← Book details Ana Dara Ga Dare Yayi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 254 OF 337

Sashe 254

Ana Dara Ga Dare Yayi Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

ba a nan aka fada Alkali na dagawa daga kujeran shi da yake zaune don an dade a wurin zaune ranan. Koke koke ne ya tashi a kotun lokacin guda wanda yan uwa keyi na tashin hankali ya dai tabbata ke nan cewa sune suka kashe dan uwan su ashe. Ga iyalin su kuma suna fadin an tauyesu ba a basu daman kare kansu ba ga kuma cin zarfi wai za a kwace komai da suka mallaka a dankawa yaran nan shine wani sabon tashin hankalin su a lokacin. Daga nan wurin sharian ko gidan kowa bamu leka ba aka wuce damu airport zamu bi jirgin yamma da zai tashi duk ko son ganin mu da aka turo text cewa daddy yana son yi a lokacin hakan baisa mun dawo ba muka bar masu garin suna a cikin tashin hankalin halin da zukata suka shiga lokacin. Saukan dare mukayi Abdulne yazo ya dauke mu daga airport ya kaimu gida tun a hanya suke hira da umma ban saka masu baki ba har muka kai gida. Daga shigan mu dakina na nufa na kwabe kayan jikina da suka dameni na shiga wanka na fito na tayar da sallah don rama sallolin dake kan mu. Karfe goma da rabi na gama komai duk da banci abinci ba amma wurin kwanciya nake nema in kwanta lokacin don yamayin da nake jin kaina abu ya tsaya min a makoshina lokacin. Abinci muniya ta kawo muna amma ban iya dagawa naci ba har barci ya dan daukeni ban kara sanin inda nake ba kuma a lokacin. Washe gari hakan yasa na tashi ina jin yunwa sosai a cikina na fita neman abinda zanci din nan na hada cooker orth na zauna nasha lokacin umma ta fito daga dakin ta zuwa wajena a falon. Sai bayan ta zauna nake gaida ita ta amsa take fadin wai mutane basu da kunya yau daddy kune ya kirani yake tambayana muna ina zaizo ya same mu. Kin fada mashi munbar kaduna tun jiya na tambaya a gagauce tace na fada mana nace muna lagos mu tun jiya ai daga kotu airport muka nufa ai. Wai sai yake fadin don me zamuyi haka bayan ga yadda aka aje magana damu ido na tsurawa umma dake min bayani sai cewa nayi amma yaji abinda kika fada a kotu ai don haka ya rike komai shiri tsakanin shine da mai dukiyan na kashe waya. Dan murmushine ya baiyana min a fuskana ganin yanzu umma tsoro ko nauyi ya fara fita a idon ta a yanzu. Mun dan taba hiran abinda daddy ya fada a cikin kotu din kafin mu sauya hiran namu zuwa na yan uwan umma dake yola. Irin yadda suka nuna muna karamci da jin dadin ganin mu da sukayi a lokacin jin nayi shiru lokacin da take min bayanin yadda suke da kowan su yasa ta dan kura min ido tare da dakatar da maganan da take min din tana kallona . Nayi zurfi sosai a cikin tunane a lokacin don haka ban gane hakan da wuri ba sai dana sauke ajiyan zuciya na dago kai nake tambayan ta da cewa. Dama wanancan kauyen shine asalin kauyen iyayyen mu maza da suka fito tace kwarai kuwa kusan duk abu daya ake ai kinsan bafilace da son zaman daji ai. Badon komai ba ya jawo hakan saboda dabbobin sune suke bin wuraren dake da sanyi don haki saboda dabbobin nasu su koshi kada suyi rama . Don shi bafilace na asali a rugga aka sanshi da zama ba a cikin gari ba amma cikin garin akwai su idan idon su ya bude zakiga sun baro daji sun dawo gari da zama to alokacin sun camfa idan ba Allah ya gyara ba mutum yakan shiga wasu halin dabana kwarai ba ga