← Book details Ana Dara Ga Dare Yayi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 326 OF 337

Sashe 326

Ana Dara Ga Dare Yayi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tsukin dai bai kare ba saidai a yanzu ya fahinci badaga bakina wanan sautin da yake ji yake fitowa ba haka yasa yakara kaimi a wurin daga sautin karatun nasa. Sannu a hankali ya fara jin numfashina yana komawa normal haka yasa ya fahinci cewa bani kadai bane a lokacin yayi mamakin hankan sosai a zuciyanshi dama ashe da gaske akwai wanan matsalan ashe ga al,umma ? Bai daina karatun da yakeyi a lokacin ba sai gabanin asubahi sosai shima barci ya daukeshi saidai lokacin sallah yanayi ya falka ganina mane a jikin shi na dunkule a wuri daya da alama sanyi ko tsorone a tare dani lokacin. A cikin dabara ya zare jikinshi daga nawa ya mike zuwa bandakina nan ma ya tsaya yana bin ko ina da kallo kafin ya daura alwala ya fice zuwa sallah. A daidai lokacin da aka tayar da sallah lokacin na falka a cikin mamakin ina duban yanayin lokaci na biyar saura na safe a lokacin mikewa nayi da sauri kada in makara ga sallah. Sai bayan na idarne na lura da alaman mutum ya kwana a dakin nawa lokacin don waya da jakkashi na laptop dake saman gado a lokacin ga wasu takardu da agogonshi duka a wurin. Mamaki naji sosai da ganin haka har yaushe ya shigo dakina ya aje wanan abubuwan kodai a nan ya kwana na tambayi kaina ganin ba amsa yasa da sauri na juya na kalli inda zan samo ansa din sai naga alaman dai mutum biyu sun kwana a wurin. Da sauri na mike na isa zuwa wurin da nake zargin an kwanta din babu abinda ke tashi lokacin sai kamshin turaren da yake amfani dashi. Mamakine ya kara kamani lokacin how comes har ya shigo dakina ya kwana a nan ban sani ba me yasa ya kwana a dakin kuma ranan ? Ban kaiga karasa tunanena ba sai gashi ya shigo dakin da sallama shi fuskanshi kuma yana nuna mamakin gani a tsaye a laman har na idar da sallah ke nan a lokacin. Ahankali na juyo na sauke kallona gareshi tare da kaiwa kasa ina fadin good morning uncle morning ya bani amsa tare da fadin how was your night Alhamdullahi na fada ina dan jada baya kada jikin mu ya hadu da nasa. Zama yayi a bakin gado tare da daukan kafanshi daya ya dora saman gadon ya dan bubuga gefenshi da yake zaune tare da nuna min inzo in zauna. Dan jim nayi kafin na iya dago kafata zuwa bakin gadon nakai zaune a gefen shi dan shiru yayi yana duban wayanshi kafin can yace ki fada min abinda kike gani a cikin mafalkin ki inji ? Cikin mamaki na dago na kalleshi kafin in maimaita tambayan da fadin in my dream ? Ya lumshe idanuwan shi yana fadin yes akwai abinda nake son in gane a game dake yanzu dan shiru nayi don ban san ta ina zan fara fada mai abinda yake sonji din ba. Mafalkin me kiyi a daren jiya daya baki tsoro kika firgita suwaye suke binki haka a cikin mafalkinda ya zamo ba mafalki bane zahirine ? Da sauri na dago kaina na kalleshi yace yes zahirine ba mafalki bane kawai kikeyi haka don tareshi nayi da fadin I know wanan yanayin da nake gani sabone a gareni. Amma duk da hakan ba nasara ga maishi son muna buga fada sosai da abinda nake gani din a yanzu barshi kawai maishi zai koma mashi insha Allahu a kwanan kuwa. Kallona yakeyi har na kare zance na ba wani alaman tsoro a tare dani lokacin kara maimaita min tambayan yayi nan na shiga fada mashi abinda nagani yana bina da kokarin son daukan wani abu a cikin jikina da karfin tsiya. Shiru yayi na dan lokaci kafin ya nisa yana fadin insha Allahu komai zaizo karshe ina jin dadin yadda baki fadawa kowa matsalan dake damunki din a cikin haka har mu sha karshen abin. Duk da a yanzu na fahinci sabon matsalanki shine da zaran mun kebe dani dakene kike shiga wanan halin kenan haka na nufin akwai abindake faruwa dake a wani wurin yanzu kuma. Kallon mamaki nake mashi don jin kusan yasan komai dake faruwa dani a yanzu saidai ta yaya yasan da hakan ke nan ? Kada ki damu ya fada yana kai hannunshi saman kafadana ya rugumoni zuwa jikin shi idona na lumshe lokaci guda don jin saukan hannun nashi da nayi a jikina lokacin. Yana kuma fadin nikaina nasan matsalan ki tun farko sanina dake sahiba bayan haka kuma ina bibiyan komai sannu a hankali nasa daga ina zan fara da matsalan nan naki tun yanzu. Hawaye naji yana zo min wanda bansan kona meye ba a lokacin gwaggo hari ashe tana da gaskiyanta wazai ga ramin maciji da rana yazo da dare ya taka bakin ramin da kafanshi. Babu mai hakkuri da wanan irin matsalolin nawa danima ya sameni da rana tsaka tunda da farko ba haka nake ba nima ai. Hada jikinshi yayi sosai da nawa ta yadda