Sashe 63
Ana Dara Ga Dare Yayi Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read
dan koya a wurin umma din bane muka iya. Sai lokacin na samu daman gaidashi da wuni ya amsa min a takaice yadda ya saba ba sakin fuska a gareni ko kadan . Magana sukeyi da umma din wanda bana fahinta kan me suke maganan yayin dana dan saci kallon shi da kyau a lokacin ne kuma na fara tunanen a inda nasan shi farkon ganina dashi. Sannu a hankali nake tunawa har na gane ai shine wanda ya zo wurun gasa masarana a lokacin wani tunane nayi nace watau ke nan tun a lokacin ya fara bibiyata ke nan. Nidai ko ma meye ya kaimu gida shine bukatana a yanzu don banda wani buri daya wuce in ganni a gaban yan uwana in san su su sanni abar kira muna da bamu da dangi. Muna yawan samun wanan matsalan tun dai zaman mu a Ajagule gidab su iya wale suna yawan yi muna wanan gorin kuma hakan yakan dameni sosai. Don haka na kwamacewa komawan mu gida a yanzu din wirin dangi zaifi muna ko dan tsare mutuncin muna zaman diya mata dagani har umma din da maza ke kawowa harin tayawa ko wani lokaci da sunan iskaci. Zancen kararun mu sukeyi da umma ta fada mashi komai kan dakatar da kararun mu din da mukayi a yanzu bama zuwa boko saidai neman abinda zamuciwa cikin da nakeyi a yanzu. Ya nuna rashin jin dadin shi ga hakan yake fadin ba zamu bar garin nan ba sai ya karbo muna transfer din mu ga hannun shi zamu tafi. Naji dadin jin wanan zance na karatun don a gaskya ina son yin kararu sosai a lokacin nan dai da yadda zanyi ne kawai yasa na daina zuwa din. Sun dan jima da umma suna hira kafin yayi mata sallama ya barmu sai a lokacin nake fadawa umma ko shi waye shine wanda ya ke ban kudin nan dana fara kawo mata a lokacin. Ummake fadin mena fada maki tun farko zuciyana ya bani run a lokacin cewa akwai abinda ke shirin faruwa damu a lokacin. Baki yarda da hakan ba yanzu ko kin yarda ko to hakana ma a can gidan da kuke son zuwa abubuwa zasu faru da dama kan komawan mu din cikin su da zamuyi a yanzu. Jikina nayi sanyu don na fara fahinta cewa dai akwai abinda umma ke nufi da hakan da take yawan fadi ko wani lokaci niko wanan wani irin matsala ne haka da zamu fuskanta gun dangin mu din kuma. Kwana biyu sai ga ya Abubakar yana fadin mu shirya zai tafi damu school din da muka bari mu an so transfer din mu. Dole muka bude wanan akwatin mu saka kayan daya saya muna din sai dai duka kayan bazan iya sakasu a jikina ba don ban saba da saka irin su din ba. Duk yadda umma taso in saka na kasa sakawa don ko zanin ban iya daurawa ba haka ya shigo ya samemu muna wanan rikici da umma din. Take fada mai yayi dan shiru kafin ya juya ya fita sai can gashi ya shigo da kaya masu yawa dogayen riguna masu kyau daidai size dina da wasu wando da riga sune daidai dani ba wanan daya sayo din da farko ba. Na saka wandon jeans da yar riga daya dace mai dogon hannu na kawo hijjab dina na dora sama sai naji wata daban can dani ga zafi da naji atake ya fara rufeni don hijjab din. Haka dai na daure muka tafi ba wani wahalan da muka samu don dan bayanin dayai masu kan rashin ganina din da basuyi ba . Sun taimaka sun bamu ba tare da yi min repeat ba din sun fada mai i can make it saboda ina da kokari sosai a karatuna din. A hakan muka barsu muka nufi makarantar su Amar can madin ba wani matsalan da aka samu sun bayar da transfer din yadda ya dace. Muka dawo inda yai muna masaukin dole din muka samu umma duk ta damu da dadewan da muka danyi bamu dawo ba a dakin. Kai zan iya cewa wanan bawan Allah yana da saukin kai don sai idan baka zauna dashi bane ganin farko zaka daukeshi wani maijiji dakai ko wani mugu can. Amma a gaskiya ba hakan yake ba sam don halin shi a sanyayye yake komai nasa don na dauka da umma tace dashi akwai abinda take son dauka a can dakin mu na semi na dauka ba zai yarda da hakan ba sam. Sai gashi tana fadi a cikin irin ladabi sa yace ba matsala zai kaimu mu dauko duk abinda mukeson dauka a can din kafin mu wuce. Wanan tafiyan ni yaiwa dadi don akwai inda nake ajiyan kudi a dakin ko umma bata san da hakan ba sai ni kadai nasan wanan abin. Haka aka kwashe mu zuwa semi din mukayi sallama da duk abokan arzikin mu na nan kan cewa zamu tafi muga gida wata kila mu dawo ko ba zamu dawo ba idan mun tafi din. An dan nuna jimamen hakan don sabon da muka danyi dasu nikan na faki ido na hako kudina da nake binnewa a dakin cikin kyalen da nake daurewa a cikin sa. Kudin na nan kamar yadda na barsu ba a taba ko kwandalaba a cikin shi duk da mun samu an dan taba kayan dankin an binciki dakin ga baki dayan shi. Duk da wanan halin ba bakon abu bane a wanan garin don da zaran kadan daga na kwana biyu hakane ke kasancewa ga mutum dama. Mukai sallama tare da amsan laban wayoyi idan munje zamu kirasu yadda mukace dasu ke nan a lokacin. Haka muka rabu dasu ba dadin rai don sabon da akayi da juna na dan lokaci. Mun dawo hotel din da muke ne da kwana biyu ya gama duk wani shirin tafiyan mu din zuwa arewa a daidai lokavin mahaifinsu daddy ke nan shima ya dawo kasan da kwana biyu. Zo kaga murna kan don ma umma ta hireni da abubuwa da dama kafin mu fito tayi warning dina sosai kan na kama kaina da kowa don kada a samu a cuta min ga hakan. Karfe shida na yamma muka bar lagos zuwa kaduna state din da nake jin labadin shi a cikin tarihi ashe dama nan ne state dinmu ashe.