← Book details Ana Dara Ga Dare Yayi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 127 OF 337

Sashe 127

Ana Dara Ga Dare Yayi Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

kakai kayan ka gidanka ne yace tun shekaran jiya ai nake garin nan ya fada har lokacin fuskan shi a daure. Ba abinda yake tunane a zuciyar shi sai yaya muke rayuwa a can tunda ya barmu ne ga bai samu nemawa ko Amar gurbin karatu ba ya tafi. Yasan ko ba zamuyi azancin cewa muci gaba da kararu ba tunda shi bai dawo gare mu ba balle ya taimaka muna da hakan. Abinci fa ta yaya muke samu yasan wanan ba wani babban matsala bane don zanyi talla in tallafawa rayuwan mu yasan da wanan din. To amma abinda ya daure mashi kai shine, idan shi baya kasan daddy fa me zaisa daddy yafita zancen bayin Allah nan haka ? Shifa abubuwan nan suna daure mashi kai kan game da daddy akan wanan zance wani lokaci anya kuwa koshi ma din ya gano hakan ne don yana kwararen dan sanda irin mahaifin shi. Muryan hjy ne ya katse shi tana fadin ke nan Nazifa da yaran suna gidan ka yanzu haka ke nan uwar nasu ta tambayeshi tana mai tsura masa ido don son jin amsan da zai bata. Ban fada mata na dawo kasan nan ba kuma bazan fada ba sai idan taji ga wani kamar yadda tayi maku itama yana fadin haka ya mike tsaye. Kallon kayan abincin da aka aje a gaban shi tayi kafin tace ka zauna ka karya kafin ka fita shima ido ya saukar ya kalli abincin kafin ya ja dan tsuki yana fadin ba zan iyaci ba mommy. Akan me ko ka karya a gidan kane ya kada mata kai alaman a,a yana fadin ban ci komai ba tunda na dawo kasan nan. A razane ta mike tsaye tana fadin bakaci komai ba mekakeyi ka tsaya haka da cikin ka bakaci abincin har tsawon kwanakin nan modibbo ? Kawai bana jin cine mommy ai wanan ba komai bane idan akwai diyan icce sai mutum yaci na dan lokaci. Zancen matar ka kana ganin hakan zaifi ba zai jawo matsala gareta da mahaifinta ba kasan halin yaya Nuhu da daukan zafi da gangan. Mommy ku wanan ya dama ni bashine a gabana ba yanzu zancen Nazifa kuma banyi fada da ita ko wani sa,insa ba amma ta zabi taci wa iyayyena mutunci da yan uwana. Don haka mommy na rokeki da kada ki fada masu zancen dawowana don girman Allah ya hada hannayen shi a wuri daya yana rokon ta arzikin hakan. Yana fadin haka ya juya zai fita Nabila tace wanan shine daidai ai mommy wallahi ayi maganin ta ta gane kuren ta zaifi. Baidai juyo ba duk dayaji abinda kanwar tashi ta fada haka yasa kai ya fice yana jin zuciyar shi tana masa kuna. Gidan sa ya koma ya kulle kanshi a cikin dakin yana faman tunane shi yanzu ma da wani ido zai kallemu yacewa wayan nan mutanen me a yanzu shekara nawa yanzu rabon su da su waige mu an dauki lokaci mai tsawo haka da wani ido zai kalli umma da yaranta yanzu. Yayi shiru taci gaba da tunane can yace bayan wanan shi daddy dake kasan meya hanasa neman su ne ? Anya kuwa ba wani abu a boye da daddy don shima ya boye kan wa yan nan ahalin dake cikin ukuba da gararaba a cikin duniya. Duk dai yasan a yanzu basu saura gararanban gidan haya ba tunda ya sama masu wurin zama ya sani kafin ya wuce . Kuma yana da yakinin cewa ba zasu daga, daga inda ya ajesu din ba in bada wani dalili mai karfi ba da zaisa su bar wurin. Bai sake fitaba a ranan sai washe gari da yamma ya shirya ya fita zuwa wani super market don ya dan sayi abubuwan bukata na gida. Tunda ya tunkaro wajen da motar shi samarin dake tsaye suna hira suke satin motar tasa har yazo kusa dasu ya wuce. Daga cikin su