Sashe 213
Ana Dara Ga Dare Yayi Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
zancen haka a nan ai bai dace ba a tsakanin ku muyi abinda ya hadamu yanzu a nan shine mafita kan Alh a yanzu baffa buhari ya fada rai bace. Daga can gefe daya kuma baffa hamza na fadin meye abinjin zafi a cikin nan yanzu don haba don Allah haka bai dace ba abinda kukeyi yanzu baffa Abdullahi ya fada a harzuke. Tafiya nakeyi duk da sunana da Felix ke ihun kira haka baisa na tsaya ko in juyo in kalleshi ba don yadda nake jin idona ya rufe a lokacin sam na manta a wani kasan muke ma. Kai tsaye masaukin mu nakai kaina saidai kowan su yayi mamakin hakan zakace na san garin ne na kuma taba zuwa kasan . Bansha wahala ba wurin kai kaina dakunan da aka saukemu a cikin sa, ina elevator karshe da zai sadani da dakunan suka iya nasaran cin mun a cikin sa. Do u want to kill your self Sahiba ki duba yadda kike ratsa motoci haka ba tare da damuwa ba a zuciyar ki . Idan kin kashe kanki ko wani abu ya sameki me kike son in fadawa yan uwan ki ko mahaifiyar ki ? Kallon shi na dingayi kawai lokacin da yake magana yaci gaba da fadin don ummi ta fadamaki magana zaisa kiyi wanan abin idan wani abu ya sameki fa ke baki tunanen hakan ne ? Kaina na dukar kasa saiga hawaye takaici ya zobo min yana sauka a fuskana nake fadin a cikin karfin hali don kukan daya zo min din nace. Kasa a mayar dani Nigeria don ba zan iya ci gaba da zama haka mahaifiyar ka tana min wani zargi ba na daban don kawai ni ba yar kowa bace ina aikine a karkashin ku. Elevator din ne ya bude lokacin mun kawo inda zamu sauka ke nan zuwa wurin dakunan namu fita mukayi gaba dayan mu sai ya juya ya kalli Felix yana fadin ka koma can ka dauko min briefcase dina yanzun nan daga haka ya biyo bayana a daidai lokacin dana bude dakin da aka kama min na hotel din da muke a ciki. Shima lokaci daya ya biyoni zuwa cikin dakin mamakin hakan ne yani sosai sai tunane nake me nayi na rashin gaskiya ko nuna wani halin da Alajan zatai min wanan mumunan zato a kan danta da bamu taba tsayuwa ko na minti talatin ba dani dashi. Muryan shine a bayana yake fadin nasan wanan ba plan din ummi bane nasan daga inda zancen hakan ya fito. Don ko jiya mun dade muna magana a kanku tare da ita bata nuna min akwai wani jin zafin ki a zuciyar ta ba saima kara yabawa da kwazon aikin ki da tayi min duk a jiya din nan da kukazo. But why yanzu ummi zata fito min da wanan matsalan haka tana kokarin rushe min farin cuikin dana rasa na shekaru da dama kan wani bukata can nasu na daban. Watau da gaske mrs kubura keyi bazata daina abinda ta shirya min ba irin wancan karon ita burin ta ke nan ta assasa kiyayya da bakin ciki ko yaushe tsakani da ummi ? Look Sahiba duk da nasan ba zaki gane inda zancen nan ya dosa ba a yanzu ina rokon ki wani alfara kiyi min koda sau dayane kawai a rayuwan ki . Sai lokacin na sake dago ido na kalloshi inda yake din tsaye a cikin bacin rai ganin na kalloshi yace yes ki taimaka min koda sau daya ki taimaki rayuwa na please . Kada ki bari suyi nasara akan ummi dani sai kin daure da wanan taumakon da zaki min a yanzu ki nuna wanan zancen da ta turo ummi ta fada maki bai dameki ba haka kuma zaton su a kan mu din gaskiyane ki barni da sauran plan din zan karasa da kaina insha Allah. Ganin irin kallon tuhumar da nake maine yasa ya kara fadin please kada zuciya ya hanaki irin taimakon da kike muna a baya nasan