Sashe 149
Ana Dara Ga Dare Yayi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Hjy fatima farar macece sol saidai bata da tsayi sosai amma kuma ba za a kirata gajera ba kuma mai tsawo ba tana da kyau don kana ganin ta kasan tayi zamanin kyau irin nata Tana da dan fada sai dai ba irin sosai din nan ba can don inda tayi nan take barin zancen bazata rike a rayuwan ta ba. Nagane hakan ne don yanzu a tare dasu nake dan zaman su damu a kasan nan da zasuyi ya azamin nauyin fita dasu ko zama ina kulawa dasu a cikin gidan don ganin masu shigowa da kuma motsin su. Saidai gaskiya hakan ba a banza zance mukeyin aikin ba don akwai alheri sosai da muke samu ga hakan a kulun daga garesu kinga ko aikin bai zama na banza don baga albashi kawai muka dogara bake nan ai. Ranan danayi wanka zan fara sallah a gudan su sallah azahar ya riskeni ranan ana sallah na mike na shiga bandakin da nake kewayawa a cikin sa na dauro alwala nazo na tayar da sallah anan falon su Allah da ikon shi hjy ta gitto ta ganni ina sallah anan ta shiga tana mamakin irin halina haka babu sakewa ko zakewa ga sha,anina duk da yanayina ya nuna akwai hutu a tare dani amma ina nuna a karkashin su nake komai a cikin girmamawa zan masu shi. A, a kece kike sallah anan baki shiga daki ba ta fada kafin ta shige ta kara da fadin idan kin idar zamu fita dake unguwa dan an jima kadan ta fada a karshe. Na idan na dan zauna nayi addua kafin na jawo jakkana na fito da kayan makeup din dake ciki na gyara fuskana kadan koshi naga duk macen da zata shigo a cikin kwaliyan ta take a fuskanta yasa na dan fara yin make din haka ba dabi,ana bane yin makeup. Daga driver saisu biyu da yarta muka shiga motan zuwa wani unguwa mai nisa dasu munje gidan wata mata dana gani wurin addu,an ranan so close to her . Mun zauna a falon matar sun gaisa muma mun gaisa da ita suna dai hiran yaushe rabo a tsakanin a cikin hiran sun ne naji ranan da zasu koma. Kusan sau biyu muna hada ido da wanan matar sai tayi saurin kawar da idonta daga kallona saina fara zarginta don mugu bai hada ido da mai iska sau uku ko biyu. Can matar take fadin wanan kyakyawar yar dai tun shekaran jiya nake ganin ku tare da ita hala da ita kuka zo daga can ? Hjy ta dago ta kalleni tana fadin wai wanan yar a, a anan dai muka sameta danki ne ya hadamu da ita tun zuwan mu yanzun ma rakomu tayi nan kin san shi da rashin yadda . Haba wanan ai kyauta haka abin tsorone sosai dan tafi kama da yar ruwa saboda kamannin ta ai dariya hjyn oga tayi tana fadin mace maikyau sai ta zama wani abu kuma don kyaun ta matar tace nan lagos nefa hjy fatima. Sai matar ta kara kollona tana dan murmushi take fadin anya kuwa wanan ba sallon yan zamanin nan bane kuwa ya fito maki dashi don wanan ai batai kama da yan aiki ba sam. Hjy Fatima mahaifiyar shi bata gane mai matar ke nufi ba tace ai ba aikin gida nake nufi na dahuwa ko wani goge goge ba a ma,akatan su dai take aiki tare dasu. Yaran nan sun iya bata sau wallahi haka dai ya fada maki shi amma wanan ai ba haka yake ba kema kin sani sabo kawai ya turata kuyi kada daga baya ki nuna baki son zancen. Anya haka zancen nan yake kuwa don nasan halin sha,aban sosai ke dai mubar zancen matar ta fada saboda bata dauka na iya hausan da sukeyi din ba yasa ta juye yare zuwa hausa sama sama don bata iya yaren sosai ba. Mikewa tayi zuwa kawo mana wai abin tabawa duk da bata sanda zuwan mu ba haka ya ban daman kallon ko ina na falon nata don hankalina bai kwanta ba a lokacin. Can idona ya gano min abinda yasani mikewa da sauri don yadda na zabura saida suma suka fitgita dani don tsoro. We most live now before she come back with her evil act now now na fada cikin fidda idona waje ina umurtan su da hakan. Aishan tsoron yadda taga mayi taji ta fake a bayan uwarnata don saitin kafanta nake kallo sosai ganin basu tashi ba yasa na nuna abin da hannu ina fadin go back to ut owner don't try to touch any one here again. Ai Aishan saita mike uwar ma hakan suka fara tafiya ban fita ba saida suka fita nabi bayan su har sun shiga mota na bude na kalli gidan ina fadin back to ur send d evil sprit. People are saying dis to hajiya ban taba yarda ba har hjy zata iya cuta min duk irin taimakon da nayi mata a duniyan nan ashe. Mama i told you duk ranan da naganta ko zan ganta sai nayi