← Book details Ana Dara Ga Dare Yayi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 247 OF 337

Sashe 247

Ana Dara Ga Dare Yayi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kwance nake shiru na kurawa rufin dakina ido ba abinda ke min yawo a yanzu sai kalamin ogan mu gasu yaya Abubakar da kuma zancen gwaggo hari a gaban mu. Juyawa nayi don zuciyana da naji yana mun zafi sosai a lokaci daya a gaskiya kaina ya daure sai tambayan kaina nakeyi nan din ma wasan yake so nayiwa yan uwana da hakan ko me ? Idan har wasane wa zamuyiwa wasan a nan kuma idan can muyiwa mahaifiyar shi don wani dalili nasa dayace in taimaka mashi a wuce wurin. Jin yadda ruwan sama ke sauka a lokacin yasa na ja abin rufa don nasan sanyi za ayi a lokacin na lumshe idona daga haka har barci ya daukeni ban falkaba sai safe. Washe gari ma hakana tashi da kyat na samu na fito falo don zazzabin dake damuna a lokacin hakana fito na karya kamar yadda umma ta bukaci in fito din in karya tunda banci wani abu tun tafiyan mu. Bayan na samu na dan sha ruwan tea din dana hada da kyar na samu na kurbe shi duk da rashin yawan shi kuwa. Na koma na jingina jikina a kujera ina dan kada kafa a hankali ummace ta fito daga dakin ta da sako zata ba kanin Abdul da yanzu shine karfin zaman shagon namu sosai. Don umma bata da issashen lokacin zama kamar da yanzu yasa ta barshi da shagon shi yana zama yana dan samu shima tunda yana da amana. Ta dawo ta zauna ta kalli kofin dana sha shayin a cikin sa kafin tace dani wanan din ya isheki ke nan na kada kai ta zauna take fadin dazun baffan ku sun kirani. Jin hakan yasa na dago kai da sauri ina kallon ta tace sun kirani kan wai ana neman bellin su iyalan su Nuhu da sauran tun jiya sun damesu da suna masu zariya a gida. Amma nace dasu duk abinda sukayi mai kyaune ai suna da daman yanke hukunci a yanzu don suma dan uwansu aka kashe yakin ba namu bane mu kadai ai. Hakan yayi umma a yanzu ko ance a kashesu ko a kwace dukiyoyin su a mayar muna sun dai da sunriga sun cuce mu ko don haka Allah ne kawai zai isar muna a kansu dama bukatana shine. Kowa yasan muna raye asan abinda su suka aikata kuma kowa ya bar maki zargi kan abinda mutane basu sani ba. Don idan ba hakan mukayi ba ba ranan da wanan zargin na mijin ki ya mutu kin shiga duniya da yarki don wasu cewa suke muna barikancin mune a nan. Hawaye naga yana zuba a idon ta nima din hawaye nake sakewa zuwa lokacin umma tace mutum akawai daukan wa kanshi zunubi. Kai zakaga mutum daga sama yayi abu wanda ba halin shi bane amma sai ka dauko wani zargi ka dora mai kana zargin shi dashi. Allah ne shedana tun ranan dana bar gida har zuwa wanan lokacin ban taba aikata wani abin assha ba da zai zubar muna da kimar mu a idon jama, a. Don haka shi yasan dalilin yin hakan a garemu nidai na shigo lagos ne don tserar da rayuwan mu daga cutarwan su ban kuma taba kai raina da cewa zan yi wani abinda ya kaucewa mahaliccina ba. Na kuma san wanan abin da kikayi maikyaune don haka kawai zamuyi nasaban mu ya dawo garemu lokaci guda. Shiyasa banyi wani yun kurin hanaki hakan ba daidao da rana daya don nasan irin tarbiyan dana tayar dake a cikin sa . Idan iyayye suna da yakini akan diyan su a zamanin nan sai mutane su dauka ko diyan sun fi karfin iyayyen ne suke kyalesu suna abinda sukaga dama har sai kaji ana fadin wani ko wance yafi karfin iyayyen shi ai . Abin ba haka bane yakine ne wani lokaci da iyayyen ke dashi kan tarbiyan da suka ba yaro idan ba,ayi dace bane sai kaddara wani lokaci ya afkawa dan don yawan bakin dan Adam akan yaro baki mugun dafine sosai ga dan Adam, . Addu,an mu ga yaya a yanzu shine neman kariya daga idon hama, a ko yaushe bawai neman abin duniya ba kawai ina ma,anan yin addua ga abin duniya kazo kuma abin ya zamo ma fitina a karshe. Umma na kalla nace umma abinda baki sani ba shine tunda na taso ba a taba fada min magana mai zafi ba irin wanda Alaja mahaifiyar ogan mu ta fada min na cewa wai ni din ba mai nasaba bace yar mace ce ni. Murmushi naga umma tayi a fuskan ta tana fadin ban tsamani ta kaiki nasaba ko tafiki nasaba a rayuwa don yanzu ita kanta kawai tasani bata san abinda Allah zaiyi maki ke nan gaba ba. Ban taba jin son kowa ba a zuciyana tun ina karama balle zancen da Asabe ta tabayi a gabana lokacin muna semi boda wanan maganan ya tsaya min a rai yana a cikin dalilaina na jajircewa a rayuwana. Wayan umma ne ya kara kara a