Sashe 45
Ana Dara Ga Dare Yayi Part 1 Complete Hausa Novel · about 2 min read
ya zaba a yanzu don yaga yafi ci a wanan zamani Don haka ya fada harkan motoci da kaya masu muhinmanci da gwaunati ta hana a shigo dasu a cikin kasa saidai saukin abin shi baya yarda yayi abinda zai zubar da kimar mahaifin shi ko kadan. A wani vangaren kuma yana harkan zinare duk ta barauniyar hanya abinda ya kara bunkasa karfi shi da kudin shi ke nan a yanzu. Wanan yasa shi saurin fice a cikin abokan harkan nasa a yanzu sunan shi ya daga ko wanan haduwan akan wani sabon ma,aikacin da aka turo yabi didigin su a nan gida Nigeria. Alh baba yaci gaba da bayani shi kamar haka bayan yayi sallama yace kowa nan yasan abinda ya taramu a wanan wurin a yanzu. Wanan matsalan babban abune da zai iya kawo muna cikas a yanzu cikin harkan nan namu don a wanan karon idan badon dollers boy ba da yanzu kayan mu na wanan shekaran sun zama tarihi a rayuwan mu wanda hakan zai iya kawo koma bayan da yawan mu a wurin nan. Kai suka shiga gyadawa tare da yan kuskus a tsakanin su kowa na fadin albarkacin bakin sa kan irin fargaban da suke ciki a da kan kayan su din. Alh baba yaci gaba da jawabin shi yana fadin mun san cewa akwai aiki ja a gaban mu yanzu kan irin matakan tsoron da aka daukan muna ga wanan harkan. Na turo wakile daga cikin mu su gana da shugabanin wanan jami,an tsaron abin ya kiya don shugaban su wani karamin yarone ke jagorantan su. Don kwata kwata yaki yarda da tayin da mukai masa na goro asalima sai kokarin bincken da yakeyi a kanmu yanzu haka. Don yayi ikirarin duk wanda ya fada a hannun sako kayan sa ba zaiji dadi a wurin sa ba kun san yaro a yanzu shike da kafi da naci akan aikin shi don haka wanan yaron ya zama dole mu san abinyi dashi don musan yadda zamu zauna dashi don harkokin mu su tafi daidai yadda suka saba. Kowa yayi shiru a wurin yana nazari a cikin zuciyar shi na hanyar da zasu bullo ma wanan matsalan da yanzu ya kunno masu kai.