mafalki da ita da wasu abu suna bina a baya zasu kamani kuma na fada maki tun kan muzo nan din. Driver kan sai gudu yake shararawa da motan har muka kai gidan nasu a waje muka samesu da Felix da Jimoh zasu fita. Fasa shiga motan yayi ya tsaya da mamakin ganin mu mun dawo lokaci yana kallon yaga hankalin su a tashe suna fitowa sai fada mahaifiyar su keyi abinda yasa ya fara takowa zuwa inda suke ke nan. Baku sameta a gidan bane ya tambaya farko mun ko sameta saidai zance ya juyane kuma uwarta fada meya faru tace ka tambayi wanan yar ita ta gani koma meye tasa mu tasowa yanzu mu bar gidan idon shi ya lumshe yana fadin ya Allah. Dama nasani nasani mama kada dai kice zan rabaki da kawarkine na yarinta don a tare na taso na ganku kike fada amma wanan matar yanzu ta canza saboda kudi. Babu abinda zai faru dasu mugun abinta ya koma akanta ya bita ita da yaran ta yanzu kin riga da kunfi karfinta ko a duniya. Duk suka tsaya suna kallona a inda nake tsaye kafin tayi karfin halin fadi No ki bari ke yarinyace baki san komai ba mun dade tare da ita mutane suna gada min wanan maganan gashi yau ya zama gaskiya . Mommy idan baki yarda ba zata kawo kanta gidan nan a yau din nan ta roke gafara don tana can cikin wahala yanzu haka mun barta abinta ya koma a kanta. Itace ta kiraki da safe kan kada ki wuce ba kizo gidanta ba kikai mata alkawarin zuwa din kafin kizo ta shirya abinda zatayi maki din taso amfani da jinin kune kawai ko naki kona yarki. God forbid bad things Allah ba zai bata sa,a ba har abada cool down mommy zata zo yau din nan ta sameku ai na fada na juya zuwa wurin da abokan aikina suke na barsu a nan suna kara tataunawa akan zancen. Karshe dai ogan mu bai fita zuwa inda zasu tafi ba din suka kwasa suka koma ciki don suna gardama cewa kodai firgitasu nayi kawai ba abinda na gani zan hadasu da mata yar tace ai a bari a gani tunda nace zata kawo kanta garesu ranan. Duk muna falon gidan a zaune har su wanan lokacin hiran kasuwanci ake da mr Jimo muna sauraren su, muka jiyo hargowa a wajen gidan. Felix ne ya mike yana fadin ihun meye haka yake ji a compound din gidan yana fita yake wanan maganan sai gashi baikai ga fita ba sun juyo da maigadi yana fadin. Hjy na dat that ur friend come de shout ebi like say she don be mad today wooo . U no here how she de shout ur name, saying dat make u na forgive am woo , d tin meke me surprisee amm woo, which one of my friend ta tambaya yace dat big Alaja who de always come dis house if u are around. Tayi wani irin tabawa tana fadin shike nan batu ya zama gaskiya ke nan shi ya mike da sauri suka bi bayan shi zuwa waje a cikin mamaki. Daga hjyn har diyanta duk sun firgice suke suna kallon kofa har yemisi dake wurin a tare damu don duk mazan sun fita a lokacin. Sai gasu sun shigo falon tare da ita lokaci guda tana faman soshe soshe tazo gaban hjy takai gurfane tana fadin kimun rai ki raimakeni. Nayi kuskure danayi kokarin taba ku nayi kuskure ba yau ba ina kai maki hari dake da yayan ki kuna kubuta daga track dina yau nayi niyar in gama daku gaba daya don haushin da nake ji naki na kin fini da komai diya ta nuna yaran kudi da gida da komai kin fini Fatma kin fini why zaki fini yanzu bayan nasan na fiki komai muna yan mata. Hannu bibiyu hjy ta dora a kai tana fadin mabinu da harshen yarbanci tare da fadin na shiga uku dama haka kike mansura ban sani ba. Ta kai ga cire dan kwali tana fadin ki min rai ki taimakeni nasan nayi ba daidai ba gareki don Allah ki yafe min ki yafe mun fatima tana hada hannayen ta wuri daya. Hjy din da yar ta suna ja da baya ganin haka na dan tako zuwa inda ogan yake tsaye ina fadin yace ta tafi daga yau ta fita hanyar su ga baki daya. Haka yayi sai tayi wani irin lankwasa can ta dago bata ko tsaya kallon su ba tafita daga gidan kamar mahaukaci duk wanda ke wajen lokacin jikin shi yayi sanyi sosai lokacin. Mommy kan ta gaji da korafin nan nasu a yanzu don har tsoron ganin kiran wayan Nazifa take yi don tasan karane zasu kawo mata a lokacin. Yauma din dai tana jin kiran ta saida gaban ta ya fadi tasan magana gudane dan kullun tana dauka ko sallama babu take fadin. Nagane kece ke daurewa Abubakar yake min wullakanci idan bashi ba don me zaki dinga bashi abinci a gidan ki yaki cin girkin mu a nan. Nazifa kinsan da wace kike magana kuwa