Sashe 215
Ana Dara Ga Dare Yayi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Yana ganina ya bar mutanen da suke tare lokacin tsaye haka ya wuto mahaifiyar nasa yana tafe yana murmushi dauke a fuskan shi har ya karaso inda muke tsaye gab dani yaja ya tsaya har muna dan hada kafada dashi. Nayi saurin dan ja da baya kadan yayi murmushi yana fadi kamar rada kada ki yarda ki nunawa kowa dake wurin nan wani abu please. Kamar gaba na ya tsage a lokacin don nauyi hakana daure na biyewa yadda yake so muje ko ya fada yana nuna min hanya da hannu tare da dan wani dukar da kanshi kasa. Wani kallo suke bin mu dashi yayin da Alaja taji wani irin tukukin bakin ciki ya kara rufeta a lokaci guda as a mother to him ba zata taba barin dan ta ya rabi wanan yarinyar mai tattare da sihiri ba a fili haka ta fada a ranta. Sam ba zai yuyu bama ace dan ta da daya tillo datake alfahari dashi a duniya ya auri yarinyar da bata da background ba yar kowa ba yarinyar da ko da nacikin cikin uwar shi ta kalla tasan me yake fadi. Ba kyau baje abin duba nasaba da dacewa sam wanan yar bata cancanci zama surukarta ba ta kara dago kai ta kalle mu a daidai lokacin da muka karaso inda take tsaye tare da mutanenta gaba dayansu duk sun sha mur a fuskan su lokaci guda. Da alama hakan bai dameshi ba shi ya nuna masu don muna isowa wurin su yaja ya tsaya yana gaisawa dasu sama sama tare da fadin ya suka kwana ? Daga inda nake tsaye na gaida Alaja da ekkaro mah da yatsune a fuskan ta ta amsa da karo joo tana kawar da ido a kaina take fadin ya bai jirasu ba ya wuto zuwa airport. Yake fasin yana sauri ne kada mu iso baya wurin Nabil ne ai ya dauko shi zuwa nan din bai dagakata ba ya juya ga fadin Sahiba meet my friend Nabil living in turkiya. Muka gaisa da wanda ya kira da Nabil din ya kara fadin she is Sahiba by name a cikin dan murmushi Nabil din ke fadi nice name is she the lucky girl that charm your heart ? Shima sin dariya kawai yayi mukayi gaba muna jere da juna gashi duk wani iri nake jin kaina a wurin don gaba daya sun zubo muna idanun su a kan mune felix ya yafuto yana fadin mu shiga kada a bata lokaci ka tabbatar da kowa ya gama kafin ka biyo mu. Ya fada har munyi gaba kadan ya tsaya kuma yana fadin idan da wani matsala ina ciki sai ka sameni suka dan tsaya da abokan nasa suka dayi magana da larabci sanan muka nufi ciki. Mazaunin mu daya da oga da tun zamana ban dago kai ba balle in juya inga na bayana da gefen mu shima kuma bai min magana ba sai zama dayayi ya harde kafafun shi. Barcine ya daukeni wanda nasan rashin yin shi da darene da ban samuyi sosai ba a lokacin don tunanen zancen Alaja da na kwana fassarawa a lokacin ban gano manufar Alaja din ba gareni. Tafiya ganin gari akace muna jin england da labarai a kanshi yau sai gamu a kasan cikin hukuncin ubangijin mu Allah. Ba zan tsaya mamaki ba akan abubuwan da mukaga su Alaja da danta nayi don shi kudi babu abinda bai saka bawayi idan suna dashi. Yammane muka isa masaukin da zamu zauna lafiyayyen daki irin na manyan mutane shi aka kama min don ashe wanda muke ciki iri dayane da nasa da Alaja sai sauran suna a cikin wanda baikai wanan din kudi ba. Tun shigana ban fito ba ina cikin dakin bayan ramuwar sallah dake kaina sai kuma na haye gado da niyar barci a lokacin kararawan dakin naji yana kara na tashi naje na bude inga kowa waye. Room service ce tsaye dauke da dan abin turo abinci tana min murmushi miss sahiba ko na gyada mata kai abincin ta shiga dashi bayan ta gaya min wanda yace a kawo min abinci din. Na jaye ta shiga daga ciki ta ajemin nayi mata godiya ta fita abincin nabi da kallo abu daya ne daga cikin abincin ya dauki hankalina watau fruits salad din dake nade a cikin wani bowl mekyau dashi. Fasa kwaciya nayi na zauna na bude na fara sha da bissimillah a bakina sosai naji dadin abin don yasha hadi na kayan lanbu sai lokaci nake karewa dakin kallo da ada ban damu da ko a ina nake ba. Idona na lumshe ina mai hamdala ga ubangiji daya nufeni da ganin irin rayuwan da ko wace mahaluki ke fatan ganin kanshi a ciki. Sosai na sake na kwashi harka a dakin don na manta rabona da tsayawa naci wani abu irin haka don na wancan kasan da muka baro tafarnuwa da wasu sanadaran girkin kasan ya hana in tsaya inci wani abin kirki. Saida na dade zaune kafin i mike na nemi wuri na kwanta ina sake