu.
Tana fadin haka ta juya ta fara tafiya yace ehh salma kikai kuwa yanzu tunda har zaki iya mayar min da martani haka kuwa amma zanyi maganin ki ita dai bata juyi ba ta fice.
Sai bayan fitan sune suka fara bashi labarin abinda ya daga mai hankali wanda bai dauka wani ya taba sani ko zaiji ba sai gashi a bakina yanzu yaji.
Kai ya girgiza yana lumshe idanuwan shi cikin takaici kafin ya bude idanun karo na biyu da a yanzu sun rikede zuwa ja ya furzo da iska daga bakin mai dan sauti yana fadin.
Yanzu na gama fahintar yarinyar nan kaf saidai ance wanda ya rigaka barci dole yake rigaka tashi ita yanzu ta soma muko min dade muna wanan.
Dadai mun barta mu bata dukkan abinda take nema kawai a rabu lafiya zaifi ina amfanin wanan tonun silar da mukeyi a tsakanin mu dasu.
Wani kallon zargi yake jifan dan uwan nasa dashi kafin yace ashe kai sakaran banzane yarinyar nan fa tazo da zuman kota halin kaka saita kaimu kasa a cikin garin nan.
Don muna sakarkkaru sai muyi zaune muko mu zuba mata ido ke nan tayi galaba a kan mu muna kallo kome kake son fada yanzu ?
Gaba dayan ku kubani kunnuwan ku kuje me zan fada maku nan ya kitsa masu duk yadda komai zai kasance idan anje kotu ga jibi banda goben sukace sun gane komai don dole haka zasu bishi din sai abinda yace dasu dole zasu bi.
Wanka na fito ina zaune gaban mirrow ina shafa mai a jiki wayana dake saman gadon ya dauki kira mikewa nayi na dauko wayan a inda yake aje saman gadon.
Duban layin nayi Abdul ne makwabcin mu kuma abokin aikina a lokacin mun gaisa yake tambaya su umm da ammar nace lafiya suke yake fadin gasu sun sauka kaduna a wanan gidan namu dai muke zaune ko nace eh.
Kaya mukazo saka hannu zamu kwana a nan nayi masu sannu da hanya don nasan aikin sane hakan saina dauka shi kadaine ko su biyu a lokacin saidai ban tambaya ba.
Bayan na fito ne nake fadawa umma zuwan shi take fadin gashi kuma ba zasu samemu a gida ba don yau fitan mu kotu na farko don haka dole muje cikin lokaci.
Karyawa mukayi tare da duk daukan wani abinda zamu bukata muka fito zuwa kotun a karo na farko da zamu shiga ke nan.
Har nakai bakin mota na juyo nacewa umma mu taka zuwa titi ba zamu shiga wanan motar ba sam a yanzu kallona umma tayi ina tafiya ina waya muka fita get din mu bamu dade da tsayuwa ba saiga mota an turo muna muka shiga.
Tun daga nisa na hango yadda wanan wurin ya cika da motoci wanda nasan na yan uwan mune mafi yawan motocin dake wanan waje duban lokaci nayi saura minti uku a fara yasa nace muyi zaman mu a motan kada mu fita.
Gashi ba mai ganemu don motar mai duhun glassce har wasu samari sukazo suka wuce wa yanda ba zan iya shedasu ba suna fadin wai ance ai kamar yarinyar nan taji tsoro ba zata zo ba kuma.
A to kai baba Alh na wasa ne ya gama ta da allon karfensa ya saka mata razana ta gudu kila itama ai rashin sani ne ya cuce ta.
Allah ya taimaka driver ya bude kofan shi yana shan iska muke tsinkayo zancen su daga inda suke tsaye a kusa damu .
Lokacin yana cika nace mu fita muka fito daga cikin motan muka nufi hanyar shiga wurin a lokacin har alkalin ya fara magana kan shari,an namu ko muka shigo don wani shari a akeyi kafin namu zaman.
Muna neman Sahiba sambo namadi da tai karan Alh Nuhu Allah gyade da buhari namadi duk yan uwan mahaifin ta.
Ko Sahiba na kusa ta gabata gaban mai shari,a na amsa da na,am gani sai lokacin kowa yasa muna wurin suka juyo a cikin mamaki karara a fuskokin su suna kallona.
Alh Nuhu da wanan ne karon shi na farko daya fara ganina shi ido ya kura min har nazo inda ake tsayi na tsaya ina kallon kowa idanu bushe.
Jikina dogon rigace a lokacin na yan kasan Mexico kinsan irin rigunan su ga kyau amma kuma dole akwai nakasu a dinki da bai dace da yar bahaushe ba.
Hakana saka don nasan zasuyi magana don kawai in nuna masu nifa ni dince da akwai bariki da komai a tare dani.
