Sashe 103
Ana Dara Ga Dare Yayi Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read
ma dai basu kasa damu ba gaskiya don akwai komai a cikin kitchen din da zamu nema ga store din shi nan shake da abincin da zamuci. Fridge da freeze na a ciki don haka na bude ai kira na kwalawa umma tazo tagani itama bata tsaya ba jin kirana sai gata ta fito da sauri daga dakin. Ta sameni a kitchen din na nuna mata hawaye ke zuba daga idon umma din wanda ba zance ga dalilin shi ba a lokacin. Takawa nayi zuwa wurin gas din dana gani ina son in dafa muna koda indomei ne muci mu kwanta a lokacin. Sai kuma na bude warmer din abincin dana gani abuncine ciki maizafi har yana tururi a lokacin na juyo na dan kalli umma din itama ni take kallo. Abincine fa umma tace nima shina gani ai aikin modibbo ne nasani yasa a kawo kafin mu iso nan kila. Shina fito dashi falon muka zauna mukaci kukan waya nake ji da sauri muka dago kai muna kallon juna da umma. Wayace ke kuka a gidan haka yasa na mike da sauri ina bin kukan wayan inda yake fitowa a dakin umma har Allah ya taimakeni naga wayan a karkashin filo tare da kwalin shi a gefe daya. Na dauka don na iya a wayan su Fa,iza daya zama kamar wayana a lokacin don nike faman jagulan shi sai idan an kirata zan kai mata. Na dauko wayan nazowa umma dashi ina fadin wallahi umma wayace sabuwa har da kwalin ta a cikin dakin ki wurin pillow. Wani kiran ne ya sake shigowa na daga da bissimillah gami da sallama abakina aka karba min. Muryan mommy ne don bazai bace min ba tana fadin Sahiba kun sauka lafiya ? Ban iya karba mata ba sai kukan dana sake kawai a lokacin ina mikawa umma wayan ta karba tana fadin menene waye kuma ? Muryan mommy taji tana fadin nice mairo ya kuka sauka ya jama, a da yaran ta amsa da lafiya mun barku lafiya dai ? Ta amsa da Alhamdullahi kafin tace kun tafi kun barmu da kewan ku har yanzu sai umma ta danyi dariya tana fadin . Gasu zaune sun kasa sake jiki tun zuwan mu na kasa gane masu balle yartaki ai gaba daya a hankali tashe take a gidan nan. Dada hjy sai kuma mukazo muka samu dawainiyan dayafi wancan da muka baro a nan kuma. Layin ne ya katse mukai kira baya shiga a lokacin dole muka kyale haka muka bar zancen neman layin na mommy din. Mikewa nayi na duba kofan a rufeyake tunda zamu shiga sallah dama na rufe kofan don ina jin lokacin da yake fadin mu saba da rufe kofan kada a barshi a bude. Lokacin da muka shiga dakin ne na bude troler kayana dana shigo dashi in dauki kayan barcina bayan na ciro na saka wando da riga na saka hula a kaina. Sai naji in bude wardrobe din in ga girman shi ko jakkar kayana zai iya shiga ciki umma na fadin daki kai kayanki wanan can dakin dayace shine naki don zaifi kunga nan sai ku barmin ni kadai. Maganan ce ta makalewa umma don kayan dake cikin wardrobe din da aka jera a cikin shi. Nan kuma hankalin mu ya dauku ga kallon kayan fita nayi zuwa dakin na duba haka din ne kayan ane a ciki shima na fito kamar mahaukaciya naje dakin Amar shima hakane dai na sama a cikin nasa. Dole muka dawo fslon muna jin wanan karamcin nasu a garemu dare har Amar ya fara barci muka shiga zuwa cikin dakin muka kwanta. Washegari kan kusan makara ne don banyi barci da wuri ba saboda tunane yan uwa da kawaye da abokan arxiki da muka baro a kaduna. Bayan nayi sallah ban kwanta ba duk da gidan baida datti amma saida na gyara ko ina na cikin