← Book details Ana Dara Ga Dare Yayi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 56 OF 337

Sashe 56

Ana Dara Ga Dare Yayi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Yau kan da farin ciki na tashi duk da ina jin abinda yanzu ya zame min jiki ko yaushe har zan iya cewa na yau din yafi na kullun . Sai dai hakan bai dameni ba a yanzu don kamar ya zamo min jiki a yanzu din Nayi sallama da umma kamar yadda na saba a kullun idan zan bar gida na kama hanya zuwa neman sa, a a gari tare da tunanen ina zan dosa a ranan. Tsayuwana na gyara daga inda nake tsaye ina tunanen inda zan dosa naji murya a gabana a na fadin ekeja. Ban tsaya tunane ba ko la,akarin motan na going ya tsaya na shiga daga ni sai driver a lokacin daga shigana sanyi da kamshi ya daki hancina ban kara sanin inda nake ba sai dai na bude ido na ganin a cikin wani saki mai kyau dashi ga sanyin AC ga kamshi na tashi a dakin duk da dakin na da duhu a lokacin . Sai dai duhun bai hanani gane hakan ba abinda mutum bai saba dashi ba dole inga bambamcin ga hakan. Kokarin yunkurawa nayi don in tashi naji ban iya koda motsawa a lokacin innalillahi na fara fadi ina hawaye tare da tunanen shike nan na fada hannun yan mafiya ke nan a yau abinda kullun umma ke min addu,a kanshi ke nan yau na fada tarkon su ke nan Allah ka fitar dani hannun wa yan nan azzaluman lafiya. Ya Allah kada ka basu ikon cutar dani koda dingon kwayar zarah duk a cikin raina nake wanan adduan ni kadai a dakin kwace an dare min hannaye da kafa. Duk wani kokarin da zan iya don in kwance kaina saga daurin da sukai min nakasa yi gashi dakin shiru baka jin motsin kowa a cikin sa lokacin. Don zan iya cewa nikadai ne a wanan gidan ko daki zon rashin jin motsin komai da banyi tun lokacin dana falka din daga barcin dole dana tafi. Hawaye ya fara zubo min lokaci daya ba abinda nake tunane sai mahaifiyana da dan uwana irin halin da zasu kasance na rashi a yanzu. Kai hardai na gaji na daina kukan na koma ihu duk da banyi zaton akwai wani a wanan gidan da nake ba a lokacin ina nemam ceto da fadin. Somebody help me, help please, help help sai kuma na fashe da kuka mai tsuma zuciya lokaci guda. Nayi ihun na nemi taimako ba wanda ya lekoni dakin nagaji nabarwa Allah ikon sa na shiga yin addu,a ido rufe . Gaskiya tashin hankali baida dadi a rayuwa don nayi tunane kala kala lokaci guda har na rasa na kamawa a cikin tunanen nawa da nakeyi. A haka har dare ya riskene a wurin kwance a daure a cikin yanayin gala baita da tausayi ga duk wanda ya ganni a lokacin. Duk da ban san lokaci ba a yadda nake a dakin tun safe har wanan lokacin da nake tsamanin dare yayi a lokacin. Naji ana kokarin bude kofan tare da jin muryoyin maza a kokafan da alama kokadin shigowa dakin da nake din sukeyi.. Naji an turo kofan lokaci guda da yai daidai da shigowan wani dakin ke nan a lokacin nabi kofan da kallo tare da kallon wanda ya shigo dakin lokacin duk da duhun dakin nai bari inga fuskan maishi. Why d u tie her like dis naji an fada oga u no how dis gurl be criminal stop calling her with that name aka fada a cikin tsawa naji wanda akewa fadan yace sorry oga. Please don't cheat me sai kuma na shiga fadi da yarbanci suyi hakkuri ban masu komai ba idan ma nayi ban sani bane nayi na hada hannu a wuri daya ina basu hakkuri. Fita naga mai fadan yayi sai dayan yabi shi a cikin daga murya nake fadin su barni inje gida kada mahaifiyata ta shiga wani hali. Aka rufo kofan da karfi na sake fashewa da kuka mai karfi lokaci guda ina ihu duk hakan bai basu tausayi ba. Sai can cikin dare aka kawo min abinci ban ko kalle shi ba bayan maishi ya banye min hannu yake fadin ga bandaki nan ina iya shiga nayi alwala ga kaya nan nayi sallah. Yana fadin haka ya juya ya fita ya kulle kofan daga baya wasu hawaye masu dumi suka zobo min lokaci guda a wurin na samu na mike zaune da kyat duk jikina yayi min tsami sosai a lokacin. Haka na samu na sauka daga gadon da kyat na shiga bandakin daya nuna min din wuri ne lafiyayye ko da ganin yadda ban dakin yake . Bin ko ina nayi da kallo kafin na daure na dauro alwala na fito duk da naso nayi wanka amma tsoro ya hanani hakan don bansan a ida nake ba a lokaci. Ledan dake saman gadon na bude a hankali kayane irin na hausawa sai hijab babba da nake ganin wasu matan hausa dashi a jiki a ciki. Hijjab din kawai na dauka nasa nayi sallolin dake