← Book details Ana Dara Ga Dare Yayi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 134 OF 337

Sashe 134

Ana Dara Ga Dare Yayi Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

barshi wa yan nan kan yare ne aida gani dangi shine na oduduwa basa jin hausa. To shiga dai dasu ciki kafin ya shigo tsohuwan ta fada sai akace mu shigo ciki da harshen turanci muka shiga jikan na tsaya na kowane takalma daga kofa ban yarda na zauna ba saidai na gaida ita a cikin ladabi tana amsa min da yarbanci. Mallam kodai sha,aban ya kawo maki kishiyane ki gani dama ai daya kyauta irin wanan yar haka mai zubi irin nasa ai sai su dinga haifo maku zabaya. Duk suna dauka bama jin hausa ne ganin da nayi lokacin sallah na shigewa yasa nace dasu mama don Allah zanyi alwala nayi sallah. Lah ashe yarnan tana jin hausa ke nan kika barmu muna zuba haka a gaban ku zo muje na kaiki ta fada tana mikewa duk suka bimu da kallo. Na kwabe gyalena na nufi inda tabi ta nuna min ban dakin nayi alwala na fito daidai lokacin ya shigo falon ya kaure da hayaniya dashi jakkana na bude na fito da hijab dina har kasa na koma can gefe zan tayar da sallah. Da sauri suke salati suna cewa don Allah zo ga daki nan ku shiga kiyi sallah mana kyayi sallah a nan kuma yar nan na bita zuwa ciki dakin ban kara fitowa ba shida kanshi ya turo yemisi ciki ta sameni na idar ina nuke kayan sallah. Dakine mai kyau da komai na jin dadin rayuwan dan adam a cikin sa ga shimfida na alfarma anyiwa gadon dakin sai kamshi ke tashi tako ina a cikin dakin har falon nasu. Babban falone da zai iya cin baki ko mutum nawane kwa yaji saitin kujeru na alfarma irin na kasan waje din nan da kashi katon photunan sune iyalan gidan tsaye an aje a jikin bango kamar wa yanda ke ciki zasu fito suyi magana. Dan zaman da nayi a falon ne na kurawa photon wata mace ido da mijin ta dake cikin kaya saki irin na masu kudin yarbawa din nan nada can shekarun da suka wuce baya har wanan lokacin ma wasu na sakashi . Babu tamtama sune iyayyen ogan mu da Felix ya ban labarin su ranan ban kai karshen tunane na ba naji sallaman matar ta shigo ga wata biye a bayan ta da katon tire dauke da abinci cikin sa tana fadin yata ga abinci ku tashi kuci kinji kada barci ya dauke ku. Mun gode mama na fada ina mikewa zaune abincine mai rai da lafiya aka shirya muna munci mun sha kafin mu kwanta barci . Duk da banda sabo amma na dan sake da matar da naji kowa na gidan na kira da hjy Laraba na dan sake jiki da ita muka dan taba hiran abinda ya faru a kaduna din damu. Yemisi na kwance tayi waya tayi charting don na kula fushi take dani tun abinda ya faru tsakanin mu da safe nima na shareta. Bayan hjy ta fitane na shiga ban daki na watsa ruwa dana fito nayi duk wani shirin barcina tare da addua na haye gado na kunna kira,a na barta zaune ta mike kafa saman gado tana zuba yare. Washegari koda akazo tayar dani sun samu har na idar da sallah ina zaune ina addua ta juya tana fadi au ashe kin tashi ma. Bayan na idar wanka nayi na shirya don nasan tafiyan safe zamuyi don haka ina idar sallah nayi wanka na shirya na koma bakin gado na zauna. Ina turawa Ammar sako a waya a lokacin yemisi ta falka daga barci ta dan kalleni taja tsuki tana gyara kwanciya. Shidda da tabi nayi sai ga kira a wayana cewa mu shirya gasu nan zuwa su dauke mu zamu wuce airport ke nan a lokacin tana jin haka ta wani zabura ta sauko daga gadon ni kan jakkana na dauka na nufi falin gidan a nan na samu hjy din tsohuwar gidan zaune tana ba yan aiki umurni don su samu suyi muna abin karyawa kafin mu tafi. Gaba dayan su sukai sallama suka shigo gidan ana karbawa suka zube a gabab tsohuwan suna kwasan gaisuwa a wurin ta yana shigowa ya dubeni a inda nake zaune yana fadin ina yemisi din mu tafi mana. Mikewa bayi aiko ya dinga fada sosai kan ba zasu kara tafiya da ita ba daga ranan don baiga amfanin zuwa da ita bama. Badai