Sashe 230
Ana Dara Ga Dare Yayi Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read
hulla mai raga . Nima cikin harshen yarbanci nake fadin zan shiga cikine kawai aiba wurina sukazo ba don kiris ya rage a lokacin na sako hawaye a idona lokaci . Kai haba hjy mairo baki koyawa diyan mu yareb mu ba sai yaren wasu kabilu can na daban baffa hamza ya fada yana kallona har lokacin a cikin mamaki. Umma dai batace komai ba son fuskanta a daure yake lokacin sai naji baffh Abdullahi na fadin suna jin fulacin kila wanan yaren daine yafi karfi a harshen su don zama cikin su da sukeyi. Ya Abubakar kuwa duk yana jin su baice komai don gaba daya na kula dashi baya cikin hayacin shi a lokacin sam. Dan shirune ya biyo falon bayan na dawo na zauna din baffa Abdullahine ya fara magana yana fadin Mairo da farko zanso na kara maki gaisuwan rashin dan uwan mu kuma shakikin mu wanda bamu samu natsuwan maki ba tun a wancan lokacin mai tsawo daya wuce zuwa yanzu. A hankali na dago kai na dan kalleshi kafin in mayar da kallona a wurin umma a lokacin da take fadin hakkurin namune ai duka Allah yayi mai rahama suka amsa da Amin. Ya Sambo ya tafi ya huta saidai ya bar baya da kura akan dukiya munga abubuwa da dama mairo wanda har muka fara tuhumar ko hakan na daga cikin abinda yasaki barin gida dake da yarki a lokacin ? Kafin umma tai wani magana Ammar ne ya fito daga dakin shi yana saye da wando three quarter na maza fari sai riga mai photon zaki a jikin shi light blue clour daya dauki jikin shi suka bishi da kallon a cikin mamaki. Falin yayi shiru shima din dan kaduwa yayi da ganin su sai daya dan nuna razana a fili kafin ya gaidasu yana fadin good evening sir yayo inda nake zaune ya zauna a gefena rabin jikin shi na a jikina. Ammar kuna garin nan baka kirani ba ashe sai lokacin ya kula da ya Abubakar din ya dan mike a cikin mamaki yana fadin broda welcome i no see u shaaa. Suko mamakin kamar yaron da mahaifin mu ya hanasu ko motsi a lokacin sai can baffa Abdullahi ya nisa yana fadin ikon Allah kunga wani ikon ubangiji a nan wurin kuma ke nan ? Bari kaidai ina ganin kamar gun wanan macen sai kuma shi wanan din yace ai ga inda kaman yake dashi sak. Watau dai lamarin nan kawai saidai a barwa Allah ikon sa don zance ya kare a nan yanzu illa kawai yanzu mu tunkari baffa Amadu da wanan zancen. Ammar din ya mike zuwa wurin ya Abubakar yana tambayan shi yaran shi sai baffa hamza ya ce kai ku tashi mu tafi sai gashi yana share hawaye daga fuskan shi dake zubo mashi yana fadin wanan alhakin dame zamu amsa shi gaban ubangiji. Da kuka suka fita daga gidan mu dai muna zaune a inda suka barmu sai ammar ne yabisu suna rike dashi da yaya Abubakar din can ya dawo yana kulle gida yake fadin sun tafi ai tare da tambayan masu kukan nan suwaye su wai ? Su baffane zaune a gaban kannen mahaifin su suna kuka wi wi wi kamar mata tare da fadin anyi sakaci baffa sakaci ba karami ba wanda na tabbatar da sai Allah ya tambaye kan hakan. Ace diyan dan uwan mu suna raye haka a cikin duniya sun koma kabila zaka rantse baffa na diyan mu bane idan kagansu. Zama tsohon ya gyara yana fadin to kai banda abinka Hamza a cikin kabilu fa uwarsu ta tayar dasu koda a nan arewane yau akace mace ce zata ba yaro tarbiya ba tare da mahaifi ba ya kuke tsamanin tarbiyan nan. Hakane baffa ya