gidan tsab na koma dakin nan da yake a matsayin nawa nayi wanka na fito. Wardrobe na bude na tsura mai ido na dan lokaci kayan an bambamtasu a mazaunin su shiryawa nayi cikin wani simple material dogon riga na fito abincin danayi muna na breakfast na fito dashi falon. Na tayar da umma data dan samu barci a lokacin don saboda bata barci sai wajajen tara na safe zuwa goma sha dayan rana. Mun ci munsha Amar daya damu sai a kunna tv na kunnawa tv din yake kallo nikuma na koma saman kujera na kwanta don umma tace kada ayi abinci sai na dare tunda na safen ya rage da muka dafa bamu cinyewa duk da ba yawa wanda nayi din amma mun kasa cinyewa duka. Barci ne ya daukeni a wurin kuma na samu nayi barcin sosai harda mafalkina na yan uwa dana bari a can da sauran mafarku dai na dinga yi. Sallah azahar ne ya tayar dani lokacin bayan nayi sallah dinne muka zauna da Amar can umma ta fito ban san ya akayi nayiwa umma tambaya ba da fadin. Wai umma kafin Abban mu ya rasu shi mai kudine sosai irin daddy ko dai shima wanan filin da suke magana yake dashi kawai dama ? Sahiba ta fada a cikin mamaki yaushe kika koma haka ko zama arewa ya koya maki wasu akida na shiga cikin maganan manya ne ? I am sorry umma ban tambaya da wani nufi ba haka kawai tambayan yazo min a raina na bata amsa ta kawar da kai ga kallona. Nima din jinin jikinane nasha a lokacin don ban dauka maganan zai taba zuciyat umma haka ba mun dade a wurin zaune ba wanda ya sake wani magana a cikin mu kuma. Zama wasa wasa ya kama mu a unguwar har yakai na fita na zagaya unguwar nagani har iyaka duk yanzu nasan na wuce level din talla da nayi ada can baya a lagos din. Saidai kasuwancin bai fita raina ba son haka na kawowa umma sharawa akan mu dan fara sana,an drinks a dayan shagon mu huta zaman gida da mukeyi din. Da farko umma bata yarda da shawarana ba wai sai modibbo yazo ta tambaye shi idan yin hakan ba zai zama laifi ba garemu. Gashi shi kuma baizo din ba bai kira kuma wayan mu ba duk shidin ya aje muna waya a gidan don amfanin mu amma kuma sai gashi bai taba kiran mu ba har lokacin nan. Ranan na taso daga barci na dawo falo ina zaune na umma ta fito tana fadin ni sana,an zamu fara ne mu dan rika fita waje ko banza mu fahinci yan unguwan nan da muke cikin sa idan muna fita. Nadago ina fadin umma kardai tunena ya zama gaskiya mutanen nan hanyan rabuwa damu suka nema kada mu caza masu fitina a kansu suma. Eh to nima ina tunanem hakan wani lokacin jin har modibbon shiru yanzu bai kara waiwayo mu a nan ba. Koma sun guje mu sun muna gata a yanzu ai umma tunda sun muna sanadin sanin gida da yan uwan mu. Ga wanan gidan da yanzu muke zaune a cikin sa duk da bamu san matsayin mu ba cikin gidan nan shin hanya aka daukan muna ko zaman su yakeyi muke zaune a ciki ? Ban tsanmani a matsayin haya muke ciki duba ga abundaya fada ranan daya kawo mu gidan nan kawai mu zubawa sarautan Allah ido yanzu muga makomar mu nan gaba. Sai kuma naga umma din tayi shiru ta shiga tunane nake fadin umma don in kawar da tunanen data fada yi din nace umma akwai kudin da zamu fara wanan sana,an ne a yanzu. Akwai kudi mana a hannuna ko kin manta da kudaden dake ajiye a wurina tunda dadewa ne suna nan banyi komai da suba har yanzu. Jin hakan hankalina ya kara kwantawa tashi umma tayi ta dauko kudin muka zauna muka kidaya ko wani umma ta dauresu daban ta ajiye su a wuri daya.