← Book details Ana Dara Ga Dare Yayi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 209 OF 337

Sashe 209

Ana Dara Ga Dare Yayi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

su muniya wurn buki don nasan bana gida yasa na yarda da tafiyan su din tare saboda hakan yafi kwantar min da hankali. Wani mamakine ya kama kowan su lokacin da wanda suka sama yake fada masu cewa ayyah ai basa nan sun tafi America tun jiya nan gaba dayan su. Kara maimaita sunan baffah Hamza yayi yana gyada kai yace America kuma yana kallon Abubakar dashi ma yake mamakin hakan . Ikon Allah yaushe har mutanen nan suka bunkasa haka kowa bai sani ba lamarin daga Allah ne Abubakar daya shiga motan karshe yake fadi. Baiwane kawai na ubangiji don Ita babban Allah yai mata wani baiwa a rayuwan ta wanda ba zan iya fadi ba a yanzu saidai idan kun ganta zaku gane hakan . Kallon juna sukayi sunzo da niyar kwana garin saidai rashin samu yasa suka koma a ranan basu kwana ba a can gida kuma suke jin labarin cewa ai yarinyar da tayi karan Alh Nuhun an nemeta don ayi sulhu ba sai anje kotu ba wai tayi tafiya zuwa kasan waje bata kasan. Baffa Abdullahine shi baffa hamza kallon juna sukayi tare da fadin kai anya ba yar nan tamu bane kuwa keda wanan aikin don yanzu haka bata kasan nan tayi tafiya itama zuwa America. Sun tatauna sosai haka labarin ya fara tafiya ai ana ganin dai yarinya dayace tazo tana juya su Alh din haka har wanan zancen ya shiga kunnen su Nabila dake zaune falon lokacin da mommy take wayan. America suka fada suna kallon juna ita da hauwa kafin suce wai Amerrica duk da ta samu aiki har wani girma da wani matsayine zaikaita wanan kasan. Mutane akwai karawa zance gishiri wallahi yanzu an shiga fadin zantuka ke nan barkatai har sai ranan da gaskiya zatayi halin ta ai Nabila ta fada tana jan tsuki a fili. Faiza dake zaune tana jin su haushi da mamakin su ya rufeta lokaci guda kasa masu magana tayi a lokacin sai mayar da hankalinta da tayi kan wayan ta sosai a lokacin. Mun samu taro na musan man a wurin su duk da hotel ne aka sauke mu a lokacin Turkeya mun huta sosai don tunda na shiga na rama sallolin dake kaina a lokacin nabi lafiyan gadon dakin da aka saukeni a ciki. Barci sosai nayi don har sunci abinci ogan mu ya shigo yagana dasu yayi masu bangajiya a lokacin sun gaisa dashi ya tafi. Washe gari kuma ya dawo da rana don ba hotel daya muka sauka dashi ba shida mahaifiyar shi a wani shahararen hotel na kasan Turkish ya saukashi . Zamu kwana biyu a garin don akwai abinda zaiyi a nan din kafin a kwasa zuwa wurin abinda ya kawomu na sister din nasa. Karfe hudu da rabi zamu halarci wani wuri da zamu gana dashi da mahaifiyar shi lokacin zamuyi liyafa tare dasu muci dinner a tare a yadda aka tsara aka fada muna kuma . Ba wani kwaliya nayiba na azo a ganiba, dogon rigace kawai kalan kakin soja a jikina gaban rigan yanada tsaga da filawowi zuwa gwiwan rigan sai igiyan daure shi dana daure tsakiyan kwankwasona sai dan kwalin shi a kaina saidai rigan gaskiya ba laifi don ta hadu wurin kyau dagani kasan na kashe naira a wurin sayen shi. Muna cikin motan daya dauko mu zuwa masaukin su inda suke suna jiran mu ashe tsakanin mu da idan suka sauka din baida wani nisa sosai da inda muke. Motar na tafiya a hankali saman titin ga ruwa daya kawata garin hakan nake bin garin da kallo ga gidajen wasu a tsakiyan ruwa da yayiwa garin kawanya ga gine gine iri iri sai inda kallon ka ya tsayama. Hakan yasa na raina kyan lagos duk da a kullun garin lagos a cikin cigaba yake fiye da sauran biranen Nageria da muke dasu Motan ya shiga wani kayattacen compound maikyau da ban sha,awa wanda kowan mu ya yaba da kyau wajen don wasu har magana sunyi. Kusan saida kowa ya gama fitowa daga cikin motar na fito a karshe ina dan gyara rigan jikina cikin kamewa don yanayi zaka kalla kasan bawai tafiyan ina jin dadin shi bane duk daulan da muke gani a wanan tafiyan. Wani mutum ne dake jiran mu a wajen wurin ya taremu yake muna sannu da zuwa shi yai muna jagora zuwa inda suke wurine mai kyau da aka kawata shi da sosai da kujeru na alfarma masu kyau da daukan hankali aga wani babban table din cin liyafa wurin ga manyan kayan cin abinci nan saman shi a jere. Alaja kamar yadda naji yan lagos na kiranta dashi itace muka hango cikin shiga na alfarma zaune tare da danta a gefe saman wasu kujeru na alfarma a wurin. Fuskanta ba yabo ba fallasa lokacin data hangomu kusan lokaci daya muka iso tare da wasu da nake zaton yan uwansune na jini kungiya biyu wasu daga arewa wasu uku kuma