zaki iya hakan ya kara marairaicewa kamar zaiyi kuka a lokaci guda cikin tashin hankali. Hakan yasa naji tausayin shi sosai naji wani irin ba dadi a lokacin don ko banza shine wani haske na rayuwana da ayanzu nake amfana dashi don haka shima dole in taimakeshi kamar yadda ya taimakawa rayuwa don nasan dai ko ya amfana dani shima ya taimake ni ai. Yana batun zube min nayi saurin fadin please Sir i can help you yadda kake so zan daure in shanye duk wani bacin rai da zan gani a wurin mahaifiyar nasa da sauran yan uwan shi don bansan manufarshi ga niyar yin hakan da yake son in masa ba a yanzu. Felix ne ya kwankwasa kofan ya shigo don a bude kofan yake har lokacin ya shigo dauke da briefcase din oga din a hannun shi. Yana mika mai ya karba yana maigodiya don oga badai godiya ba kan gaskiya ko dan karamin yaro kake kayi mashi abin kyautatawa sai ya godema. Wanan wani haline nasa na daban don gaskiya ni kan ba zan iya kiyasta maki halin salihanci da kirki irin nasa ba don shi mutum ne na daban zakaita magana yana shiru kamar baya jin ka. Sai can idan yaji inda ya dace ya dan bada amsa zai dago ya fadi kalma daya zuwa biyu shike nan iya zancen shi. Laptop din shi ya dauka ya danyi abu a ciki duk muna tsaye a cikin ladabi muna kallon shi kafin ya dago yana fadin zamu fitane ya aikawa jimo sako suna jiran mu a waje yanzu. Felix ne ya fara fita daga dakin kafin ya juyo kamar rada yana fadin plan din mu zai fara aiki daga yanzu sai ki kula ki daure sosai ya fada a hankalin cikin kalman hausa da dukan mu kinsan hausa ba zama yayi sosai a bakin mu ba. Wasu shaguna muka tafi an yace kowa ya dauki abinda ranshi ke so a wurin a gaban idon kowa da muke tare yaja hannuna muka nufi wani sashe na wurin . Kaya ya fara jidan mai yawa irin na matan musulmai na kasan inda ina kallo yemisi sai cika take tana batsewa ta dauka wani sabon gani ba bazata tayiwa idon ta akan mu ba yemisi ba kawai duk wanda ke tare damu hakan ya dauka lokacin. Sai dare sosai muka dawo masaukin mu da kaya niki niki shida kanshi kamar gaske ya taimaka kama min kayan zuwa dakina. Ban tsaya jiran komai ba bayan fitan su bandaki na fada nayi wanka tare sa alwala na fito nayi sallolina sai barci don banjin cin komai a lokacin. Washegari kamar yadda yace karfe takwas duk mun shirya zuwa airport mukai ban kwana da wanan kasan mai dadin zama da ni,ima dukda zaman kasan yazo min da akasi saidai hakan bai hanani jin wani iri ba lokacin. A nan airport tun nufar mu wurin muka hagoshi suna magana da wasu mutanen kasan na Turkeya su biyu suna tsaye . Yana saye a cikin suit dark blue clour daya kara haska farin shi ya fito mashi da kurciyarshi a fili ba zakace ya haura talinta da dan kai ba lokacin. Mutum akullum shekarun shi gaba sukeyi yana kara canzawa amma shi sai ka rantse da Allah a kullun kara masa kuruciya akeyi idan ka kalleshi. Ganin muna tun karo inda suke tsaye din ne yasa ya juyo yana kallon mu da alama cikin mutanen akwai wanda yayi magana a kan mu. Wani iri naji lokaci guda faduwan gabane ya ziyarceni a lokacin ga tsikan jikina da yai wani yarrr har zuwa yatsan kafana ganin yadda yake sako min murmushi daga nisa. Kafin mu karasa sai ganin Alaja da mutanen ta su shidda din nan a tsakanin mu dasu don haka sun tare muna hangoshi da mukeyi . Haka yasa a hankali na sauke ajiyan zuciya tare da ja na tsaya a wuri daya don dan tako kadan ne ya saura dama tsakanin mu dasu.