hakan. Asali dai bafilace shi a daji aka san rayuwan shi ba acikin gari ba duk da a cikin garin akwai fulani yan asali da asalin sune garine suma. A can kaduna kuma an wayi gari kwatsam kotu ta tura a kargame dukkan gidanjen su har wanda iyalan su ke rayuwa a ciki ashe. Abin bai tsaya a nan ba don duk wani kaddara na Alh nuhu dai na mahaifin mune ashe don haka kotu ta bayar da daman cewa a kwace komai daya mallaka ayi kudin su ko zasu kai adadin abin mu dake hannun shi. Zancen gidan shi yafi daga hankalin kowa a cikin ahalin namu don har ya Abubakar shima a karshe hankali a tashe ya kira yana fada muna abinda ke faruwa. Don yanzu shi kanshi sharian namu yana bashi tsoro sosai don ya gano akwai wanda ke izza wutan abin daga sama kuma maishi ya tsaya muna saidai ya kasa gano ko ta inane. Don dai Alkalin ya fada mai case din babbane sosai don an bashi umurni tundaga sama akan yayi sharia yadda ya dace idan ba haka ba a bakin aikin shine. Saidai kuma yayi mamakin jin yadda mukai mamakin faruwan hakan don sam bamu sanda wanan zance ba a lokacin mu sai a wurin shine muke ji lokacin. Ko dai waye wanan din yana da wani alakan hakan daku ko kuma dashi marigayin ke nan tunda yan jarida sun yadda zancen kowa yaji a yanzu. Ya barmu da mamakin hakan don muma munyi bincke a bagaren mu mun kasa gano ko waye mai wanan danyen aikin yanzu kuma. Gashi sai waya ke zuwa yana dawowa na yan uwa dake neman mu a layin su don wai a roka mu yarda iyalansu zauna a ciki kafin asan abinyi garesu. Saida kyat suka samu layin na na dauka mun gaisa su babbaf hamzane suke fadin haba Sahiba bai kamata kiyi hakan ba idan sunyi maki su. Idanuwa na lumshe a hankali ina rauraren baffah hamza din don abinda yake labarta min lokacin na halin tashin hankalin da kowa ke fuskanta a cikin su. Baffa ban san waye ya bada wanan umurnin ba don na tambaya a nan bangaren mu babu wani daya saka ai hakan na bashi amsa a sanyayye. Mukai sallama na fara jin digon tausayin su a kasan zuciyana don wanan yawan iyalan nasu ina zasu zauna wanan korar kai tsaye haka lokaci guda ba zato. Da sauri wani zuciya ya gargadeni da har kin manta da naku bakin cikin rayuwan da suka jefaku ciki na maraici bayan kisan gillan da sukaiwa mahaifin ku ? Ko har kin manta da irin kunci da kadaicin rayuwan da kuka kasance na tsawon shekuru masu dama ? Daga inda yake zaune da sauri yake sarrafa computer din nasa yana son gano abinda yake nema a lokacin koda zargin shi zai iya zama gaskiya . Idonshine ya sauka ga wani rubutu na shafin mutumin farine dogo saidai ya girmey masu sosai ga shekaru yana tsaye a cikin bakkaken suit da suka karfi jikin shi. Shigan shi zaka dauka dan shekara ashirin da wani abune lokacin nan ko shekara talatin da biyu yake ma,ana zai iya kaiwa sa,an ya Mustaphan gwaggo hari a wajen shekaru ke nan. Ga wasu baiti da yayi kasan photon nasa da wanda ke nuna halin kunci takaici suyan zuciya bakin ciki dayayi na rashin ubangida aminin shi a baya . Sai ya dawo kasa yana nuna cewa duk da kuncin da zuciya ke ciki a yanzu hakan ba zai hanamu tunawa da Allah ba kan amsan adduan mu na tsawon shekaru kan Allah ya baiyana muna azzaluman da sukai maka kashin gillah. Lokaci yayi da zasu fuskanci hukunci daidai da abinda suka aikata a gareka suma a yanzu sai wani photon da ya sake yana mai murmushin mugunta.
Chapter 254 · 0% Book details