daga kudu suke. Muka hade a tare dasu gaba dayan mu sun nuna farin ciki da ganin mu suke muna sannu da zuwa ba bata lokaci bayan gaisuwa aka nufi saman dinning table din don cin abincin. Gaba daya a takure nake a wurin don nice karama cikin su gaba daya da muke zaunen addua akafara wanda shida kanshi ya jagoranci adduan . Kafin abawa daya daga cikin kiristocin shima yayi addua a lokacin aka shafa jimoh ne ya fara magana yana fadin sunyi maraba da kowa daya samu halartan wanan tafiyan yadda kowa yazo lafiya Allah ya maida kowa gida lafiya. Sai abokan aikin mu ya nuno mu a inda muke zaune yana fadin wanan gaiyatan da biyu maigida ya shirya maku shi don kuzo nan ku huta na sati biyu saboda ci gaban da kuka samowa company a yanzu. Nan dai aka dauki tafen jin dadi bandani da dan guntun murmushi na sake kawai iya fuska da baikai ciki ba a lokacin don jin har sati biyu zamu kwashe a wanan tafiyan da in mun dauko yarsu data gama karatu zamu wuce Dubai daga can muyi sati daya mu dawo gida Nigeria daga can. Muryan Alaja ne ya dawo dani daga tunanen da nakeyi inda yemisi dake kusa dani zaune ta dan zungureni na dawo firgigit daga tunanen da nakeyi a lokacin. Tana fadin yata ya kuma kamar bakya farin ciki da wanan albishir din da kukaji a yanzune na dauka kowan ku nan zaiyi farin ciki da wanan karamawan da dana yai maku a yanzu. Don muma kun jawo muna cigaba sosai a cikin harkokin mu a wanan lokacin don gaba daya ma,aikatan da muke dasu sun mayar da himma wurin kawo muna dukiyan mu yadda ya kamata a yanzu. Dan murmushi na kara sakewa ina fadi a cikin yarbancin da itama din tayi muna cewa nayi murna da jin hakan Allah ya kara rufa asiri aka amsa da amin lokaci guda. Nan aka fara cin abinci ni dai na zubane amma sam banji dadin abincin ba sin haka cibi biyu kawai nayi na kurawa cup din dake gaba cike da ruwan lemo mm a ainihi idanu. Daga inda yake zaune shima ido ya kura min babu ko kiftawa haka Alaja dake magana dashi ta dago tana kallon shi jin yayi shiru a lokacin ta kalli inda dan nata yake kallo din taga na kurawa cup idanu ina tunane. Let me feed you by myself oyyah come close to me ta fada tana tayar da wace ke kusa da ita zaune a lokacin wace sai alokacin na shedata wanan kanwar natane dai da muke haduwa a sha,anin su. Dan murmushi nayi na dauki cibin na dibi abinci da sauri don jin abinda Alaja ta fada a kaina don nuna damuwan ta kan rashin sake jikin da nakasa yi dasu. Matsa min tayi akan na dawo kusa da ita din inda tasa wata tashi don dole na mike na dawo inda take na zauna. Ana cin abincin ana hira da dariya ganin hankalin su ya dauku ana surutu yasa na mike daga wurin na nufi can inda muka samesu da farko na zauna ina bin wayana da baida amfani da kallo don katunan wayan mu basu da amfani a kasan yanzu. Hankalina ya dauku ga wayan ban san zuwan felix inda nake ba sai muryan shi naji yana fadin meke damun kine haka yan mata ? Kaina dago na dan kalleshi kafin in ce dashi nothing meka ganine kawai ina tunanen mahaifiyatace dana baro a gida. Don ban taba tafiya haka mai nisa ba tare da ita ba asalima idan ba tafiyan da muka tabayi da oga ba yayi saurin fadin wanan da bom ya tashi ko kai gaskiya mutanen ku they are wicked. Felix kazo kabi mutanen nan kayi muna odan abincin dare ya fada daidai lokacin da yake karasowa wurin namu. Haka yasa muka dago kai da sauri muna kallon shi kafin ya karaso inda muke zaune ya zauna na yunkura zan mike ina fadin felix ya jirani zanga yadda wurin yake yace no in zauna magana zaiyi dani. Felix din ya wuce inda ya aikeshi a lokacin ya kai zaune yana fuskantana kafin ya fara din miss Sahiba bansan irin godiyan da zan maki ba in nuna maki jindadina ga abin da kukai min. Gaskiya na yaba nakuma gode sosai da wanan aikin da kuke gabatar min ko nawa zan baku sai dai kawai in baku badai kudin ladan aikin ba a gareni. Aikine na kasada babba kukayi wanda ba kowa zai tsaya yai makashi ba don ni kaina da farko da Jimoh yace a baku aikin na tsorata matuka ina gudun wani abu mara kyau a sanadin aikina yazo ya sameku Don na bincika naji labarin mutanen nan bashi da kyau sosai akan dukiya zasu iya salwantar da rayuwan mutum. Kai na dago tare da murmushi ina kallon shi don jin abinda ya fada nace kome zasuyi nasan cewa Allah ba zai basu sa, a akan mu ba asalima ai sune suka taba abinka don haka kome zasuyi a kansu zai koma yanzu. Gaskiyane sun kawo muna hari da dama dan zaman da mukayi dasu saidai Allah bai basu sa, a akan mu ba don muna tare da tsarin Allah hakane yace yana
Chapter 209 · 0% Book details