Sashe 316
Ana Dara Ga Dare Yayi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ko ina na dakin tsab yake ba dakin ba har gidan duk Fatima tabishi ta gyara ta saka kamshi tare da taimakon wanan matar da hjy ta turo ta taimaka min . Don haka gidan ya kara haske ga nutsuwa ba wani hayani saina kiran da fatima ta kunna dake fitowa daga dakina a hankali, yana kuma karama mai sauraron shi natsuwa. Don duk dakin muyi shiru muna bin karantun a lokacin ciki ciki yayi sallama daga kofan tare da dan jira mu amsa mai don yasan ba ni kadai bane a dakin balle ya shigo ciki kai tsaye. Kamar sallama ko anty haka yasa na dago kai daga kallon wayan da nakeyi lokacin ina mai kallon kofan nima. Wanan karon nokin yayi don yana zaton bamuji sallaman nasa bane haka yai daidai da budan kofan da fatima tayi da sauri taja baya tana mashi sannu da zuwa. A cikin fara,a ya amsa yana fadin a a badai tsoro yasa kuka shige daki ba a wanan lokacin dare baiyi ba is just past nine yanzu fa ? Tana murmushi daga inda take tsaye take fadin muna dai hirane a nan shiko duk maganan da yakeyi a lokacin hankalinshi yana a kaina. Ya karaso ciki yana fadin idan zaku shige ku dinga saka key daga ciki saboda tsaro duk da akwai masu gadi dags wajen gidan amma hakan is not safe gaskiya. Da hausan shi yake maganan da fatima kafin daga inda nake zaune bakin gadon nake fadin nothing will happen koda masu gadin ma basu ai a cikin hausana dana iya. Kallo Fatima yayi a inda ya barta sai yaga har ta fita dakin ko alokacin yaci gaba da fadi cikin mamaki so you are hering the languege abi ? Not long na bashi amsa ya karaso har inda nake zaune yakai saman gadon kusa dani har jikin mu na iya guganna juna sosai a lokacin yake fadin. How far my Lady kada kiyi fushi dani please aikine da wasu baki suka zo min dashi ya hanani zuwa nan in time kiyi hakkuri da hakan don Allah. Haba haba don't say that to me again ko ba baki ai akwai iyali dole ka gana dasu and beside you are my elder you have the right to do whatever you like a rayuwanka bani da matsalan haka sam na fada a cikin ladabi da iyakar gaskiyana a fuskana. Murmushi yayi tare da kai hannunshi sama hannuna yana fadin nagode da kika zamo mai fahintar hakan amma yana da kyau na tsare maki hakkin ki koba haka bane? Ya tambaya yana kokarin son mu hada ido dashi sai dai sam ba zan iya hakan ba a lokacin don ni din jinin hausa fulanice ko yayane akwai wanan kunyat a jinina na addini dana al,ada. Dukar da kai nayi don na gane me yake nufi sai naji yayi murmushi tare da fadin anyway anything to eat ko sai an fita an sayo aci ? No mun riga mun yi girki for the first tima bayan hakan banda ra,ayin cin girki waje ga rayuwana nafi ganewa na girka muci. Masha Allah Alhamdullahi sahiba akwaiki da abubuwan mamaki na rayuwa ga wanda bai sanda hakan ba zai dauka ba abindata sani game da rayuwan duniya don tashin da sukayi a cikin bariki. Farko abindaya tuna shine yadda ya bar gidanshi a cikin tashin hankali da fitina kan zaizo gidan sahiba din ya kwana. Gashi yadda ita sahiban ta nuna mashi ba komai zai iya kasancewa da iyalin shi ba damuwanta bane hakan, shin wanan maganan nata gaskiyane akwai matar da zata yarda da wanan a tsakanin ta da kishiyarta ko ? Ko dai hakan na nuna cewa wanan yarinyar har cikin ranta har yanzu bata aminta da aurenshi da ita bane ga kuma zancen abinci da yanzu ta fada. Haka ya nuna cewa kuma tana shirye da ladabi akan auren su ko zama dashi ke nan donga Falmata haka kawai zata kwashi iska afima shekara sai abincin fizza da sauran ire iren su zata dinga sa akawo suci duk da tasan baida bukatan hakan a rayuwan shi . Shi mutum ne da yafi bukatan irin abincin mu na gida da al,ada ya koyar damu cin shi don hakane idan yana Nageria koda tare da iyalinshi yazo ya kwanmace da yaje gun mahaifiyarshi yaci abinci a can . Kokarin mikewa nayi tsaye sai naji ya mayar dani na zauna muna fuskantar juna dashi da sauri na mayar da kaina a kasa don kallon da yake min yasa gabana faduwa lokaci guda. Kin gaji da yawa ina zaki yanzu ya fada kamar me rada yana kokarin mayar da bayana saman katifa dan rutse idanuwana nayi kafin nayi karfin halin fadin zan tafi falone na hada abinci don naga kamar a bukace kake dashi yanzu. Murmushi yayi irin na manya kafin yace ban fada maki hakan ba don ina son kasancewa dake ne kawai a yanzu naji dumin jikin ki na saurari muryan nan naki a kunnuwana. Jin wanan yasa na dan saki murmushin iya