← Book details Ana Dara Ga Dare Yayi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 147 OF 337

Sashe 147

Ana Dara Ga Dare Yayi Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

fada kafin tace Lalalala haram haram ta fada tana yare cikin larabci shima yaren ya fara mata jikin ta yayi sanyi sosai tana fadi kalas kalas yallah yallah. Ta juya turanci tana fadin shine tsiyata da mutanen nan wallahi baka zuwa sai wani ya nemi da yahalaka yaga bayan ka. Ganin zata kaiga barin abin ya tabi jikinta yadda take fada na taka zuwa inda suke a cikin ladabi nace dashi zancire gyalen a jikin ta yanzu sai ya yafa mata na jikina kafin akawo wani Adnan zaizo yanzu dashi insha Allah. Hakan mukayi yaja wanda ke jikina ni kuma na cire nata ya yafa mata nawa din tayi tagumi tana kallon ikon Allah gabanta sai faduwa yake mata anan ya fada mata cewa kada su yarda su taba komai naci a wurin. Adanan ya kirani ya dawo na fada mai inda muke yashigo ya mika min na walwale kai mata gyalen maikyau dashi ta yafa ledan mukai amfani muka saka wanan a ciki. Iya tunanen duniya yayi shi a rayuwan shi don ya gano gaskiyar maganan da yaji a bakin Nazifa matar shi don yana son ya dago wanan case din ba tare da sanin kowa daga cikin mahaifan shi ba. Abune wanda yake son binciken siri don haka gaba daya a yanzu sai bai yarda da yan ahalin shi ba don duk yana zarginsu dayin rubda ciki a gadon uyan maruyun Allah da aka bari bayan kashe masu mahaifi da gangan . A wanan fanin yasan yana da evidence ko umma ta ishesu shedan komai ga irin bayabar da tabayar a lokaci don an kashe mata miji a gabanta ta kuma san ko suwaye sukayi shi. Saidai ta ina zai fara wanan binciken nasa yanzu karshe dai yayi tunanen zuwa police station ya binciko wanan case din saidai hakan ba zai yuyu a gareshi ba sai a sirce zai gudanar da komai yadda ya tsara din. A gidan sa kuma duk wani dabaran da nazifa zatayi mai yaci abinci ya kaucewa wanan zai fita yaje waje ya hada take away ya zauna a motan shi yaci don kada wani ya ganshi girman shi ya fadi. Yauma zai fitane da safe yana shiri tana zaune gefen gado ta zuba mai ido tana ba yar ta nono take fadin. Nasan a gidsn hjyn ku kake cin abinci yanzu don baka yarda da girkina ba kana nufin za a hada kai danine a cuta maka ko me koda yake ma ba kaine mai laifin ba mommy din ai tasan hakkina ne yanzu in baka abinci ba ita ba amma take baka don kawai a kuntata min. Dakatar da abinda yakeyi yayi yana kallon ta tare da fadin Nazifa kanki daya kuwa koda a can nake cin abincin ma laifi ne idan naje can naci abincin ? Ai kin fi kowa sanin cewa mommy ce mahaifiyata don baki da kunya zaki bude baki kina fadin wanan banzan maganan haka a gabana yanzu. Ta tabe baki tace dama ai haka akeson ya kasance a tsakanin mu shiya ake kirkiro abubuwan da akasan zanyi magana a kanshi. Saukin abindai mutum bai iya rabumu saidai yayi sherin shi ya barni wallahi indai nice. Ya rasa abinyi sai ido daya zuba mata wai uwarshi take fadawa wanan maganan haka yana mamakin rashin iya maganan Nazifa haka Wace ma bata iya boye sirin uwarta da ubanta ba wajen katobara wa zata ragawa ga duk abinda ya fito a bakin ta wautane ko rashin tarbiya ke damun ta ? Wani haushi ya shigeshi nata ta ya juya yana saka talkama a kafanshi a cikin kulewa da ita yaji muryan ta tana fadin wai fitan zakayi baka karya ba da gaske ? Don kawai na fadi gaskiya bai kulata ba sai tura wayan shi da yayi cikin aljihun ya dan juyo ya kalleta a cikin takaci yasa kai ya fita yana jin ta tana mashi masifa har ya bar jiyo muryanta don nisan da yayi da ita lokacin. Haka muka wuni a wanan wuri Allah ya taimakeni ina fashin sallah a ranan don haka na biyewa abinda sukeyi har aka gama muka kwasa zuwa gida bayan anyi rabe raben gift masu tsada da jawabai daga yan uwa da abokan arziki da suka san mamacin a baya. Dole saida muka koma gidan nasu tare dasu don haka nakai yamma sosai a ranan ban dawo ba sai dare na shigo gida na samu umma a cikin damuwan rashin dawowa gashi na wuni ban gida a ranan. Koda nayi sallama a kofa na tsaya ina cire takalmana a cikin gajiya na jingina jikina ga bango ina kallon umma dake amsa min sallaman yaran Avdulhamid ne a falin tare dasu suna kallo suka dago suna kallona tare da yi min sannu da dawowa. Na karba na nufi cikin dakina ina fadin umma ina zuwa don a matse nake na watsa ruwa don yanayn da nake ciki a lokaci. Na dade a cikin bayin na fito na zauna na gyara jikina ba zancen yunwa sai barci a tare dani don haka na dai fita naje muka gaisa da umma ban dade ba nayi mata saida safe na dawo dakin na kwanta. Washegari ban tashi da wuri duk da nasan gidan Oga zan koma a ranan aiki kuma an fada muna mu fito da wuri akwai abinda zamuyi da safe. Sai dai gaskiya gajiya bai barni nabi umurnan ba a ranan nafito na samu umma tayi alale wanda yaji kwai sosai cikin sa da kifin teku sai kamshi ke tashi suna zaune har yaran Abdulhamid suna ci yaban shawa sosai amma na kasa zama naci ko kadan saboda saurin da nakeyi a lokacin. Goma ya wuce da yan mintuna a lokacin haka nayi masu sallama a gurguje na fita daga gidan na samu abokan aikina har yemisi suna falon farko zaune muka gaisa suke fadin karfe nawa na fito nida akacewa mu fito tun safe. Wuri na samu na zauna oga jimone ya fara magana kan aikin mu na jiya da mukayi ya yabawa kowan mu daba,a samu wani kuskure a wurin kowa ba a lokacin. Yar aikin gidan ce ta fito tana fadi a cikin yaroba ance Sahiba tazo idan tana nan jin hakan yasa na mike nabi bayan ta muka shiga ciki tare. Bakin su nan nan basu tafi ba son haka gidan yake da jama,a cike gashi kayan aikine a jikina na saka bakin wando da riga fari ta ciki sai corth din mata dana saka baki a sama kayan sun matukar karban jikina sosai. Suna daki da hjyn shi ta sauka a nan na samesu zaune tare da wasu bakin su suna hira na gaida su a cikin mutunci na mike zan fita hjyn tace oh Allah sarki yarinyar jiyace ashe ? Na danyi murmushi zan juya in fita muka hade da Ogan mu da zai shigo dakin da suke din don yayi sallama da bakin da sukazo masu daga arewa zasu koma gida jirgij karfe daya na ranan.
Chapter 147 · 0% Book details