← Book details Ana Dara Ga Dare Yayi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 236 OF 337

Sashe 236

Ana Dara Ga Dare Yayi Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

ake fadin kokuwan kine yasa yake kwance muna rokon a sassauta mashi idan hakane . Ni ni ai ban masa komai ba a yanzu zagin mahaifina yayi muka dakatar dashi don yasan ba abinda zai iya babu babu . Amma baffah kun ban mamaki da kuka zauna kuna kallon yadda yarinyar nan ke kokarin zuba muna rashin mutunci kuna zaune kuna kallon ta wai iska ko iskancin . Kaita kanka tukunna kafan ka idan bakai hankali ba har abada ba zaka tashi ba shine ajalin ka shi zai kaika kamar yadda kuke kai mutane lahira. Ka tuna shi kukaje kashewa a ranan kaida yaron ku dake kwance a yanzu an rasa meke damun shi akan fadan baki kukaso kasheshi a ranan. Kaf na basu labarin shirin su a lokacin Ya Abubakar ya shigo falon shida su baffa Abdullahi kaf nabasu labarin komai dake aike daga bangarena. Har kisan Abban mu da sukayi da rabon komai da sukayi iyasu da abinda suka tsorata daddy dashi a lokacin har ya karbi abinda suka bashi daga ciki. Aradu yarinyar nan manyace baffa gyade ya fada lokaci guda kai kai ka daina fadin hakan a fuskanci abinda ke gaban mu yanzu tsohon ya fada. Kai ina wanan yarinyar ta gama damu ta shuci rayuwan mu ke har kin isa ki muna wanan tonon silar idan da a bayane shan. Kun dai yarda kun aikata ke nan baffa hamza ya tambaye shi a fusace yace in Nuhu yashe ya yarda ba idan bai sheba muma ba zamu sheba don ya fita sheri kun sani. Daga bayan su baffah Buhari yace nikan na yarda na kumayi nadama kai Ali dcp ka sani ba yauba na fada maka komai ko a lokacin barazana da rayuwana sukai min kuma da kurciya a lokacin na fadama komai ai ? Kallon daddy modibbo yayi yana fadin why daddy why ka aikata haka akan dan uwan ka sai yayi shiru don hawayen da yazo mashi a lokacin. Kafin yace nasan komai daddy na sani tun lokacin dana dawo na samu kafita wanan zancen nake kwankwanto a kanka har yakai naje na bincika file din case din wanda mutanen kan sahibane suka fada min inda zan sameshi. Ikom Allah dayan tsohon ya fada yana kara kallona yace wallahi tsoho su suka fada min inda zan dauko file din don wanan yarinyar da kuke gani ta wuce yadda kuke kallo ayanzu kan komai. Wanan case ne daya shafi hukuma don haka dole abar yarinyar na akan karan da tayi baffa hamza ya fada idan munce a rufe wanan magana a gida haka dole dai zancen nan fita zaiyi waje ku sani. Haka su masu bin hakkin su ai kunga bamu kyauta ba idan an kyalesu a haka ana kallonsu su kansu zasuga rashin adalcin mu a nan don haka wanan zancen bana gida bace bafa a yanzu. Hamza nasani ba yauba kake son ganin bayan mu wanan zance nata ina shedun ta idan haukan ta ya bata haka tana shara karya har kuna yarda muma ba kyalesu zamuyi na bana muna suna da suke son yi tunda bata da sheda kan hakan . Ya yun kura tare da daukan sandan shi ya mike tsaye ya kallo inda muke yana fadin zaku gane ba a taba mu a wayen lafiya gaba daya sai nayi karan ku kotu kan kokarin bata muna suna da akeson yi har kai hamza da nake ganin kana kokarin mara masu baya su bata muna suna. Au haka kace to jeka kayi karan don Allah Allah ya kaika kaje karan su ke kuma zaki san kin tamu a garin nan karshen iskanci kikeyi yanzu. Idan uwarki ta shiga bariki dake kin tashi a gaban yan jagali kin