lokacin ta dauka ya Abubakar ne a layin bayan sun gaisa naji tana tambayan shi baida lafiya ne taji muryan shi wani iri a cikin wani yanayi? Yake fadin kawai dan zazzabi nake fama dashi tun jiya amma da sauki sosai sai ya fara mata zancen da yake son suyi da ita karshe yace ta dan dakance shi anjima zai kirata ai. Ganin har kwana biyu bai kira ba yasa ranan muka tuno dashi nake fadin umma ai kamata yayi ki kirashi ki masa ya jikin nasa da kika jishi shiru. Ina da niyar hakan a raina sai dai Allah bai ban ikon kiran nasa ba tana magana ta daga waya ta kirashi abin mamaki wayar shi a hannun nazafa yake ranan don muryan tane radau a wayan. Hakan yasa na daina abin da nakeyi na dago kai ina kallon inda umma take zaune don tana dauka ba sallama sai cewa tayi waye wanan kuma ? Ke wacece na fada daga inda nake kutumar uba kikira min miji ki koma tambayan ni wacece au idan ke mijin kine ni kuma brother dinane and so what ko wa kike gareshi don ban sanki a cikin dangin sa ba. Kece zakifi kowa shedani kuwa don Allah malama ki bashi wayan kinji na fada a hasale ni kuma kara haukatata nakeyi ko banza muna da azzaza da ita da dadewa dama. Daga inda yake kwance ya bude idon shi yana fadi da kyar ke ban wayana nan ita kuma tana kokarun surfa min zagin cin mutunci shi kuma sai fadin yake da hankalin ki kuwa kikewa yar uwan ki wanan zagin haka nazifa ? Yar uwata ta ina me muka hada da ita kaima maye hadin ka da sune wai don ban gane me haka ke nufi ba wai kai kadaine a cikin dangi halan da komai sai kai ? Ganin sunan ummane a screen din wayan yasa yace umma zan kira dan anjima kadan to yana asibiti uwar bin didigi sai a barshi ya huta. Wani iri naji har cikin raina umma kuma na fadin don me zaki biye mata kuyi haka wanan ai shi zaku tayarwa hankali shida baida lafiya. Umma wanan matar ko tana da hankali kuwa daidai baki biye mata ba kunyi wanan don shi kike gani bana son kiran shi idan bashi ya kiramu ba son gujewa irin hakan. Zanko dinga kiran shi sai tayi abinda zatayi din idan na kira na fada ina haran gefe kamar itace a tsaye wurin. Kinji wai asibiti ciwo ya kaishi gashi taki bari muji meke damun shi saboda bakar kishi irin nata na hauka rai bace umma ta kalleni tana fadin a, a banga laifinta ba akan mijinta take hakan ai. Nikan kodana ce zan kira tun wanan ranan bankara komawa takan wayan shi ba kuma amma nakanji suna waya da umma tana masa ya jikin ? Mun shirya zamuje kauyen su umma amma sai mun tsaya kaduna mun gaida ya Abubakar dan kafin mu dawo sai lokacin shiga kotun mu hakan zaisa yaga badon shi kanshi muka zo ba. Mun shirya tafiyan mun isa kaduna a cikin dare don haka saida muka kwana washegari muka nufi gida daddy duk da bamu san irin taron da zamu samu ba a lokacin wurin su. Sam nika bamji komai a raina ba don wanan ne karo na biyu da zan shiga gidan daddy kuma da ranan da ya Abubakar yazo damu daga lagos daga baya aka mayar damu kan wani dalili dabamu sani ba a lokacin . Sai yau kuma da zan shiga don kaina ba kawoni wani yayi ba don ko yanzun din kan bin umurnin umma ce da tace a nunawa ya Abubakar bamu rike da mahaifin shi tunda ita umma tasan komai. Karma yadda mukasani gidan nan kamar yadda muka sanshi a baya komai ba a canza mai ba in kin debe fenti shima din nasan lokacin bukin baby ne akayi shi. Tun kan mu shigo muke jin muryan su a falon gidan babba suna dariya a daidai lokacin da mommy ke fadin kai hari wallahi baki da dama wallahi. Wallahi Addah haka kawai ai gara in fada mai gaskiya kan wata wai Sahiba can daga sama dama ace mahaifinta yana raye ne har yanzu . Ko kuma ta tashi a nan cikin mune kinga ka shedi tarbiyan yaro amma ni da nake son ya banbaro min yar gidan wani babban kusa zai kawo min zancen wata wai Sahiba can ana zaune kalau ? Abin ko dadin ji babu fa yaro ya gigice min shiko mahaifin shi har da son mara masa baya akan karya wai meye ga Sahiba din ? Mommy tace Allah dai ya sawake ai hanyar jirgi dabam ta mota daban dariya suka kara kwashewa dashi mommy na fadin aini tuni na kakabe shi da wanan zancen haukan modibbo zai kalli idona yace min shifa daya sani da sahiba ya aura tun farko. Dafani naji umma tayi a bayana ta kada min kai sai na dan hade bakin cikin daya tokaremin makoshi lokaci guda. A take nayi sallama daidai da shigowana falon nasu umma suna bayana har lokacin suka juyo a razane suna amsa muna a cikin rikicewa dukkan su daka
Chapter 247 · 0% Book details