← Book details Ana Dara Ga Dare Yayi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 336 OF 337

Sashe 336

Ana Dara Ga Dare Yayi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

fada. Nayi hakan ne a gaban shi don kada yasan kalar kishina don ba karamin tausan zuciyana nayi ba a lokacin har na nuna ba komai a zuciyana game da wanan haukan nata da tazo tayi muna a gida. Saidai nasha alwashin cewa zanyi kokari nayi ta daurewa ina nuna sanyi a zuciyana kamar yadda matan yarbawa suke taushe zukakatan su akan kishin mijinsu wanda kai bare ba zaka taba gane hakan ba garesu. Saidai zan manna mata karamin hauka a kaina ta yadda zan sace zuciyar mijin na rike a hannuna na juyashi yadda bata son ganin shi da ko wace mace a duniyar nan. Tayaya zanyi hakan ba wani abu bane me wuya tunda kowa yasanshi zanyi kokari na yaki zuciyana bazan yarda na taba zancen abinda ya shafi hjy falmata ba a gaban shi. Haka koda wasa ba zan taba nuna gazawa da yan uwanshi ba ko wani mutum da wata halaka ya hadashi dashi har na sanshi koda kuwa masu aikinmune irin maigadi da mai waki ko cookers da sauran su zuwa abokan hurda da yake girma da arziki dasu. Fanin gyaran jikina koda yaushe na koma kamar yarinya wanan ya zama wajibi a gareni ko yaushe jikina gidana ya kasance min a gyare. Haka kyautatawa a tsakanin mu ba gazawa ko kissa balle cutarwa tunda ni bai cutar dani ba ya zama dole nafishi son diyanshi da duk wani nasa a yanzu idan na dan kwatanta haka ina ganin na wadatar da yadda nake so. Sun gwaggo satin su biyu a can suka dawo gida inda suka barni tare da ummana da dan uwana Ammar wanan shine sillar dawowan ummana a tare dani. Hakan ya batawa yan uwan mu na kaduna rai sosai da suka fahinci cewa umma ba zata dawo Nigeria ba kuma ta zauna a nan din. Don wai da har ana shirin cikin baffah Abdullahi ko baffah hamza daya ya nemi umma ya aureta sai gashi na dauke uwata na tafi da abata can inda mukai masu nisa. Haka bai hanani yo masu aike ba lokaci lokaci sanan kuma zan bisu daga daga na aiko masu da sako mai ingaci a garesu wanda hakan ya jawo min farin jini da kauna garesu. Zuwan mu na farko Nigeria mun zone lokacin da Fatima da Ammar suka samu hutu a makarantarsu a lokacin har yarana sun iya tafiya don suna da shekara uku da haihuwa a duniya. Don haka ba wanda yasan yanayin su koda mukazo din dasu lokacin sallahne don haka a Maiduguri muka fara sauka . Mun samu an gyara muna gidan mu sosai ba kamar yadda muka barshi ba a baya can yanzun an kara gyarashi yayi kyau sosai ga ganin mutum. Hjy Falmata tazo a wanan shekaran don bukin sallah din duk da ita tana zuwa duk shekara nima don kawai ga irin yadda muke da yan uwanane yasa bandamu da zuwa ba na share kowa na zauna can tunda ga mahaifiyata a kusa dani yanzu. Hjyn su mukhutar ta kara dan tsufa amma da yake akwai kulawa ba zaka gane hakan ba gareta sosai tare sukazo da uwargida falmata daga Paris don haka sun rigamu shigowa Nigeria su don mu sai washegari muka iso . Amma bai zo gidan namu ba sai safiyan sallah ya kama ranan jumma,a za,a hau idi a Nigeria, ba wani aiki a gidana don sister tace kada muyi komai zasu kawo muna daga gidan hjyn su idan an girka a can. Da safe ina daki kwance ya shigo kafin aje mosque yana cikin shirin shi na babban kayan day saka a jikin shi wanda ya fito mai da shekarunshi a fili kana ganin shi zaka hango kamalla da kasaita a tare dashi ga kwarjinin shi a fili. Daga inda nake zaune nayi mai ina kwana duk da banji dadin rashin nuna kulawanshi da bai nuna muna ba lokacin da mukazo, duk da na kirshi bayan mun sauka din. Sai baizo ba bai kira ba don haka na danji zafin hakan a raina, kisan halin namiji mijin mace biyu baibar kowa ba don haka yanzunma shima a tsarge ya shigo din yana dan kame kame amma haka na daure na nuna ba komai a zuciyana kamar yadda na saba yi mai duk daya fahinci hakan gareni a fuskana. Bayan na gaidashi yana min ya hanya na basar tare da fadin har zaku tafi mosque ke nan yanzu ina duban lokacin a wayana. Time ya kusa ya fada a kasalance yana gyara tsayuwan shi lokaci guda ba tare dana kalleshi ba nace sai a tafi dasu babami suma suje su hau sallah idi yace OK idan zasu yarda ai saimu tafi nima zanso hakan ya fada har lokacin yana kallon fuskata. Mikewa nayi daga inda nake da sauri na fita na barshi dakin tsaye ya bini da kallo tare da mamakin hali irin nawa yana girgiza kai. Na samu umma ta saka masu kayan da wani kanin mukhatar din ya dinka masu don hawan sallah idi don tun muna can ya turo min photo kayan a waya. Dan Allah ya dorawa yaran farin