ajiyan zuciya wayana na lalubo ina duban sako kamar da wasa na kunna datana sai naga sakkon ni na shigo min a lokacin. Mamakine ya kamani yasa na danna kiran layin umma da damuwa da rashinta a kusa dani ya addabi zuciyana a yan kwanan kin nan da mukayi ba tare dasu ba. Saidai sam wayan nasu bai shigaba yasa na fara duban sakon nina saiga sakon ya Abubakar mm a gani a wayana yana fada min sunzo basu samemu a gida ba ya lissafo min sunayen wa yanda sukazo tare din nan lagos wurin mu. Amsan dana bashi shine ayyah Allah sarki see u next shi kawai na rubuta mashi a lokacin karshema wayan na kashe na fada tunane. Barcine ya daukeni a hakan yasa na manta da komai dake gabana don dama kuma barcin dai nake ji gaskiya don a takure nake sosai a lokacin. Bude wayan yayi bayan ya kammala komai yana duba sakon nam shi dake shigo kamar a sama saiga amsan dana bayar ya baiyana mai ya soma karantawa. Baiyi mamakin hakan ba don abinda yafi wanan ma din zan iya rubuta mai a lokaci idon shi ya mayar ya lumshe a hankali yana tunanen yadda abubuwa zasu kashe a karshe. Naziface ta shigo dakin motsinta da taji yasa ya mayar da idanun nasa ya rufe a hankali yana ci gaba da nazarin abinda ke cikin zuciyar shi. Saida ta zauna a gefen shi ta hau gado da kyau take fadin yanzu shike nan haka Abban mu zai zauna a tsare sai ranan da yar iskan yarinyar nan data tsaresu ta dawo daga balaguron ta ? Wacece yar iskan ya juyo yana tambayanta a cikin mamaki tare da tsareta da idanun shi mai alaman mamakin abinda ta fada karara a lokacin. Ehmana idan ba yar iska take ba gantalala har Abbane zata sa a kama don kawai su nuwa mutane su yan barikine basu san daraja da girman babba ba. Shi kuma babban daya tabawa yara kayan sufa shi kuma meye ko wanda bai taba an kamashi duk idon shi na a kanta yana mata wani kallo na tsana. Kafin ya kawar da kai yana fadin koda yake banga laifin ki ba don kin fadi haka yanzu don ke yarinyace baki san komai ba a zancen. Wai shigar mata ke nan zakayi ko me ko dai ka shigan mata ai bata kaini a gurin ka ba kome ko Abba yayi ma da kake jin zafin shi yanzu. Dama nasan ba wai ka damu da wanan abin bane tunda kowa yasan kaika nemisu ka kawo su garin nan har take ganin kamar ita din watace can. Au ashe kin sani ai ban san abinda kuke fada ba ke nan nako godewa Allah da yasa nine silan dawowan su cikin yan uwan su a yanzu . Ashe ku haka a wurin ku laifine ban sani ba to kije gun wanda ya fada maki nace ya dauki matakin hakan a kaina idan zai iya. Tsuki taja tana juyawa baya taci gaba da fadin saukin abindai wallahi Abba yafi karfin hakan duk ko me zatayi ya riga da yasha gaban ta ko wallahi ai tazo zata hadu damu kowa na jiran isowan ta ai. Za ko tazo din kuma zaku ganta sai muga wanda zai taba ta idan kun shirya mata don ma ki sani karewa a gidan ku zata zauna tunda nan ne tushen ta na asali. Wanan kuma fadane kawai kayi a yanzu amma ko ubanta yayi kadan yace zai zauna muna gida balle ita don haka inma haka aka shirya gara tun wuri a bari tunda ba gidan ubanta bane. Au ke na ubanki ne ya fada a hasale lokacin da baisan hakan zai fito daga bakin shi ba duk da hakan bai daina zancen ba yaci gaba da fadin ki koma ki tambaya wanan gidan na waye tun farko ? Yana fadin hakan yaja tsuki ya juya baya tare da lumshe idanun shi kamar yadda ta sameahi dakin da farko shiru tayi na dan lokaci kafin ta mike fuu ta fice dakin tana fadin mutum kullun kazo mashi da zancen arziki sai ya nemi ya bata ma rai shi. Washegari ya shirya bai tsaya karyawa ba don yasa tea sai bread zai samu kawai yasashi fita zuwa gidan daddy da safe don ya karya a can duk da yasan da wuya mommy ta bashi abincin don gudun zuciyar matar shi da takeyi. Babu kowa a falon sai faiza dake karyawa a gurguje kada ta makara zuwa makaranta a lokacin. Gaidashi ta fara yi a gurguje kafin tace mommy na ciki barin kira maka ita yace no barshi hada min abin breakfast in karya sauri nakeyi yanzu nima zan tafi abujane. Da sauri ta juyo tana kallon shi Abuja yaya yace eh yi sauri ki ban ta nufi kitchen din part din su da sauri tana aje mai ita kan ta fita tana mashi Allah ya kiyayye hanya. Saida ya kusa gama cin abincin mommy dake jin motsi a falon ta dauka faiza ce bata fita ba har lokacin ta fito. Ja tayi wuri daya ta tsaya tana kallon dan nata da ya bata tausayi lokaci guda mutum