kaina don a gaskiya bana wasa da sallah a duk inda ya riskeni zan tsaya inyi shi don horuwa da hakan da umma tayi muna akan sallah. Ina nan dai dakin a zaune dare yayi don alaman daya nuna hakan a nan kasa na kwanta inata faman sheshekan kuka har barci ya sace ni a hakan ban sani ba. Sai gabanin asuba na falka naga alaman an shigo dakin lokacin ina barci don wani abincin da aka aje min gefe na duk banci ba. Kiran sallah nadan fara jiyowa sama sama haka yasa na mike na shiga bandakin na watso ruwa a jikina a gurguje don nasan wanan lokacin wanda suka kawoni nan suna can suna barcin su a lokacin. Hakan yasa na danyi amfani da wanan daman na watsa ruwa ko zan danji jikin nawa ya sake min a yadda nake jinshi lokacin. Sallah nayi na idar nake ta faman tunanen yadda zanyi in kubutar da kaina har wani dabara ya fado min. Plate din abincin nan na juye na rike a hannu na ban yarda nayi nisa dashi ba daidai kofan na tsaya lokacin da naji ana kokarin bude kofan. Maishi yana sawo kai na daga plate na kai mai duka ya tare na samu hannun shi nayi kokarin gudu ta hanyar kusawa ta bayan shi har nakai wajen dakin na hango dogon korido ba kowa waje a lokacin. Daga kafan da zanyi naji an jawoni an mayar a dakin da karfi ina jhu ina fadin help help somebody help me please. Ba wanda ya leko har lokacin tsuki naji anja an fita tare da turo kofan na sake wani kuka mai cin rai. Na dade a zaune ba wanda ya kara lekoni dakin idona nakai ga plate sin daya tarwatse a kasa da alaman na samu maishi sosai ga dukan dana kai mashi din. Har zuwa karfe daya saura yan mintoci ba,a shigo dakin ba haka yasa na mike zuwa bandaki na dauro alwala gashi lokacin na fara jin yunwa a cikina. Don rabona da abincin tun daren shekaran jiya da mukaci abinci da su umma kafin na kwanta koshi saida umma ta matsa min na daure naci don barcin da nake ji a lokacin. Shine har wanan lokavin a cikina don abincin jiya da aka kawo min ya lalace ba zai ciwu ba saboda irin hadin da sukai mai. Can naji anturo kofa an shigo su biyune wanan karon da yake akwai hasken rana a lokacin haka yasani gane fuskan maishi saida na mike ina fadin. What have i done to you? You kidnap me here god go punish u for dis sin u made na fada ina nuna shi da yatsan hannuna a cikin mamaki. Common shutup ya fada a hasale yana fadin idan kina da sako gun mahaifiyar ki kiyi magana don yanzu zan tura a fada mata kina nan wurin mu, mun kama ki. For what reason ta fada muna abinda muke son ji a wurin ta idan mun kamata an jima jin haka yasa na zube ina fadin No No mai mahaifiyana tayi maku zaku kamata. Wayo kada ku kama min ummana bata da lafiya don Allah ku rikeni duk laifin da nayi ni nayi ba umma na ba na fada ina kuka. Basu tsaya saurara min ba suka fice abinsu ina jin ana rufo kofan dakin da nake da makulli aka rufeni a cikin dakin. Umma kan suna van sun shiga tashin hankali kamar zata haukace fun a daren da ban dawo gida ba lokavin dana saba dawowa. Haka suka kwasa zuwa bus stop din unguwar inda muke shiga mota suna tambaya koda wanda ya gani a wurin tare da nuna masu photona . Sai wani tsoho dan kamisho ne yace ya gane ni kuma yaga na shiga wata mota da ba bus ba da safe maishi yazo ya dade a gefen titi kafin can yazo nan inda suke a lokacin dana karaso wurin. Ihu umma tasa lokaci daya tana fadin shike nan sun sace mata yarta yar aamana a nan dai umma tayi ta sake magana saida su ladi suka jata zuwa gida a cikin duhun dare. Ranan kan, kan umma ladi ta kwana dole tana bata magana da ban baki haka suka kwana zaune hanlali tashe. Washe gari tun safe sukai shiri suka bazama zuwa cikin gari har gidan hjy halima suka so zuwa sai basu gane gidan ba don rudewan da umma tayi sai bata gane gidan ba. Haka suka juyo zuwa semi a nan kuma suka samu wani rabarin tashin hankali don ko gida ba, a bari sun shiga ba aka tare su da fadin wai yansanda sunzo neman umma din. Yan sanda kuma Ladi ta tambaya sukace yansanda kuma ba masu saukin kaiba don har da sojoji suka zo da motocin su nan basu dade da wucewa ba duk sun shiga gidajen unguwan nan dazun. Ai basu fargaba sai ganin umma ta tafi suuu kasa ta some sukayi nan kuma hankali ya kara tashi sosai. Aka kwashi umma din zuwa cikin gida sai da kyat Allah ya farfado da ita duk hankalin ladi ya tashi ranan don ta shiga tashin hankali ba kadan ba. Ranan dai a nan dakin mu Ladi
Chapter 56 · 0% Book details