Sashe 294
Ana Dara Ga Dare Yayi Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read
addua shine takobin mumuni Allah yasa albarka a cikin rayuwan ku ga baki daya. A hankali na samu kaina da amsa mata da amin mama nagode ta kara da Allah yai maki albarka na amsa da amin again. Komai yai farko yana da karshe akace yau gashi mun kare lafiya zamu tafi washegari kowa zuciyar shi cike da zumudin hakan. Don tafiyan namu an kara kwanaki saboda yan kwanakin da yayi bai iso ba haka yai cuku cuku aka karawa tawagan nageria din kwanaki yakuma bi kowa da alheri mai tsoka a wurin. Ban so sake haduwa dashi ba har mu bar kasan amma da gajiyan nan muna dawowa masauki sai ga uncle hamza ya kirani . Wai mijinane yake son magana dani lokacin nayi mamakin jin hakan a bakin baffah din shi ba zai iya min magana ba ke nan komai da zai hadani da baffah a lokacin. Wani wawan tsuki naja bayan mun gama wayan dashi lokacin na wurgar a gefena suka kalloni dafa inda suke zaune don wayan har yacin ma faiza lokacin. Lafiya ta tambaya tana kallona idona daya cika da kwalla na sauke a kanta cikin takaici ina fadin jimun wanan mutumin fa wai uncle ya fadawa yana son ganina a yanzu zamuyi ban kwana dashi zai aiko a tafi dani masaukin shi. Masauki ta fada tana kwalalo ido waje nace rainin hankaline nafishi iyawa yanzun nan zan gwada masa kuwa. Da sauri na mike kanar ina shiryawa saida nagama tsab ne har faiza tana tayani tana fesa min turare . Sai suuu na koma na kwanta saman gadon tare da dafe kaina ina fadin washh ina fadawa na fasa kara mai firgitarwa duk suka rude lokaci guda . Yaren yarbanci na fara yi da sauri fatima ta nufi kofa sai dakin su umma take fada masu abinda ke faruwa. Ai sai gasu tare hankali tashe sun shigo dakin namu tundaga kofa umma ta fara jin abinda nake fada tace dasu. Ai mutanen kantane suka taka mata ashe har a kasa mai tsarki suna hawa kan mutum haka nan ta shiga shafana sai wani sauti nake sakewa kas kasa gaba daya duk wanda ke dakin zai iya jin hakan . Hankali tashe mama ta kira su baffah tana fada masu yace yanzu fa muka gama waya da ita saidai dama naji muryanta ai wani iri can. Sai gasu dakin suma a cikin tashin hankali sun shigo don baffah yazo da niyar ya fatatake ni ne sai ya samu abinda yafi karfin shi a dakin. Sai gasu sun koma ban hakkuri jin har abinda bai taba fadawa wani yana da niyar yiba ana zakalo mashi da kaf labarin wurin aikin shi . Da sauri ya shiga bada hakkuri yana fadin ba karya mun yarda daku mmdon munsan a kwaiku kamar yadda akai dan adam shima. Nan ake fada mai ai yarsa na can kwance don shi ya tabo su ya batawa godiya rai ummace ke fassara masu duk abinda na fada a cikin harshen yarbancin wani kuma in yazo da turane suna jin abinda suke fada. Text ya turawa mukhatar din yana fada mai abinda ke faruwa shima yaso daga hankalinshi amma baffah din ya kwantar mai da hankali. Abinda basu sani ba shine turarena na shaka suka taso min don gaskiya na dade wanan matsalan bai taso min ba haka don gaba dayan su dakin ranan sun gaskanta hakan. Sai dare sosai suka samu ya lafa min amma gaskiya koni nayi dana sanin yin hakan aiko da sassafe sai gasu har hjy tashi sun shigo gaidani ina kwance sharkaf dini don jikin da naji din. Hajiyan tasu ke fadin kai tana da wanan matsalan ne haka dama umma tace ai yanzu ma yai mata sauki ke nan sosai sama ga da can baya. Don tana kai sati daya tana fama da wanan laluran idan ya taso mata daga gefe baffah ke fadin ni ai na sheda yanzu. No Wonder yarinyar nan take tsatsaye haka ashe manyan abubuwane haka saman kanta zancen yata data fada wallahi na kira suke fada min sati ke nan suna fama da ita sai jiyan nan suka baro asibiti. Haka dai kowa ke fadan albarkacin bakin shi a wurin suna tsaye sun kura min ido kowa da abinda yake sakawa a cikin su. Murya a sanyayye yake fadin uncle ko zamu daga tafiyan nan ne har taji sauki da sauri umma ke fadin yanzu data falka insha Allahu zata ji dama. Zuwan daine na yanzu suka zo mata da karfi sai hjy nasu tace ai da kawai a dage idan sauran zasu tafi tunda sun shirya sai su tafi su. Nagodewa umma data kafe da ai kawai a bari mu tafi zaifi koda an tsaya din ma duk abin dayane a can kuma za a samu a karbo min magani inda ake karba ai. Da haka suka yarda da zancen umma har muka samu a ranan muka baro kasa mai tsarki zuwa gida nigeria.