Sashe 174
Ana Dara Ga Dare Yayi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Don haka kawai naji gara in fada mai hakan don su sanda sanin cewa bawai surin su mukazo ba lokacin namu ne ya kawomu garin. Masangalin kujera na dafa ina kallon shi kanshi ya dan dukar a kasa kamar yana nazarin abinda na fada mai a lokaci. A kujara na zauna gami da ciro wayata dake ringing a daidai lokacin dan basarwa nayi har kiran ya katse na dago kai ina fadin . Wallahi ninace kada umma ta fada ma haka kada mu sakaka a cikin matsala kuma don aikine na yan watani ya kawo mu nan ba wai munzo zama bane nan kaduna kaji dalilin dayasa nace kada umma ta fadawa kowa muna nan. Abin mamaki ya bashi yadda na zauna nake maganan zakace wata babban mace ce a lokacin. Kafin ya juya wurin umma din yana tambaya tun yaushe kuks zo garin nan ke nan umma har ban sani ba ? Kafin umma ta fada mai nace shekaran jiya nan a takaice ya dan kara kallo inda nake saini kaina amsar bata bada ma,ana a gareni ba amma kuma hakan ne na shirya dama tun baizo gidab namu din har idan sun gano muna cikin kaduna. Kanshi kawai ya girgiza cikin wayancewa don yanayin yadda yaga ina masa a yanzu yace I na Ammar yake ? Wayata ta fara kara kafin ni ko umma mu iya cewa wani don idon daya zubo min na mamaki komai da nakeyi a yanzu din. Daga kano suka kirani suna min bayanin irin abinda suka sama a wurin da wullakancin da manager da suka sama yayi masu don bai ko yarda an zauna dashi ba bama balle har su fara aikin da sukajeyi a can sun kira oga sin fada mai yace su sanar muna nan kaduna. Ku dawo nan kaduna kawai kada ku kara kwana a kano din zan shiga da kaina next week in Allah ya yarda. Yemisi ta karbi wayan tana maganan banza da dan sauri sauri nake magana dan haushi kawai sai na katse layin. Na dago kai na kalloshi sau biyu muna hada ido dashi yayin da nake wayan don haka ina gamawa na mayar da hankalina a wurin shi. Daga umma ke zaune take fadin sun samu matsalane acan din ko na gyara zama ina fadin dama nasan hakan zai faru tunda mutane basa son gaskiya yanzu . A sake ya dago yana fadin suwa ke nan umma kaida gani kasan a cikin dauriya yake maganan tasa lokacin. Umma ta fara zuba mai labarin abinda ke faruwa duk da daure fuskan danayi lokacin amma haka ta labarta mashi komai game da zuwan mu din. Kanshi ya kara girgizawa kafin yace dani wani company ne a cikin kuke bincike a kai ya tambaya yana kallona. Madaidaitan idanuna na lumshe kafin nace dashi na maigidan mu dake garin nan tare da yi masa kwatance yadda zai gane su. Kina ganin zaku iya da wanan aikin kuwa da kuke rainawa a yanzu don nasan masu hurda a wurin a baya can shu,uman mutane sosai don haka yawancin baki masu masana,anta a garin nan suke kuka dasu. Na sani yaya saboda hakan ne ai na zabi nazo nan din don sanin irin halinsu danayi tun kan muzo din. Kibi a hankali don yanzu mutane sun baci sosai balle suna ganin ki karamar yarinya haka dake zasu nemi illanta maki rayuwan ki. Nasan komai yaya a kansu har dama abinda basuyi tsamanin zan sanshi ba game dasu don haka zan gwada sa,a na a kan su yanzu. Haka nada kyau idan kuna da wani matsalan da sai kun nemi taimakon mu zaki iya kiran layina insha Allahu zan taimaka maku dashi. Nagode yaya Allah ya kara girma amma nasan basu shirya yin lalama akan matsala ba don tun yanzu sun fara kawo muna hari akan aikin sun gamu duk yarane ba wanda yakai shekarun su a cikin mu. Mikewa yayi yana fadin mama ni zan tafi dama wanan tracker din ne ya jawoni a yanzu sai na sake juyowa da fatan baku da matsala a yanzu dai a nan ? Bamu da matsalan komai a na gaskiya don komai kawo muna shi akeyi basai mun saya ba ta fada mai cikin kulawa. Ok ni zan tafi ya fada lokacin kuma na mike tsaye nima ina fadin mungode ya tare da bin bayan shi dan dan kallona da umma tayi lokacin. Har bakin motar shi na rakashi ta juyo a yana fuskantana a cikin karamar murya ya kira sunana yana fadin . Kuyi hakkuri nasan abinda akai maku mm a banza daku a cikin duniyane yanzu yake maki zafi har nake ganin kamar shima ya dawo gare mune don ya cuta muna yanzu. Banyi magana ba sai wasan da nakeyi kawai da yatsun hannuna lokacin a karshe dai ya kara da bamu hakkuri har yake fadin yanzu haka a kan case din mune yasa bai koma ba don akwai binciken da yakeyi a asirce ba tare da kowa nasa yasan yanayi ba. So yake ya gama kafin ya fito masu da zancen a banza shine dalilin daya kira umma