har nake iya jin saukan numfashin shi a lokacin a cikin gangan jikina har banyi aune ba naji saukan hannayen shi saman jikina yana yawo a hankali. Jikina na kankameva wuri daya tare da kara runtse idanuwa da suke rufe a lokacin don jinda nake kamar ana watsa min ruwan zafi masu zafi nake ji a lokacin. Banyi aune ba naji yana kokarin kwantar dani saman gadon a cikin wani irin karfi da bai taba tsamanjn jinshi gareni ba kasancewata yar firit dani ga idonshi. Yasa yayi saurin jada baya yana zuba min ido tare da kallon yadda jikina ya dauki rawa lokaci guda saina fara jin ina zuwa baya suuu lokaci guda idona yana kara rufewa Kafin hankalina ya karasa gushewa ina iya dan jiyo sautin karatun daya fara yi shi kadai zan iya karaswa a lokacin wanda naji a lokacin. Nidai a karshe na bude ido na ganni wujuga wujiga kwance saman gadon dakina da sai warin hayaki dake tashi ko ina na dakin ga baki daya. Yunkurin tashi nayi zaune bayan nagama bin ko ina na dakin da kallo lokaci guda na yunkura na mike zaune murya hjy su uncle ce dake zaune da a gefena tare da kanwarta. Sannu yar nan suka kara fada lokaci guda sannu kinji sannu da fama wanan abu haka yaki guda tun safe ana abu guda. Ai Allah ya kawo saukin abin nata mabiyan manyane fiye da wa yannan da aka turo matasu yanzu gashi sun fada da bakinsu cewa sarki ya tare wuri yana wahalal dasu da basu azzaba. Aini jikina duk ya mutu idan ba ko aikin aljani ba har yaushe yar nan tasan wa yannan labarun data bamu a yanzu ? Bashi bama ba abinda yafi ban mamaki shine kamar wai yadda zancen gonan gadon su yaran nan ya fito a bakin wanan yar har take bamu labarin shi tas kamar a gabanta akayi komai alokacin. Jinsu kawai nakeyi don ina son kewayawa bandaki a lokacin kuma suna zaune a dakin nawa haka yasa ina mikewa suke tambayana da turanci nayi magana na fito daga dakin suna ganin haka a zatonsu bana cikin hankalinane yasa nake kokarin fita daga dakin gashi sai wani irin zufa nake tarsowa a jikina lokacin na wahala. Ina zaki tafi gaba dayan su suka fada lokaci guda na dan juyo na kallesu ina fadin zan shiga bathroom ne aiga kofa nan dakin Fatima zan shiga na fada. Jin hakan yasa sister ta tashi da sauri tabi bayana zuwa dakin har na kewaya na fito sallah nake kokarin yi a lokacin haka dai na daure nayi sallah dake kaina a lokacin. A nan na kara kwanciya don banson hayaniya ido na lumshe duk da ba barci nakeyi ba lokacin amma saika dauka nayi barcine a lokacin yadda na lafe. Kokarin bude kofan da akayine yasani bude ido shine ya shigo tare da wani tsoho sosai mai farin gemu gajere da dogon tasbaha a hannun ga warin turareshi yasa kaina hawa na fara jin wani iri lokaci guda. Da sauri uncle mukhatar yazagayo zuwa inda nake ya tallafoni lokaci guda na fara shakuwa ina gyatsa duk lokaci guda ga hamma da nake sakewa ba kakautawa . Kai tsohon ya fara kadawa tare dan matsowa inda muke din zaune sai kokarin kankame jikina nakeyi don kada ya kara tabani. Ido sosai tsohon ya kafa nan ya fara karatu yana tofa min tare da umartan uncle da yadafe min kaina sai girgiza kai nakeyi hawaye na zuba min a idanuwana. Ya dan jima yana karatu kafin ya fara fadin wanan babban kayane a kanta sai baki gasunan sunsha fama sai sun shiga jikinta suma amma hakan bai yuyuwa . Karatu yaci gaba dayi abin mamaki yaren su na farayi na kanuri ina fadin abar karatun nan nan muka zuba yare dashi nan abinda naki fada a farko na fada cewa anturosune su hanani zaman aure da mijin wata. Sai sukai rashin sa,a sarki mai karfin iko yana jikina do haka ba wani wanda ya isa ya rabeni a wanan lokacin su kuma sunyi alkawari har sun amshi jini a matsayin hadayansu ko. Salati dakin ya dauka daga can kofa muryan sister ne ke fadin waya turoku wanan aikin haka gareta wani kallo aka watsa mata kafin ace wace ta turosu ta riga datafi karku dukkan ku banda wanan godiyan da aikin mu baya iya tasiri a jikin ta ko kadan. Mun gwada ko wani hanya bamuyi nasara ba ga hakan gashi kuma yanzun ana kona mu ba zamu yafe ba dole mu koma jikin wanda ya aikomu zuwa wurinta. Sai wani Ihu da kowa dake wurin ya razana da hakan dajin ihun maishi yana wahala a lokacin an dauki lokaci ana wanan yakin kafin su ce sun fice su tafi nayi lankwas kamar bani da rai a wurin. Allah ya taimaka tunda nayi barci ban falkaba sai washe gari na tashi da ciwon jiki da kasala haka yasani kwanciya ko falo ban iya lekowa ba a ranan. Yayinda shi kuma yake ta faman sintiri dayin hayaki da shafa abubuwa a jikina hardasu shakawa haka sunin ranan suka wuni dani da dare kuma tare dashi din muka kwana duk da
Chapter 326 · 0% Book details