dayan ne ya sake murza idanun shi ya duba da kyau idan ba idon shi ke masa gizau ba tabbas modibbone a motan yake tukawa . Da mamaki ya bishi da kallo tare da fadin yaushe guy din nan ya dawo garin nan ? Abokan shine suke tambayan shi ko yasan shine yake fadin mijin Naziface fa datake aure suke zaune a kasan waje dashi. Kai mutumina kace zaka dauko muna dani ke nan ashe wata rana mu faso gari a cikin sa yace ku bari kawai aisai na dana motar nan kota halin kaka duk shi din jan wayane shegen kanshine sosai shima. Har ya sawo abinda zai sayo din ya dawo ya wuce su a wurin bai shedama akwai mutane a aurin ba lokacin. Sai bayan sati dayane ya shigo cikin gida ya samu yar nazifa na kuka yake lalashin ta kafin can yace dasu ke nazifa ashe mijin ki ya sawo wata kafiran motane da zai dawo ? Da mamaki kowa ke kallon shi har mahaifiyar su yace Allah wata rana zai ban motan nan in dana ta don nima na faso gari zama cikin salebiritin garin nan. Mahaifiyar nasu tace kai ina kaga mijin ta a garin nan da naka shirmen kuma yace kai ji mama fa ? Shi modibbo din ne kuma ban sani ba ko me sau nawa ina haduwa dashi saidai kin san sbi da ahegen daukan kai yasa nima nake kyaleshi . Sai dai mota kan saina dana motan nan nasa komai jin kan shi kuwa don nayiniyar hakan a zuciyana. Na shiga ukku modibbo fa dan wajen Addah kacw ka gani yace tun yaushe nake ganin shi a garin nan. Hankalin Nazifa da uwar yai mugun tashi tana fadin mama ya dawo kasan nan ban sani ba ke nan ko me mama ? Bar dan iska daga shi har uwar tashi Addah idan ma wani makarkashiya suke kullawa ga hakan zasuyi kunya indai nice. Don wanan auren mutu karaba dake dashi a duniyan nan har udan mashi din zubairu ya gani din. Kira layin sa mu gani idan zai shiga mu tabbatar da zancen zubairu din idan da gaskene don shi ya faye shirme wani lokaci. Nazifa ta dauki wani layi tana kiran shi sai kiran ya katse don yayi blocking din layin ta ga baki daya ba zata sameshi ba lokacin idan bashi ta cire hakan ba. Kira barkatai yana mata haka ta kalli uwar tana fadin kiran yaki shiga umma kanwarta dake gefe tace da ita. Mama a gwada kiranshi a layina idan zai shiga mu gani ana saka layin aka kira sai kiran ya shiga saidai bai daga kiran ba har ya katse. Duk sun zuba mata ido ta dago tana fadin kiran ya shiga saidai bai daga kiran ba a lokacin don dama yana suspecting din kiran nasu ne ya shigo mai don ba mai kirashi da baida layin shi a wayan shi. Gashi kuma ba kowane yasan da yana kasan ba da zai kirashi washe gari kuma ya nada ya tafi abin shi bai dawo ba ko mommy bata san yayi tafiya zuwa Abuja ba wani aiki a lokacin. Washegari bayan sun gaji da zancen ne suka kira layin hjy Addah kira uku bata daga ba don in takirasu haka suke mata sai anga dama a daga mata kiranta. Gashi ta rama kuma sunajin haushin hakan da tayi suna fama zunduma mata zagi sai gashi ta daga kiran. Suka gaisa sama sama kafin suce da ita ashe moddibbo ya dawo garin bamu da labarin hakan hjy tace dasu oh baku da labarin dawowan shi ashe yanzu ko ai sati uku yake nema a garin nan ke nan. What sati uku Addah amma daga ke har dan naki baku da mutunci ashe haka in ba aure kaddara bane mai zaikai Nazifa auren modibbo har kuso ku rainawa mutane wayau haka. Kashe wayan mommy tayi don zuciyan ta ba zai juri jin wanan zagin da hjy din take mata ba alokacin . Don zata iya ramawa hakan kuma zai haifar da matsala sun yi ta kiranta taki daga wayan sai da suka hakkura suka kyaleta.
Chapter 127 · 0% Book details