Sashe 282
Ana Dara Ga Dare Yayi Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read
birnin madina don rashin zuwan shi da wuri ya jawo hakan. Ina yawan ganin su tare dasu baffah sosai a ko ina zamu hadu suna tare dasu banda gaisuwa ba wani abinda ke hadamu dashi don yawan kallon da yake min idan mun hadu har na fara tsarguwan shi. Ban faye zuwa inda yake ba idan suna tare dasu baffah zan tsaya daga nisa dasu ranan dai har nakai ga jan tsuki don na manta tare da yan uwanshi muke ina fadin kai nina tsani kallo wallahi. Waye ke kallon ki faiza ta tambayeni wancan mutumin mana har bana son mu hadu yanzu wallahi sai ya dinga bin mutum da kallo haka kamar , , , , Faiza ce tayi min nuni da su cewa dan uwansune fa naja tsuki ina kawar da kaina gefe daya hankalina ya koma kan wasu yan kasan chaina na bisu da kallo. Banyi aune ba sai jin muryan shi nayi a bayana kusa sosai yana fadin sun baki sha,awane kike kallon su haka ? Firgigit na juyo inda muryan nasa yake yana kusa dani din kamar yadda nake zargin gaida shi nayi cikin basarwa kamar banji abinda ya fada ba da farko. Ya gyara tsayuwa yana fadin kuna kokari sosai dake da yan uwanki uncle ya fada min irin kokarin da kukeyi ai saidai ku dan rika ba kanku hutu umurah ba aikin hajji bane dake da dokoki da yawa nayin sa. Nagode kawai na fada ina kokarin wucewa muryan shi ya dakatar dani da yake fadin zanso ki samu lokaci mu dan tattauna dake kafin mu bar kasan nan don akwai abinda nake son muyi magana a kai daga ke sai ni a nan din. Kallon ido da ido nayi masa wannan karon a cikin mamaki nake fadin a kan me ke nan zaka so zama dani fa ?. Saida ya dan murmusa yace wani abune daya shafi rayuwan mu a yanzu duk da mun fara magana dasu malam hamza amma zanso naji ra,ayin ki kema kan hakan. Idan ya shafi rayuwana ai ko a waya zamu iya maganan don ban faye son tsayi haka da mutane ba in public gashi kuma kace su baffah sun san zance ai is OK tunda shi baffah hamza yana da wayewan kai sosai ina fadin haka na juya na tafi. Na barshi yana bina da kallo tare da mamakin baudaden halina nan kan sam ban biyo mahaifina ba ga hali ya fada cikin zuciyar shi. Washe gari da darene bayan mun dawo masauki kwana biyu ya rage mu wuce zuwa makka sai ga kiran ya Abubakar ya shigo min. Na dauka muka gaisa ya tambayeni yan uwa nace duk suna lafiya yai muna ya ibada har na bashi kowa su faiza suka gaisa dasu. Kafin ta sake miko min wayan yace akwai wani abinda ke gudana ne dama tsakanina da mukhatar usman ashe don dazun uncle hamza ke fada mashi. Da sauri na tare shi da meke nan fa no ni ba wani abu jiya madaine yake fadin yana son yin magana dani ai dadai ya fahinci ban san komai sai cewa yayi is OK zai kira gobe sai muyi magana don ya fahinci yanzu darene a wajen mu. Bayan muyi sallama na kashe wayan zuciyana yana cike da tunanen wani magane wai gashi su baffah basuyi min wani bayani ba. Muna kuma tare dasu dazun da zamu dawo masaukin mu ai kawai saina share zancen ni naci gaba da tsabgogina na kwanciya na kwanta. Washe gari ya kama jumma,a da wuri muke shirin fita zuwa masalaci don mu samu sallah a lokacin cikin masallacin. Kowan mu yana shirin umma ta shigo dakin da wani leda mai kyau ta miko min tana fadin yau jumma,ane mu saka fararen kaya mu fito. Na bude ledan wani dogon rigane mai kyau da daukan ido kafin ma nayi magana take fadin in saka ba lokaci idan mun dawo zatai min bayani ta fita. Ni dai na bita da mamaki faiza ta bude rigan tace na saka yana da kyau sosai gashi yau jumma,a dama ban so ba amma na daure na saka don umma. Saidai ina jin don me zata kashe kudinta ta saya min riga haka ni ban saya mata ba haka muka fito dole motan dake kwasan su zamu shiga mu bisu kada mu rasa sallah a haram din. Har mun zauna cikin motan na hangoshi ya fito shi da wasu mutum biyu shima fararen kayan ne na yan Pakistan a jikin shi sun karbeshi sun masa kyau sosai. Suka shigo motan ya tashi ban yarda na dago kaina ba a lokacin don kada mu hada ido dashi tun kallon dana jefa mai lokacin da suka fito din na kawar da kaina gefe ina karatun wani addua a cikin wayana. Har muka isa masallacin muka nufi wurin mata suma maza suka nufi nasu wurin har dare muna ciki muna ibada kafin mu dawo masaukin mu. Duk dai gani nan banjin dadin kaina a ranan gaba daya tun safe ina jin bakin rai muna sauka mota su mama Amina suka tareni da fadin yar nan ashe abin arziki ya samemu haka yau ? Ban fahinci me take fadi ba a lokacin don haka murmushi kawai nayi mata na wuce zuwa ciki na barsu suna tafe bayana suna fadin wanan abin da mamaki yake babu abinda bai iya faruwa ga bawa idan Allah ya nufa dama ?