tafiyan ke nan ba ya kalli agogo yana fadin hjy zamu makara a cikin hausa jirgi bakwai daidai zai tashi kinga in mun tsaya zamu makara mikewa tayi tana fadin haka ba zai yuyu ba ka kawo min kawata har gida kace ta tafi haka bata karya ba kuma. Kitchen din ta nufa can sai gasu tare da mama Laraba da ledojin take away a hannun su suka mika ma kowa nasa nawa kan ko ba a ce ba yafi na kowa yawa a ciki muka karba muna godiya tana fadin kwa karya a jirgin ai. Ta miko min wani warmer sabo yana kyali tana fafin karbi wanan ki rikawa ogan nasa kinji wanan in kunbi nasa baya cin abinci. Mukai masu sallama muka fito a gurguje yana can dan nesa kadan da tsohuwar suna magana mama Laraba kamar yadda ya kira ta tasamesu a wurin har mun shiga mota mun zauna ta dangwara min wani leda a jikina na dago kai a cikin damuwa na kara mata godiya. Mun samu jirgi da kyat da fudun tsiya da sukayi ba ai wani tsayawa ba jirgin namu ya tashi zuwa lagos . Allah ya taimakeni a can baya na samu seat na zauna na sake saidai har lokacin ban wani sake jiki ko in duba abinda ke cikin leda ba. Allah ya sauke mu lafiya mun sauka mu mata suka fara saukewa gidajen mu nice ta farko yaran Abdulhamid da Amar dake kwallo a waje suka sheko suka tareni. Naji mamakin ganin ana sauke buhun dankalin turawa da doya wani na kulan dana bari nasa a mota da nake kaya sai ga yara nagani dashi sin shigo sun bayar akawo min. Bayan yaran sun fitane muka zube a falo da umma da Amar ina basu labarin tafiya da abinda ya faru har hira da yemisi duk saida naba umma labarin komai. Amar ne ya jawo kulan yana tambayana meke cikin sa nake fada masu yadda akayi har kulan yazo gareni lokacin kuma muka bude babu komai a cikin sa sai sayayyen kaji da dan irish da manyan suyan kwai a cikin sa kajin daine masu yawa sosai saida kulan yacika duk girmansa kuwa. Mikewa nayi zuwa dakina daga nan ban fito ba na kwanta sai barci barci sosai nayi a ranan ban tashi ba sai bayan karfe uku da kwata na falka ma dubi lokaci. Aida sauri na mike zuwa bandaki na dauro alwala na fito sallah nayi kafin in fara jin wani irin yunwa na ziyarana lokacin. Falon na fito wanan abinci na sama din da alama basu girka komai naciba da rana don haka shina dauka nayi warming din shi naci nima. Bayan ya gama sauraren mahaifiyar shine yaji tayi shiru ya kwantar da murya yana fadin naji hjy zan tafi amma ki sani wallahi idan naje suka zageki ko daddy aurena da Nazifa ya mutu ke nan har abada. Da sauri hjy ta dago kai ta kalleshi yace kwarai mommy don haka tunda dai ba fada mukayi ba indai har tana sona har yanzu ku bari ta dawo dakinta da kanta yafi. Mommy tasan kwanan wasan don dai sai sun nemi suja masa rai zasu iya zagan masa mahaifan sa a gaban shi tundai yayan nata dayafi kowa hawa a lokacin. Budan bakin mommy din sai cewa tayi idan dai hakane kada kaje a bata goma daya bai gyaru ba abinda kawai zakace dasu ke nan. Ta dawo dakin ta tunda ba fada kukayi ba shike nan don dai nasan sai yaya yayi masifan hakan don kai yake son gani yacima mutunci son ransa. Da nayi masa me mommy dako ya raina kanshi ranan wallahi yara kuma idan zasu rike sune su rike din nasan dai idan muna raye sai sun nemeni. Shiru mommy tayi tana nazarin maganan su da fan nata shima dai hakan ne don mikewa yayi yana mata sallama ya fita ranshi a bace a nan waje ya samu sauran mutanen gidan a zaune inda ya barsu din Fa,iza tayi tagumi tana tunane. Amirace tana ganin shi ta mike tsaye tana fadin kakaini wurun ta yaya sai yarinyar ta bashi tausayi ya dan kakaro murmushi yana fadin zan kaiki ai Amira yanzu akwai inda zani daga nan ne. Sahiba din tana garin nan kenan yaya Fa,iza ta sake tambayan shi a karo na barkatai yaji tausayin yaran sosai saidai bai yarda ya nuna masu komai a fuskan shi ba sai murmush kawai da ya sake masu ya juya ya nufi motan shi ya shiga ya bar gidan.
Chapter 134 · 0% Book details