din har ya gane muna kaduna a lokacin. Idona ne ya kawo kwala kafin nace dashi ai dama kabar wanan zancen inda suka aika muna mahaifi gaba dayan su can zasu tafi ai idan anje lahira Allah yai masu shari,a a can. Don wani tone tone a yanzu sai nake ganin baida amfani tunda sin riga da sunci dukiyan ko nake gani a yanzu tunda Allah ya fitar damu daga kangin wahala da a bar zancen kawai zaifi a yanzu kada rayuka su baci don naga akwai wa yanda basa son zancen. Shiru yayi ya dukar da kan shi kafin ya ce dani sai anjima idan kuna da wani matsala ki nemeni a waya zan taimaka maku dashi in Allah ya yarda. Yana fadin hakan ya shiga motan ya tayar ya bar unguwar namu a hanlali na jawo kafana zuwa ciki ban zauna a falo ba don umma ma bata falon na shiga ciki. Wanka nayi kafin na fito na hada muna abin karyawa muka karya dashi na koma daki na kwanta. Gwago Hari ce da kanta taje airport ta dauko dan nata cikin jin dadi da nuna kulawa a gareshi sai wani haba haba takeyi dashi lokacin kamar dai karamin yaro. Agida kuma tarbo na musan man ya sama an shirya mashi duk saboda dawowan shi wanan wahalar da kai din da sukeyine yasa baison fadawa mami din nasa dawowan shi saidai su ganshi kwatsan ya shigo garin. Bai tsaya falon su ba kai tsaye bayan gaisawan shi dasu gwaggo Asiya dasu mommy da aka gaiyato suzo taron dan lelan kai tsaye ya shige part din shi ya barsu zaune a falon. Wanka ya shiga duk da baida wani datti amma yana jin kansa a takure lokacin son haka yake ganin watsa ruwan zaifi mai sauki. Bin bandakin yayi da kallo na dan lokaci kafin ya fito ya dan sauya kaya wanan karon zuwa riga da wandon yan Pakistan mai laushi har farin singleting shi na maza yana haskawa daga cikin kayan. Yasan suna jiran shi a falo aci abinci don inda sabo ya saba da irin rayuwan mami din nasa kan yadda take nuna masa rsagwaran so zalla a gaban ko wayema zata gwada hakan. Ya samu ma sun karu a yarda ya barsu a baya faifan Nazifa suka bude a gidan kan iskacin da tayi masu a gidan buki da sujaje. Har gwaggo Asiya tayi mata magana bata ganesu bane halan ta zaune yadda take take fadin na ganeku mana ba su gwaggo Asiya bace bata kuma gayar dasu din ba ta kyalesu. Wanan yasa duk ta kara fita cikon ransu shine yanzu gwaggo Asiya din ta tayar da zancen suke mayar da magana akan abinda ya faru a ranan. Fitowan Almustaphane yasa suka dan sassauta muryoyin shi daya karade falo gaidasu ya sskeyi kafin uayi kokarin samun wuri yana kaiwa zaune. Gwaggo Asiya tace zaka zauna kuma bakaci abinci ba dan murmushi ya sake yana fadin a koshe nake yanzu mama sai zuwa dare zanci wani abu. The boy kayi wanan uwar tafiyan mai nisa kace ba zakaci komai ba yanzu maza muje danning ko wani dan abu ka taba a ciki. Tashi sukayi zuwa cin abincin shikan zaune yake kawai a wurin yana kallon uban abincin da aka zuba mai cilin plate a gaban shi gashi bai iya mussa hakan. Ya dan yi spoon uku da kyar ya dauko abin goge bakin shi yana gogewa da sauri uwar ta dago kai tana fadin boy zamuyi fada yanzun nan . Murmushi yayi yana mikewa tsaye tare da fadin zan ci anjima mami idan na dawo yanzu ina son hutawa ne kadan ya dan rungumi uwar tashi. Nan ya barsu zaune sukan suci abincin su sosai basin sun rasa a gidajen su ba sai don marmari da kuma haduwa da juna. Basu bar gidan ba sai da akayi sallah la,asar kowansu ya kama gaban sbi cikin jin dadi da kasancewa da junan su a lokacin. Daga gidanshi yaje gidan su ya dubasu ya samu mommy bata gida Nabila ke sheda mashi inda ta tafi din ranshine yaji ya baci sosai. Ya rasa meyasa suke bata lokacin su akan wanan mara tarbiyan da gata yayiwa yawa har baisan abinda yakeyi ba bai kallon kowa da daraja yana ganin kamar yafi kowa. Bai zauna ba yayi masu sallama suka suna masa magana yake fadin zaije ya dawo ya gansu ya fice daga gidan . A get motan su ya hade dana mommy din dake dawowa ita da gwaggo Asiya yana gani su ya bata rai a tsatsaye ya tsaya ya gaidasu ya wuce. Mommy ta fahinci dalilin sharesu da yayi a lokacin don haka ta danji ranta ya baci a lokacin yadda ya nuna masu din. Ta shiga cikin gida su Nabila suke gaida da ita ta amsa tana zama tare da tambayan Nabila din yayan ku ya shigo gidan nan ko ? Me kuka fada mashi daya shigo gidan nan mun fada mai inda kika tafi gidan gwaggo Harira wurin dawowan ya mustapha. Dariya sosai Fa,iza ta kwashe dashi lokaci guda duk suka juya suka dubeta suna mamakin abinda takewa dariya