Mai gabatar da kara ya fara fadin abinda karan ya kunsa aka nemi su Alh nuhu da sufito sai gasu da babban riga ruuuuu sun fito suna fuskantar mai shari,a din sai wani cicika suke suna batsewa in ka debe mutum daya da fuskan shi ya nuna damuwa karara.
Tambayan su aka fara suka gabatar da sunayen su sai mai magana yake fadin ko sun san da wanan kalubalin da ake tuhuman su dashi ?
Alh nuhu yace su basu sanda hakan ba asalima basu san nidin ko wacece ba don haka basu san zancen da nake magana a kanshi ba yanzu.
Aka juyo wurina ana tambaya a daidai lokacin da yan tawagan mu suka karaso cikin kotun hakan ya mayar da hankalin mutane wurun kallon su din kowa sai yake zaton lauyoyine ko wasu bakin yan sa ido.
Mai maganan ya dan je wurin alkalin sukai kus,kus dashi kafin a juyo da zance a wurina suna fadin naji ko ina da lauya da zai kareni ?
Kafin nayi magana can ya dago hannu yana fadin gashi tare da gabatar da kanshi shine lauyan da zai kareni .
Aka juya wurin su Alh suma nasu lauyan ya mike yace shine mai kare bangaresu nan kotu ya fara aka bawa mai kareni dama mutumin da bansan inda ya fito ba sai a wanan ganin da nayi mai don har yaya Abubakar yazo da lauya wani abokin shine da ya kware shima wurin sharia.
Jin babban lauya da kasa ta sani a bayana yada har Alkalin ya fara kama kanshi a lokacin tambayan su yayi da cewa ko sun san dan uwan su daya mutu shekara goma sha biyar daya wuce ?
Mai karesu yace wanan tambayan ai batayi daidai ba gaskiya Alkali yace a barshi yayi ya kara maimaita tambayan sukacw sun sanshi dan uwan sune mahaifin su daya saidai uwa kowa da nasa uwar.
Yace da kyau shin ko kunsan yana da mata da ya a lokacin suka kalli juna kafin da sauri Alh gyade dake dan dogara sandan shi yace munsan da hakan.
Au to kuma kukace da farko baku san wanan zancen ba mai karesu ya daga don nema masu kariya a wurin shi yace an bashi a bar wanan tambayan shima aka bashi dama ya juyo gareni.
Ke kin taba ganin su kin san su a matsayin su na yan uwa gun mahaifin ki kema kuma ya a garesu nace na sansu mana amma da yake su basu nemeni ba kamar yadda mahaifina ya bar masu amanan mu nima kuma din ban nemesu ba kamar yadda suka sheremu a cikin duniya.
Au to baki nemesu ba tsawon wanan lokacin yanzu kuma da zaki nemesu sai kika nemesu a kotu ke nan ko ?
Hannu mai kareni ya daga kai an fafata sosai wanan yace wanan wanan yace wancan a karshe aka ce meye hujjana na tuhuman su da kissan mahaifina da kuma neman dukiyana da ban tunkaresu ba sai kotu ?
Nan suka tsaya ja inja har Alkali ya dan doki gudumar shari,a yayi gyara yana fadin kotu ta dage wanan karan sai nan da sati biyu mai zuwa tare da bani daman zuwa da hujjana na fadan hakan.
Nan aka fara fita daya bayan daya ga text din Adnan cewa kada in nuna ai tare muke haka yasa na fito muka koma wanan motan su kafin ma in fito har sun riga da sun shiga motocin su sun bar haraban kotu din lokacin.
Mun tsaya mun gaisa da yan uwan da basu da tsoro wasu kan tuni suka karawa talkaman su mai suk bace a wurin don sanin halin Alh nuhu din wurin iya baraza da rayukansu din.
Zagi kan nasha shi a motan da suka shiga sai can suka samu lauyan su da fada wai su ai sunso ya gama komai daga ranan nan alkali ya sallami karan namu ne.
Waiko kai Alh bello ka tabbatar da kaga Alkalin nan kuwa ya juyo yana kallon shi don son jin amsan da zai bashi a lokacin .
Yace komai kamar yadda ka tsara haka na shimfida mashi saidai kila wani hikimace nasu haka yasa ya daga karan a yau din.
Wayan shi ce tayi kara kamar kada ya dauka amma kuma ya daure ya dauka don sanin halin da suke ciki din ko wani zancen ne zaiji a kaina.
Muryan da yajine ana gargadin shi kan gobe ya tabbatar yana Abuja don case din dake can yana jiran shi.
Wani irin tsuki yaja tare da fadin anya yarinyar nan zan iya mata hakkurin wani abu a rayuwan ta kuwa din na tabbatar idan nayi wasa zata shige min hanci da kudundune a garin nan.
Chapter 237 · 0% Book details