← Book details Ana Dara Ga Dare Yayi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 54 OF 337

Sashe 54

Ana Dara Ga Dare Yayi Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

min wanan tambayoyin haka. Sukuku na shiga gida har umma taso gane hakam nasan in na fada mata ba zan kara shiga gariba ke nan kuma ni ba zan iya zama a gida ba saboda sabo da fitan da nayi a rayuwana. Don haka na shatata mata karya na samu na kwanta tare da karyan kaina ke min ciwo a ranan ina faman tunanen inda zan canza ba tare dana kara haduwa da wanan mugun mutum da a yanzu yake son shiga rayuwata ba. Washe gari din na dai fitane ba zance ga inda zani ba kawai na sakai na bar gida na dade a bakin titi kafin na nufi surulere da niyan yin wani sana,a acan. Ance ido wa ka raina don Alh Nuhu ga hjy Addah ya sauke haushin danta don ya taso Nazifa gaba da uwarta har gida suka samu hjy. Sai abinda ya raga mata nacin mutunci hjy sai hakkuri da take bashi kawai a lokacin bayan haka bata iya furta komai ba. Har yana ikirarin ta kira danta yazo ya sake mashi ya don ba gadin gida ya kawo ta nan tayi masu ba a cewan shi. Hjy dai ta rasa na fada sai ayi hakkuri take fada jin abin yayi yawa yasa hjy karima fitowa daga part din ta kamar da gaske. Tana dan basu hakkuri tare da fadin haka yake tun farko ya kamata, ace sun sanda hakan don haka aikin shi ya gada. Nan dai ya kare masifan shi tare da jawa hjy kunne akan suyiwa dan su fada shifa bai daukan haka ga diyan shi ko kadan. Tun fitan shi hjy ta zauna tayi shiru abin duniya ya isheta akan wanan aure da ba koyi wasu watanni da shiba an fara samun baraka haka a tsakanin iyayyen auren kan yaran nasu. Abinda kowa ke gudu ke nan a yanzu yasa ba wanda ke sha,awan hada wani alaka dashi kan aure da diyan shi itama din dai kaddaran haka ya jata har ta furta a gaban yar uwanta cewa tana son zabawa dan mata . Budan bakin ta sai cewa tayi da hjy me zai hana ki zaba mashi a cikin yaran yaya Nuhu gasu nan kyawawa dasu mazan yanzu ai irin su suke so . Yan boka kuma ga wayewa wanan zancen ne yar uwan hjy din ta dauka kafin hjy takai ga yanke shawara takai gidan dan uwansu din. Matar shi uwargidan shi naji hakan ta dauki zancen da zafi takai gaban mijin su tare da kara gyara zancen tayi mai kwaskwarima har Alh din yaji shima yana sha,awan wanan hadin a tsakanin yaron da dayan yarshi . A take hjy ke fadin ai zasu fi dacewa da Nazifa nake gani don gashi dama shima din wayayye ne kuma dan gata kamarta. Don shi kadai ne da namiji a wurin mahaifin su a yanzu sai nake ganin kamar hadin nasu zai dace gaskiya. Shima Alh Nuhun a lokaci wani irin shu,umin murmushi ya sake don akwai abinda yake bukata a wurin wanan yaton nan gaba sai yake ganin ai wanan dama ne a gareshi ya samu. Wanan ne dalilin hadin auren su daya taso haka kai tsaye kuma Alh Nuhun ya matse aka daura shi a kam lokaci. Tun bayan daya gano cewa yaron yana son ya subuce masu a karshe yasa daurin auren cikin dan kankanin lokaci kuma akayi haka. Yawan son diyan shi dayasa a zuciyar shi yasa yanzu da Nazifa ta kawo karan mijin nata ya rufe ido yayi masu cin mutunci ya tafi. Tafiyan shi keda suya hjy Asiya ta shigo gidan a nan ta samu hjy a cikin tashin hankali da farko hjy ta boyewa kanwar mijin nasu amma saiga hjy karima ta fito itake labarta mata duk abinda ya faru da shigowan dan uwan nasu kan zancen diyan su din. Budan bakin hjy Asiya sai cewa tayi ai dama yaya Nuhu mutumin banza ne baida tunane sam a rayuwan shi idan idon sa ya rufe yana iya yiwa mutum komai kan yayan sa. Da alama kan yadda yazo gidan nan ido rufe shi da matar sa da yar tasu a gabanta ya fadawa maman Nabila komai da yake son fada. Hjy dai tana jin su bata iya tankasu ba sai maganan banza suke fada game da dan uwan nata tana