gyara zama yana fadi tare dayin fifita da hularshi daya rike a hannun shi kafin ya kara gyara zama yana fadin kai jiya munga ikon Allah Baffa kamar yaron sak dana ubanshi har tafiyan nan na marigayi din. Yanzu dai karfe biyu idan an fito daga sallah sai a hadu a nan din a fadawa kowa kamar yadda aka sabayi harsu din sai a fada masu. Saidai kan yana da wuya ace sun amsa wanan kiran naku nake gani don gaba daya suna nuna kamar basu yarda damu bane ga baki daya mu nake gani. Dole a yanzu su nuna hakan amma idan an fahinci juna komai zai koma yadda yake don haka a kara hakkuri baffa Amadu ya fada sukai mashi sallama suka tafi tun a mota suka fara waya suna gaiyatan yan uwa har mata wurin wanan haduwan. Kamar yadda umma tayiwa hjy hari alkawari nice na tuna mata ta kirata tare da mata kwatancen inda muke sai gata da safen sun shigo da dan nata. Ina daki kwance sai kulawa da kwancewa nakeyi wanda har lokacin ban gama tsara yadda nake so ba naji sallaman su har fitowan umma daga dakin ta. Tayi masu sannu da zuwa bayan sun shigo sun zauna akai yaushe rabo da juna naji muryan Ammar daya fito yana gaidasu . Kuka naji gwaggo hari din tanayi tare da wasu maganganu hakan yasa na fito daga daki a lokacin daidai kujeran dake saiti da inda zan shigo falon daga dakina na tsaya tare da dafa kujera ina gaidasu. Naji tace zo gareni yata ku gafarce wanan duk sherin su yaya Nuhu ne kedai kin san komai dama mairo sai yanzu na kara yarda da cewan da akeyi suna da hannu a cikin kashe muna dan uwa dayawa mutane sun fadi hakan lokacin da sukaga ba a dauki lokaci ba an wawashe abinda ya bari kuma ba a nuna damuwa da bacewan ku ba. Ba wani nuna damuwa da akayi a lokacin haka ana kallo bayan kowa yasan irin makircin su yaya nuhu har suka rabe dukiyan ku iyasu ba wanda ya iya masu magana duk da asanshi da iya salwantar da rayuwa ba wani aiki bane a wurin shi shi yanzu. Kitchen na nufa don ban iya jin wanan zancen nasu bansan abinda yasa ba ko sau daya ni ban taba jin wani darrr akan shi ba yadda naga mutane na nunawa koda sunan shi sukaji. Wai a cewan su ko sunan shi ka kira ka zageshi yana ji ko a wani garine kuwa don haka mutane suke yawan tsoron shi sosai. Daga kitchen din ina jin abinda suke fadi a lokacin naji muryan gwaggo hari tana fadawa umma a cikin damuwa cewa ayi hakkuri tunda Allah ya dawo damu cikin su lafiya a janye wanan karan da yarinyar nan tayi a sulhunta komai a gidan kada daga baya hakan yazo ya jawo muna matsala wani abu yazo ya samemu kuma don halin su baida kyau har gobe zasu iyayin komai don dukiyasu. A fusace na fito daga kitchen din na tsaya a inda zata iya ganina gaba daya yanayin fuskana ya sauya raina ya baci bakikirin idanuwana duk sun kankance na fara fadin . Kuna ina a lokacin da aka watsar damu a cikin duniya ko lokacin da suka kashe muna mahaifin mu a kan abin duniya wani mataki a ka dauka a lokacin har batan umma damu da ba,a san ida tashiga ba na tsawon lokacin nan. Yanzu lokaci yayi da komai zai baiya kara muradin mu a yanzu ba karban dukiyane kawai ba don nemawa mahaifana yancin sune da aka tauye a lokacin na dawo yanzu koda nan karbi komai nasu ba dolene abiwa mahaifana hakkin su a yanzu kan duk wanda ke da hannu a cikin cuta masu. Na kare magana ina jefa mata wani irin kallo na ke kinsan koni waye kuwa a yanzu ?