← Book details Ana Dara Ga Dare Yayi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 6 OF 337

Sashe 6

Ana Dara Ga Dare Yayi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

KADUNA
Hajja Addah ta fito don jin gidan shiru da tayi babu motsin kowa daga cikin yaranta a lokacin gashi har karfe shidda da rabi na safe.
Dakin ta tura taji shi a bude suna kwance dukkan su suna barci hankalin su kwance kamar ba su ke fita karfe bakwai da rabi na safe ba zuwa school.
Hjy Addah ta tsaya cak ta rasa abin da zatace don takaici a fili ta furta wai ya zanyi da yaran nan a rayuwana ?
Wanan wani irin rashin hankaline haka ace ko sallah safe babu wace ta tashi a cikin ku tayi shi kan lokaci balle kuma har kuyi shirin makaranta.
Tana fada dasu cikin hasala sai Nabila ta dago tana fadin mommy har gari ya waye ne haka ashe shine ba,a tashe mu ba tun dazun .
Wani harara Addah ta watso mata kafin tace a hasale ai to ku jarani kullun nazo na tayar daku kada ku saba da lokacin sallah a zukatan ku ta juya zata fita daga dakin
Sai kuma ta juyo tana fadin wani albishir da zan maku shine kada ku manta yau kune zaku mana abin karyawa a gidan nan don talatu ta tafi kauyen su tun safe a can zata kwana.
Ba shiri kowan su ya mike daga yadda suka lafe da farko suna hada baki wurin fadin mene mommy talatu tayi tafiya ?
Ta juya tana fadin idan kunga dama kada ku tashi ku gaida Allah sai ku gyara kwanciyan naku ina daki in an gama abin karyawa kukaiwa hjy karima nata a part din, nikuma ku tayar dani nima in karya ta fita abinta daga dakin ba tare data kara sauraren su ba..
Ba shiri suka mike suna rige rigen shiga bandakin a lokaci guda dan gaba daya yau sun san nasu ya samesu dan sauki shima karfe takwas zasu shiga lecture kuma yau uku zasu dawo gida.
Sun halin mahaifiyar nasu kan abinda ta fada ba fashi koda hakan yana nufin zasu rasa karatun sune na ranan ba zata janye abinda ta fada aiki kan sai sunyu shi a gidan ranan.
Sunyi dabaran raba aikin a tsakanin su su ukun mai gyaran gida da mai fere dankali da wace zata dora ruwa da sauran aiyu ka har Allah ya taimaka suka hada komai.
Addah batayi barci ba koda ta fadi hakan tana zaune tanaci gaba da azzakar don neman gafara da dacewa ga ubangiji tare da neman kariya da tsari ga iyanlanta ga baki daya.
Suka shigo suna fada mata sun hada komai yana danning din ta kai kawai ta gyada masu taci gaba da abinda takeyi.
Uwa ta gari ke nan idan yaro yayi ba daidai ba a cikin hikima zaka hukuntashi gobe da kanshi zai gyara kuskuren shi kan abinda ya aikata din idan ya gane hakan.
Wayan tane yai kara ta dauka tana duban mai kiran ta da safe haka dan murmushi ta sake kafin tace modibo da safe haka.
Ta dauki wayan da sallama ya amsa mata yana a cikin shagwaban daya saba yana fadin uwata mai sona da kaunata antashi lafiya ya kuke ya gida da sauran yan uwa.
Ta dan lumshe idon tare da fadin lafiya ya aikin anyi nasara ko har yanzu da saura mami aiki ai bamu ko fara ba tukun nan dai yai mata bayani a gurguje tayi mai adduan nasara dana kariya tare da fadin ya kula da kanshi kamar kullun.