sauraren su kawai don tasan dama irin daman nan suke jira su fada mata cikin zuciyar su game da auren na Abubakar. Don tana sane da son hadin yarta da hjy Asiya din ke so tun da dadewa kuma har ta gabatar da zancen gaban dan ta yaki yarda. Wanan wace irin yarinyace haka kamar yar daba yarinya tana abu kamar wata mai tabin hankali ? Anya ma kuwa wanan ba wahalan banza yakeyi ba akanta ita din kuwa yar uwasu ce kodai watace can na daban yake wahalal da kanshi akanta yanzu. Zama ya gyara yana fadin to amma kuma ai kamarsu ya baci da yan gidan don ma har ita wanan din idan ga gata harta zarta yaran gidan yake gani wurin yin kama da iyayyen su. Don da ganin ta kaga yar fulanin asali da ita saidai da ta bude baki tayi magana zakafi danganta ta yar wani kabila da ba hausawa ba. Koma dai wacece ita ya sha alwashin cewa zai taimaka masu tasan ko ita wacece tunda ta shigo rayuwan shi a yanzu. Haka kawai dan interview din da yayi mata da wanda ya hada tun farkon haduwan su sai ya gane yarinyar tana son tasan mahaifan ta da jaharta. Kai mutanen mu na arewa akwai kaskantar da kansu a irin wanan wuraren da ba, a san daranjan su ba. Ta yaya macen bahaushi zata zube yara kamar haka tana yawo a cikin gari wai tana tallan magani da sunan neman kudi. Dan murmushi ya sake don tuno da kayanta data sake a cikin motar su ta gudu ta barshi garesu in ba shirme ba nawa zata samu ga wa yan nan kayan da ya gani a cikin jakarta. Shawara da Nazari yaci gaba dayi shi kadai a dakin yaga dacewan bibiyan case din ya zauna mai a zuciyar shi yace koma meye tsakanin yau da gobene zai shawo kan matsalam su don zai binciko har uwan yarinyar nan yaji idan yaran ma suna da mahaifi. Gaban shine ya fadi ya dauko waya ya fara neman layin chuku yake sanar mai cewa zuwa gobe yake son su kama yarinyar nan suzo da ita don akwai tambayan da yake son masu ita da mahaifiyar ta. ALIYU MAKAMA THE BOY zaune yake a hadeden gidan shi dake Apapa Alabi street dake tall get . Yana zaune kasa don nan yake zaton zaiji dadin zama a wanan yanayin daya daure mai kai a yau don yau dai taron nasu ba,a watse shi da dadi ba. Don shawara yasha bambam a tsakanin da abokan kasuwancin nasu dake da shawara daban daban kan yadda suke son su canza arkalar su a yanzu. Shikan gaskiya a wanan katon yasan zasu raba hannun riga dasu don baida ra,ayin shiga wanan harkallan tasu tun farko. Don bai fara wani kasuwanci ba irin na mahaifin shi saida ya dan koyi wasu abu daga halaiyar mahaifin nasa na gaskiya. Shi tun farko dama bai yarda da wa yan nan kurayen kudin da yake tare dasu ba kuma bai taba zaton suna wanan haramtacen sana,an haka a cikin tafiyan su. Hannu ya mika ya dauki cup din dake gaban shi cike da lemo tattaciya ya dan kurba ya mayar ya aje a inda ya dauka. Don yadda yake jin kanshi a yau sai yaji kamar ya kurba ruwan guba ne a cikin sa lokacin don bacin rai. Taya yayyafi zai masa haka ya boye mai abinda ya saka a cikin kayan shi har yayi kasadan fitar mai dashi tun daga turai har nan kasan ba tare daya san hakan ba sai yanzu da yaron shi ya tsegunta masa hakan da sukai mai. Akarshe dai yasha alwashin zai masu yankan baya ta yadda zai iya fitar da kansa daga zargin da aka fara jefan shi dashi zai nuna masu shi din jan koma ne idan su kifaye ne masu kwakwalwa daskare. Da wanan tunanen ya mike tsaye daga inda yake zaune din zuwa dakin kwanan shi don yau baijin fita ko ina don yadda yake jin kansa din. Haba dole ashe yan sanda su nemesa haka ruwa a jallo don wanan abin yace a fili rai a bace dan guntun murmushi ya sake don shawaran da zuciyar shi ta zauna a kai lokacn. A haka barci ya dauke shi mai nauyi har da mafalkin sun hade da yan sanda ana gumu dashi kan wanan case din daya zauna mai a rai.
Chapter 54 · 0% Book details