Sashe 130
Ana Dara Ga Dare Yayi Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
wurin ta kasa komai don tunanen daya dameta kan auren dan nata daya dauko sabon sallo na son mulkan shi kota halin kaka shi kuma yaki yarda da hakan. Ya isa gida wankan yayi kamar yadda ya fada ya fitone ya dauki wayan shi ya fara aiki a cikin sa yana neman wani labarin da yake so a cikine yaga taron manyan yan kasuwan da za ayi a garin kaduna din ranan Laraba mai zuwan nan. Murmushi ya sake yasan zai samu dan haske ga abinda yake son samu da dadewa a wurin don haka ya hake wanan ranan yana murmushi. Tun a daren ya bugawa duk wanda yake bukatan aikin nan dasu ya sanar dasu shirin shi da zai aiwatar a wurin. Washegari shiru shiru mommy bata ji motsin shi ya shigo gidan ba har yamma ga wayoyin shi baya shiga a lokacin suna rufe. Hankalin mommy ya daga take zaton ko yaje gidan yayan nata ne kamar yadda ta umurce shi wani abu ya faru dashi a can don tsoron ta Allah yanzy tsoronta yayan nata . Tunda ya iya furta cewa a gaban ta yake fadin Aliyu kai ba komai bane kuma ba kowa ba kawar dakai da dan naka ba wani jan aiki bane a wurina. Cikin karfin hali shima mijin nata ya mayar maida amsa yana fadin Nuhu kayi sherin ka ka barni don ta Allah ba taka ba duk kace zaka tabani ko ahalina wallahi karyan ka ya kare a garin nan ke nan. Wanan hasumin mommy ta rike a zuciyar ta duk da manya sun shiga zancem sun sulhunta su an raba irin wanan fadan sunce sun bari. Saidai sanin halin yayan nata da tayi yasa tasan zancen bai fita zuciyar yayan nata ba duk ya ce ya sake komai ya wuce tasan yana rike dasu rikicin duniya da mairai akeyin sa. Ga dan uwan haihuwan shi Alh gyade ya nakasa yanzu baida wani moriya daga tsaye sai zaune bai iya komai anje asibiti da gurin yan tsubbo abu ya gagara tun lokacin har yanzu kuma ba a fasa ba don har kasan an bari dashi ba a dace ba. Hankalin hjy bai kwanta ba sai lokacin da suka samu wayan shi ya shiga ya sheda masu cewa shi yana Abuja a lokacin. Amma ka daina halin nan modibbo duk kabi ka dagawa mutane hankali har mahaifin ku na kira na sheda mashi bamu jika ba tun jiya. Haba mommy sai kace karamin yaro tace umm, umm bari wanan lokacin da ba a dauki rayuwa a bakin koma ba ba yaro ba babba a wurin yaudara. Yana dariya ya kashe wayan shi yana fadin a zuciyar shi ba inda zani mommy sai sun gane basu da wayau idan ma zai karbi yarsa ne ya karba wallahi. Fita yayi zuwa wani unguwa a can samarin gidan su Nazifa suka ganshi har gaisawa sunyi dashi yayi masu alheri sukai godiya suna jin dadi. Suka dawo gida suna murna suna da alherin da yayi masu din suna fada suna kari a cikin murna da farin ciki mamakine ya kamasu yan gidan abinka da gidan yawa take zancen yakai kunnen Nazifa. Aiko har wajen Alh Nuhu yaji kamar ya hade ranshi a lokacin don takaici da bakin ciki yana fadin watau yaron nan ni zai nunawa shi dan iska yake ko ? Shima kuma din yayi hakane don ya tura masu sako ta yayan shi su san su suka dauku Nazifan a bakin wata tsiya yayi alkawarin ba zai tafi ba sai ita data bar gidan don kanta ta gaji ta dawo. Nikan zance shawaran umma yayi min rana sosai don naga fa,idan shawaran a yanzu tunda na fara aiki dasu wanan ne karo na biyu da zamu bar lagos zuwa wani gari na farko muje abuja dasu mun dawo a ranan. Ga wanan katon kuma kaduna zamu tafi meeting mu dawo duk da bani kadai bace mace yanzu dake cikin su akwai Yemisi da ta dawo daga kasan waje tana jin kanta mu shidda ke nan ke tafiya yanzu wuri muna take mai baya kowa da aikin sa kuma. Sai shawaran umma din yai min dadi a lokacin don shiga ta alfarma shine ya dace da wanan shigan munyi da safe karfe bakwai zasu daukeni mu tafi. Sai ga zance ya canza aida karfe hudu zamuyi tafiyan ke nan wanan katon