kwaso hauka kinzo muna kina barazana nan kaniyar ki zakici wallahi yana kainan ya fita fuuu kowa ya bishi da kallo. Lalai zance na kasa don hauka na damun wa yan nan jahilan da suka dauki hukuma wasa baffah Abdullahi ya fada a cikin mamaki kafin ya juya kan Alh buhari yana fadin . Yanzu kaima binsu zakayi kuyi kara ke nan kome ya nisa yana gyara zama yace gashi nan ku tambaye saunawa ina zuwa wurin shi kan wanan maganan. Don haka wallahi ni yanzu a shirye nake da duk irin hukuncin da za ayi min muddin shine zai zama yafiya a gareni kan kuskuren da muka aikata duk da nasan bani cikin kashe shin da sukayi. Amma kuma nasan sune ban fada ba don tsoron su da nake ji a lokacin kuma sun bani rabo na karba daga ciki ina amfani dashi. Nuhu ne da shi gyade sai abokan shi mutum biyu Alh Shafi,u da Alh bello su suka aikata hakan ina waje ina jiran su a lokacin . Don na dauka abinda suka kace zasuje yi wurin shine ya kaisu sai washe gari labarin mara dadi ya zo muna na mutuwan Sambo din. Hankalina ya tashi sosai a lokacin don wanan abinda suka aikata ga dan uwan mu tun lokacin naso in fadi gaskiya amma sai suka kulleni a dakin bello sukai min barazanan kasheni nima idan na fadi gaskiya har kawo wa yau din nan kulun a cikin barazana suke min duk lokacin dana yunkuro masu da zancen. Ko lokacin da yarinyar nan ke fadi daya tura a kashe mai Alh Ali nayi iya kokarina don inga na haja faruwan hakan amma basu saurareni ba. Daddy hular shi ya cire ya goge zufan dake tsiyayo mashi daga cikin kanshi don tashi hankalin abinda kunuwan shi keji mai a lokaci. Zuwa wanan lokacin duk wani wanda ke falon kuka yakeyi wiwi hankali tashe tsohon yace tir tir da hali irin na Nuhu da gyade. Alh wanan maganan dole sai anje ga hukuma don ita kadai zata warware wanan manakisa nasu kai tsaye idan ba hakaba ko yanzu tsugunne bata kare muna ba a nan. Ganin suna kan tataunwa akan zancen na mike zuwa ciki don ba zan iya zama ina sauraren wanan abinda ke kara daga min hankali ba haka. Ya mustaphane zaune saman dining ya dafe kanshi da hannuwan shi bibiyu shima a cikin tashin hankali don duk abinda ake fadi daga inda yake yana jin su. Yana jin motsi ba tare da yasan ko waye ba ya dago nice ya gani naji ya kira sunana a wani yanayi hakan yasa na tsaya a inda nake ba tare dana juyo na fuskance shi ba. Mikewa yayi ya tako zuwa inda nake tsaye din ya yazo ya tsaya har muna iya jin hucin numfashin juna a lokacin don irin kusantar juna da mukayi . Hannuwan shi ya fara hardewa fuskan shi ya nuna alaman damuwa a cikin sa sosa yasoma fadin nasan an cuta maku sosai a rayuwan ku. Ban san ma da wani ido zamu kalleku ba a yanzu a matsayin mu na yan uwanku alhalin muna dashi muka bar rayuewan ku a cikin wahala haka. Saidai ina son ki sani duk wani abinda za ayi a kotu don muga an hukunta mutanen nan ki sanar dani wanan zaluncin nasu ba zai tafi a banza ba insha Allahu. Kaina dago na kalleshi tare da dan sake murmushi ina fadin mungode saidai duk wani shiri da zanyi kan hakan na riga na shirya a yanzu ba sai an taimaka min ba. Oright hakan yayi kyau ya fada har na fara tafiya naji yace saidai ki sani dis is arewa not lagos ko yayane sai kin nemi taimako a wani wajen. Ba damuwa na fada ina shigewa tare da fadi a raina da kasan dalilina kin kowa ya jefa kanshi cikin wanan fitinan da kowa yanzu ya fahinceni.
Chapter 236 · 0% Book details