Sashe 285
Ana Dara Ga Dare Yayi Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read
Zan tafi naba umma amsa a takaice tace tagode amma kada ki dade ki fito tunda ta shirya tace ta sake fadin in kula da kaina don Allah. Haka na tashi na shirya raina a bace don dai babbace zan raka din haka kuma umma din da tayi min tsaye sai in tafi yasa na shirya don dole na fita . Har nakai kofa ina jin wanan din dai da suke kira da sister ita matar auren kenan tana fadin Amarya ke nan a dawo lafiya ban kawo komai a raina ba na dauka don katon hijjabin dana saka take min sherin hakan. Dakin su umma na fara zuwa muna cikin magana aka turo kofan wanan budurwan yar wancan tawagance ta shigo tana fadin waini suke jira gasu a waje. Tare muka fita da Rukkaiya din zuwa dakin su sai gasu su fito shine a gaba uwar tana baya tana gyara mayafin jikin ta a cikin hausan da bai zauna mata ba take fadin au ga yar tawa ta fitoma ashe yanzun muke niyar bin bayan ki. Kafin ta rufe baki nakai kasa irun gaisuwan mu na yarbawa na bar girma gaba dayan naje kasa ina gaida ita da sauri ta dagoni tana fadin kai kai haba dai ke yatace fa yanzun mun kara zama daya sosai daku ki daina hakan kinji. Yi nayi kamar ban ganshi a wurin ba muka jera muka fita na dauka da Rukkaiya din zamu fita dukan mu ashe dagani sai sune kawai fitan. Wani motane lafiyayye a waje muka sama ita muka shiga shida driver suna gaba muna baya da tsohuwar sai yaren su sukeyi da banji aikina kawai bin garin da kallo yadda aka tsarashi. Wani katafaren ajen sayar da gwala gwalai mukaje motan ya tsaya muka fifito muna kallo wajen amma shi baiko damu da kallon da mukeyi ba din. Yake fadin bissimillah hjy mu shiga ko zamu shiga din ta juye mai da yare ya dan juyo ya kalleni yana min guntun murmushi. Nan muka shiga wajen har kasa a kwai gina na shagunan gwalagwalan gasunan kowa na kira kazo ka saya sai binshi mukeyi zuwa wani babban waje. Bayan an bamu wajen zamane mun zauna suka shiga kawo irin kayan da suke dashi a wajen muna dubawa da kudin su . Wanine ya dauke min hankali na rike na dan juyashi har bayan shi zubin shi yaimin kyau sosai ga gani da nice zan saya wanan din zan zaba saidai ban san ra,ayin maishi ba. Ban kuma san wace zasu saiwa ba a lokacin muryan shi naji yana tambayana da wanan dai yana da kyau ke nan ko naga kin rikeshi. Kamar ba zan bashi amsa ba sai can nace eh yana da kyau sosai design din yayi min baida girma ko nauyi saidai kudin shi yayi yawa sosai nake gani. Idan yana da kyau kawai a dauka ya fada ba tare da damuwa ba sai kuma yakai hannun shi ga wani shima dai zubin shi gaskiya kamar yafi wanda na zaba din yace wanan fa ? Sai lokacin zaice yaga murmushina kadan har diple dina yana dan lutsawa nace kamar yaso yafi wanan din ma kyau din ban gashi ba sai yanzu duk a harshen turanci dole muke magana. Ai is ok uwar ta fada shida kanshi ya zabo wasu awarwaro ya hada da kayan sai mamaki su nakeyi a raina don nasan uban kudi suka tara a wana wuri lokacin. Bayan yan canza magana kawai naga ya tura masu kudin su a take muka fito zuwa lokacin ashe har yamma yayi ke nan na fada a raina ba zamu samu zuwa sallah ba a haram ke nan. Wanda banso hakan ya kasance dani ba a lokacin muka dauki hanya a zatona masalaci zamu ko gida sai gamu wani wajen kuma nan kan sayayya sukayi sosai ina mamakin tana da wasu yara ne dai haka ashe bayan su sai gab da sallah magariba muka nufi masalaci a can muka hade da yan uwa. Bayan mun dawo ne faiza taso bugun cikina da ina kayan da muka sayo nace suna wajen masushi a can na barsu dashi. Washe gari kan da dawowab mu sallah aka daura tafiya zuwa makka na dauka tafiyan wasa ne ashe tafiyace mai nisa a tsakani dukda motocin lafiyayyune amma sai wani tsawon lokaci muka isa birnin makka din kusan tafiyan yini guda a hanya. Duk na Annabi ya roka Allah ya karawa Annabi daraja dashi da sahabban sa da mu duka musulmi na duniya amin don tafiya mai nisa mu gamu a mota munga nisan tafiyan ballesu da a kafa sukai wanan tafiyan saman dabbobin su. Ranan muka isa masalacin makka mukai dawafi dukko da tarin gajiyan da muka dauko din kamar yadda sunna ta koyar ayi.