Yau tun safe babu abinda nakeyi sai shirin fita da masara da zan gasa a bakin titi duk da alaman hadarin da ake hadawa a garin sam wanan bai daga min hankali ba ko kadan.
Umma daga daki take fadin Sahiba idan masaran nan ba zai baci ba ki bari har zuwa gobe don yau kinga yadda garin ya tashi da hadadi haka.
Ga wuri ya koma tankar gari bai waye ba umma ko kin manta nan lagos ne ba ruwan su da hadari ko ruwa don wanan baya hanasu harkan gaban su.
Dole tana kallo haka diyan nata ta shirya ta fita zuwa vakin titi da kayan gasa masaranta data ara wurin iya wale data bata aron kayan da gaiya bisa rijejeniyar bata dari biyu idan ta dawo daga tallan.
Dukko da tasan ko ita riban da zata samu ba zaifi dari uku ko biyun ba ga dan masaran data saro din don gawa a bakin titi.
Don kyata da ganin iyakarsu tayi hakan don kawai ta samu hanyar da wani fitina zai hadusu ta kware masu zani a kasuwa don sunfi kowa zama matalauta a gidan hayan nasu.
Tun fitowan Sahiban taga yadda hadin yagame baka ganin komai sai duhun ruwa mai shirin tsunkewa a kowani lokaci.
Amma saukin abin haka mutane suke zirga zirgansu ba tare da andamu da yanayin da garin yake ciki ba.
Wuri ta samu a gefen titi tabi jerin masu sayar da kaya saman titin itama sai dai tana dan nisa dasu kadan don kiran kasuwa kowa a wurin kusan haka ake tsayi a wurin.
Sai da ta gama shirya komai yadda ya dace ta zauna tare da aje ledan da zata rufa idan ruwan ya gwauce ta fara hura wutan gason masaran.
Dan yayafi aka fara a hankalin a daidai lokacin data dago kai tana wani tsaye a gefe dan tako kadan ta ita yana kallon duk abinda takeyi a wurin.
Ta dago don daukan leda ta gyara koda ruwan zai zo da karfi ta rufa suka hada ido dashi daga inda yake tsaye din.
Tun data zauna din take kula dashi tsaye a wurin ci gaba tayi da abinda takeyi na gaso tana fadin azo a saya.
Ruwane mai karfin gaskene ya dauko lokaci daya hakan yasa kowa ya gyara kayan sana,ar shi a wurin hakan kuma bai hana masu son saya su tsaya ba.
Wani ne yazo kamar zai saya sai kuma ya tsaya yana son ya kawowa Sahiban iskanci a wurin ta dinga masifa dashi .
Ganin haka yasa ya dan matso daga inda yake tsaye din a cikin turancin shi dake nuna shu din ba mazauni lagos bane na gidi ya kore mutumin a wurin ta.
Jin dadin hakan yasa ta dan cewa dashi ta gode taci gaba da abinda takeyi a wurin na sayar da masara din ba tare data kara kulashi ba.
Kallon yarinyar yake daga nisa ta bashi matukar tausayi don wanan bata koyi sa,an hafsa babban yar hjy karima ba balle su Nabila da suke ciki daya davewa kannen shi dake gida.
Ya lumshe ido gami dajin tausayin tallaka yana ratsa mashi a zuciuyar shi shidai wanan yarinyar Allah na yawan hadasu da ita tun shigowan shi garin lagos din.
Muryan ta yaji tana yare a cikin yarbanci tana kallon shi kafin ta juya da turanci tana tambayan u no sebi yaruba ?
Kai kawai ya gyada mata tace o i see if no worry meka help u stay under my ledda .
Kafada ya dan daga don wanan din ma mai kama da yare da tayi sai da kyat ya iya gane me take nufi da hakan.
Haka suka dan shiga ledan kusan duk haka wasu suka samu suka dan laba ga ledojin masu talla a gefen titi din wa yanda basu son ruwa ya tabasu ke nan.
Hankalin shi naga titi yana kallon masu suce a surin ita kuma tana faman gyaran kayan ta kada su jike da ruwan saman.
But u are new here ba ta tambayeshi ya gyada mata kai kaiwa don duk a kage yake ya gaji da wanan yanayin da suke ciki gara da itama a dan tsugune take saman wani roban penti karami.
Wuta ta dan taba da hannun ta a take ta furta subbahanallah wai Allah na da sauri ya dan kallota kafin yace kin iya hausa ne dama ?
Ita fadi take lah kai bahaushe ne kaima saidai yanayin hausan nata duk da ta iya yana dan surki da harshen yare alokacin.
Mamakine ya kama shi sosai na yadda ta saje da yan garin har ba a iya bambamta ta dasu ya kara dan satan kallon yanayin yarinyar ba inda tayi kama da hausawa ko kadan.
A nata dabi,an shine idan taga bahaushe kamar taga dan uwanta najini ne a garin don haka ta dauki masara daya mai zafi ta mika masa.
Kai ya girgiza mata don bai saba da irin wanan ciye ciye din ba tace take zakaji dadin shi ya karba dole yana fadin nagode.
Ba damuwa taci gaba da abinda takeyi fuskanta a dan sake ke yar inace ya tambaye ta ba tare daya sake kallon ta ba.
Ni nidai hausace amma ban san sunan garin mu ba amma umman mu tace garin mu arewa ne .
Arewa wani gari ke nan a cikin arewan tace ban sani ba tana dan jera masaran data samu ta gasa a lokacin .
Mamakine ya kamashi shi ya sake jefo mata tambaya mahaifin ku fa take fuskanta ya sake a lokaci guda har saida gaban shi ta fadi.
A zuciyar shi yace ko dai irin shegun yayan nan da ake shigowa bariki a haifane su tashi a garin lagos din a wahalce karshe su zama yan daba masu batawa arewa suna.
Don yanayin ta da yaga ya canza da tambayan da yayi mata din sai can ta bude baki tace umman mu tace tun kafin a haifi Amar kanina mahaifin mu ya rasu iya abinda ta fada min ke nan kawai.
Allah ya jikan shi yace ya mayar da kanshi gun masu wucewa harkan gaban su yana kuma kula da yanayin su don abinda yazo nema wurin.
Meye sunan garin ku ta jefo mashi tambayan sunan garin mu kaduna kin taba jin kaduna ko tace kwarai kuwa a cikin history ko ba a stete din queen Amina take ba ?
Tambayan yaso ya bashi dariya don yadda ta fada din sai a lokacin ya kara kallonta ya fahinci iya shekarun ta.
Wata rana zaki kai ziyara ke nan tace umman mu tace akwai nisa sosai a nan kaga kuwa bazanje ba tunda kudin motan shi ba da yawa da naje naga garin da tayi mulki da ake fada.

ZAINAB IDRIS MAKAWA

ANA DARA GA, , , , , , , ,
Chapter 6 · 0% Book details