baki na lumshe idanuna kawai don ni nauyin shi da kwarjinshi yanzu nake ji musanman ma ida yana agaban nawa haka ? Balle yanzu da yazo min da wani abinda nake hangowa a tsakiyan kwayar idanun shi lokaci guda tun bayan shigowan shi daki. Ji nayi yayi min rumfa da kirjinshi lokaci guda tare da kokarin kai bakinshi a cikin nawa da sauri na kawar da kaina gefe da sauri ? Dan bina yayi da kallo kafin naji sautin ajiyan zuciyan shi yana mikewa zaune daga yadda yake din kada Fatima ta shigo ta samemu a haka ko ? Tana da hankali sosai ba zata shigo nan ba yanzu tunda kana ciki na fada tare da mikewa tsaye ga baki daya bin jikina yayi da kallo don rigan yayi matukar matseni ya fitar min da duk suran jikina a baiyane. Kusan duk haka dinkuna na suke don haka ni ban dauki wanan a komai ba a wurina shiko wani iri yaji lokaci guda yana dan lumshe idanun shi. A tare muka fito zuwa falon yana rike da hannu na muka tako a cikin natsuwa fatima tana tsaye a gaban dinning din ta kara gyara ko ina ga candles ta kunna a tsakiya da akai decoretion dinshi a jikin wasu glass an kawata wurin sai gwanin ban sha,awa. Tun daga nisa ya fara fadin a, a Fatima wanan aikin bai maki yaba ke kadai haja keyinsa tana dan dariya naji tace a, a wallahi bani nayi karasawa nayi kawai anty Sahibace tayi komai tunda da kanta. Da sauri ya kallo inda nake wai yana mamaki kamar karamin yaro yace kune duk da wanan aikin haka gaskiya ku daina aiki haka yana kallon inda nake daga gefen shi. Dan murmushin yake na sake haka yaja hannuna zuwa bakin table din muka kai zaune ya nunawa Fatima kujera ta zauna sai cewa tayi a, a zanci a daki alaman nauyi da kunya. Shima murmushi yayi tare da fadin au na tuna fulanine ku ai kunya ko zaki daina idan kina gidan nan ki zauna muci matata ta ciyar dake irin abincin da baki taba ci ba. Da alama dai shi mutum ne mai son barkwancin da raha sosai ashe kada ka yankewa mutum hukunci a lokacin daka fara ganin shi sai ka gama nazarin shi zaka gane hakan amma ganin farko na dauka ko magana aikine a gareshi. Bayan mun zauna jin abinda ya fada yasa na mike na fara zuba masu abincin na zata irinane shi saina zuba kadan ina kokarin juyawa yake fadin. Har kin zuba min ke nan kome na kalli abincin dana zuba din yake fadin kara min nikan aini da tuwo muna gaisuwan mutunci sosai dashi. Dauko wani ledan nayi na bude na zuba a plate din na gyara cup din ruwan dake gefen shi da plate din miyan ina dan tusunawa nace bissimillah. Nagode ya fada na juya na zubawa Fatima itama kafin na dauki plate na dauko leda daya na rabashi biyu saidai daya yafi daya yawa sosai na saka karamin a plate. Sai duk suka bini da kallo lokaci daya kowa na kallon abinda na zuba meye wanan din ya tambaya yana kallon abincin da nake kokarin zama inci din gaz kuma cibi na dora a sama. Samun wuri nayi nakai zaune wanan ma ai yayi mata yawa indai anty Sahibace sam bata cin abinci haka kamar kowa . No ki dinga cin abinci zaifi yanzu ba daya bane da wancan lokacin ko kina son yan kaduna su Fatima su raina da kiwona ne ? So ki daure ki koyi cin abinci please ya fada yana jawo plete dinshi zuwa gaban shi da kyau kafin ya fara da bissimillah. Zance ruwan miya nasha da dan naman dana zuba abinci kan cibi biyu kawai nayi na ture sai wayana na jawo dake gabana na fara dubawa. A hankali ya dago kai ya dubeni kafin ya juya ya kalli fatima data soke kai tana murmushi a kasa kasa don ganin draman da mukeyi dama tasan ba zanci komai ba ita. Ankai kamar minti biyar sai tura loma yake yana kurba ruwa lokaci lokaci muryan shine ya dawo dani daga sakon faiza da nake karantawa a lokacin. Badai kinci abincin ba ke nan ya fada kai na dago ina dan bata rai nace naci ya isheni haka tsam ta mike tare da fadin uncle saida safe. Ya dan bita da kallo kafin ya juyo gareni yana fadin idan baki saba da wanan abincin bane aida saiki girka wanda zaki iya ci koma meye ni zan koyi cinsa. Amma ba zan barki ki dinga zama da yunwa haka na kallon shi nayi cikin ladabi nake fadin wallahi i am OK with diis haka nake cin abinci ko a gidama. A hakan shine ci ya sake tambayana yana kallon plate din dake gabana a lokacin sorry sir iam OK! Lumshe ido yayi yaci gaba da cin abincin shi hankali kwance yana ci yana dan kurba ruwan dake gefen shi a hankali. Sai mamakin yadda yake cin abinci haka nakeyi a zuciyana kafin ya kusa gamawa ya dago kai tare da fadin. Zanyi kwana hudu tare dake a nan kafin na juya zuwa London