kwana zamuyi a can yaya zan tari umma da wanan zancen ta kwana tare da maza haka. Abdulhamid na sama a gidan shi bayan ya dawo aiki na fada mai abindake faruwa shima din saidai yayi tunanen abinda zai fadawa umma din kafin ni kuma yayi min nasiha da kama kai da mutuncina duk da yasan ba halina bane yin hakan. Saidai baisha wani wahala wurin fadawa umma din ba sai cewa da tayi ta kama kanta da mutuncin ta nasan halin sahiba amma duk da hakan ta tsare mutuncin ta dai a can don kaduna gidane gareta. Data shigo kuma take fada min yadda sukayi da Abdulhamid din ta min nasiha tare da cewa na leka gidan daddy koma na kwana a can din ba komai bane din sun watsar damu hakan mu sai mu bisu ai yan uwan mune su. Allah ya rufa min asiri karfe uku sai ga felix gidan yazo wurin umma yake fada mata don lokacin da suka kirani suna fada min nace ba zan tafi ba ni shine ya fadawa ogan shi kuma ya turo shi wurin umma din akan ya roketa zamu tafi aiki kaduna mu dawo gobe. Shima din rokon shi umma tayi akan akula mata dani don Allah kuma akwai yan uwa a can don mu din daga kaduna din muke ai. Karfe uku da rabi muka bargida zuwa airport don jirgin hudu zamu bi ba bata lokaci kuma jirgi ya daga sai kaduna garin gwauna damu. A wani katafaren hotel muka sauka kowa da dakin shi karfe takwas zasu fara taron nasu ke nan na dare don haka muna da sauran lokaci ke nan sallah nayi na zauna zaman lazumi. Kafin na mike na shiga nayi wanka a bayin na fito sallah na tayar na fara shirin barin hotel din shiga nayi sosai na alfarma da daya daga cikin rugunan dana sayo din baka mai duwatsu farin ado a jikin shi na zauna gaban mirrow din na daura dan kwali baka ganin komai sai zagayen fuskana sai turaren muzawa mai kwanci daya bi jikina yana tashi a gankali takalma mai hill ne a kafana sai jakka dana dauka shigen kayan jikin nawa kafin na dauko jakkar laptop dina daga baya. Ni kaina nasan ban taba shiga irin wanan din ba haka zaka rantse da Allah ni din wata balabiyace a lokacin Felix ne ya kwankwasa min kofa a lokacin na bude yake fadin suna jirana a waje fa nasan oga baison latti. Ashema har yemisi na cikin gidan lokacin tare muka jera mu ukun dukkan mu a cikin bakaken kaya . Mun samesu a cikin mota sai satan kallon motan nakeyi don kyau ya nuna min inda zan shiga na nufi gaban motan zan bude da sauri wani yace min baya dai na bude bayan na shiga. Budewa nayi ina mamakin sauyin ranan na shiga na dauka yemisi ma nan zata shiga naga ta nufi wani motan daban ta shiga. Ina shiga ogan mune a ciki a cikin rikicewa na gaidashi ya amsa min ciki ciki a takure na zauna muka fara hanya motan yana shiru saishi dake aiki a cikin computer din shi yace na bude nawa yana miko min wani abu . Ganin ba zan iya ba yace dani na miko mai photon mune mu da umma da mukayi ranan sallah na saka a screen din computer din . Saitin ta yayi min tare da dan fada min abinda zanyi ya miko min tafiya mai dan nisa sai gamu haraban wajen taron tun daga nisa zaka ga irin haske da yawan motocin dake wajen. Daga can dan nisa kadan muka samu wurin parking din motocin mu bamu fito ba sai da wasu security sukazo aurin aka bada umurnin fita. A ciki kuma kallo yake don matasan masu kudin zamani ne birjit a wurin sai tsofi da dattawa da kososhin gwaunati masu fada aji a cikin kasa. Wow ga sha,aban nan ya shigo da nasa tawagan wanan taro yayi albarka sosai da amsa gaiyatan matasan mu dake tasowa da kulada jin dadin kasa. Idanuwa sukayo kan mu caaaa yana dan daga masu hannu irin na sallama ga yan uwa har muka isa inda akai muna mazaunin mu a wurin. Daga can baya inda suke zaune da zasu iya ganin masu shigowa yake kallon fuskokin mu daya bayan daya sai dai ya tsayar da kallon shi ne a kaina zuciyar shi na bashi karya a lokacin.