jini sosai ga wanda ya gansu sai yaji yana son su a tare dashi kaunarsu yana shiga zuciya farat daya ga wasu . Ida mai karatu baki manta ba farko labarin mukhutar din na fada maki wanan guy din sunzo wurin shi tare da mahaifiyan shi kan a taimaka mashi da sana,anyi a lokacin. Mahaifan shine wanda suke mahaifan su daya dana mukhutar din kanin mahaifin mukhutar dine da har yayi sanadiyan daukan mukhatar zuwa kasan waje dashi sai suka samu matsala dasu a lokacin kuma ya hadu da mahaifina. Yanzu muna zaune tare dashi a can shima yana zuwa yana dawowane don international business sukeyi dashi ta haka nake samun daman turo kayana zuwa Nigeria wa anty Amarya da mommy dasu gwaggona Amina da kudidi suna sayar min. Ina kuma turawa sisters dinshi suma sai gashi Allah yasa muna albarka sosai ga harkan suna samu ina samu sosai ayanzu ga aikin company da nakeyi a can tare dasu. Wanda koshi saida akasha fama sosai da jidalin hjy Falmata don tace itama sai tayi aikin irin nawa karshe ma dai yace to tafito itama ta fara aiki irin nawa din tace kuma bata yarda da hakan ba tunda bata iya ya sani. Sai dai ya dinga biyanta albashi da kudi daidai wanda company ke biyana a bata itama hakana . Don yace bai yarda ba shine sukai jidali kanshi sosai dole tazo ta hakkura ta barni ina aikina da nake jin dadin yinshi sosai araina. Wanda hakan yana kara dauke min hankali ga komai ina kula da yarana da mahaifiyata da yan uwana dake tare dani sosai da kuma aikina shi maigidan idan yana kasan mijine idan kuma ya tafi sai Allah ya dawo dashi lafiya kuma aikina dai inayin abina yadda ya dace ban dorawa kaina wahalan duniya akan namiji ba. Yaran na riko daga dakin umma muka fito zuwa part dina sai muka hade dashi a falon tun daga nisa yake sakar muna murmushi har lokacin dana karaso dasu inda yake tsaye. Mamaki ya fada har yaushe akai masu wanan dinkin haka ya fada yana mamaki nace Abba ne ya dinka masu kafin muzo kai ya jinjina ya mika hannu sai yaran sukaki zuwa gunshi. Murmushi nayi a cikin harshen yarbanci nayi magana dasu suka dan kalleshi lokaci guda da kyar suka bishivdon basu saba dashi ba sosai saboda zaman da bayayi damu sosai. A sauko lafiya daga masalaci ya wuce da yaran gidan sarki daga gidan sarki suka nufi gidan shi a can ne suka kwasa da hjy falmata wai don me zaizo mata da yaran gidan ta. Sun danyi sa,insa dashi inda ya kwashe duka har da yaran ita falmata din suka wuce zuwa gidan mahaifiyar shi ancen yake fadawa hjy abinda falmata din tayi kan yaran yake fadi wana zai kawo masu babban matsala a tsakaninsu. Sai gasu gidana lokacin duk muna falo a zaune har Ammar taro na mutunci suka samu a wurin mu ina jin yaran na tambayan shi who is she Dad ? Your stepmother ya basu amsa sai dayan tace but mum told us that she is wicked and,and also a witch she is too dangerous i mean mun said. But she is nice dayan ta fada to nima shinagani ai amma mum tace muyi hankali da ita ta fada tana dan satan kallona inda nake tsaye ina cirewa yarana kayan jikinsu da yai masu nauyi ajiki. Wani tsawa ya dakawa yarinyar lokaci guda har ta dan kadu yake fadin she is my wife yaranta kuma sune blood brothers din kune nan ya shiga yi masu bayani suna kada kai. Dakina na koma don yayi baki a lokacin saidai raina yayi matukar baci jin yadda matar shi ta batani a wurin diyanta duk saboda kishi . Kinshin da ba a gida daya muke zaune tare da ita ba a lokacin amma saboda tsananin kishinmuna mata ta batani haka a wurin yaranta da haka suma zasu taso kishin su ya girma a zukatansu. Na gama fadawa umma komai ta nisa tare da fadin ai yadda ya nuna shine daidai tunda yatsawata masu atake kuma yayi masu nuni da suso yan uwansu na jini a zuciyar su. Da dare ya dawo gidan mu a nan zai kwana saida na gama hada mai komai da yake bukata kafin ya kwanta na juya zan fito. Naji muryanshi yana fadi ina zaki naso muyi dan magana dake yanzu ya fada hankalinshi akan laptop din dake gaban shi tun shigowana dakin yana aiki a cikinsa. Zan ba babami magani naji kamar mura nason kamashi OK baida matsala ya fada tare da dan dago kanshi a lokacin na juya na fita har lokacin bawai na sake bane hakana. Nasamu yaran suna barci a jikin umma na shiga dakin take fadin kiba yaron nan magani kafin barcin shi yayi nisa na amsa da shina dawo in bashi a yanzu. Da taimakon umma na bawa yaron magani kafin naji ta ambaci suna na juyo take fadin kada wanan zancen yasa ki sauyawa mijinki a yanzu sahiba. Idan kinyi duba ga irin halin abokiyar zaman ki meye laifin shi a cikin zancen nan tunda
Chapter 336 · 0% Book details