← Book details Ana Dara Ga Dare Yayi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 300 OF 337

Sashe 300

Ana Dara Ga Dare Yayi Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

dangi. Shima haka modibbo tun bayan wayan mu dashi kalamaina suke damun shi a rai don shi baiga abinda zaisa muce mun yafe dukiyan mu alhalin hakkin mune a hannun iyayyen su. Da suka kwace da karfi da yaji daga manalakinshi kowa ya sani don me yanzun zamuce mun barsu dashi me hakan ke nufi kenan a yanzu. Da wanan damuwan da yake ciki ne har yashigo gaida mommy data kula dan nata yana cikin damuwa a lokacin ba zato yaji ta jefo mashi tambaya . Hira take mai na sabon saurayin da Faiza tayi Bello dan zaria duk yan uwan nasa na zaune a falon don hakan dabian sune zama a cikin falo tare dashi idan yazo saidai har in wani abu na muhinmin zasu tattauna da uwar yan uwan nasa zasu daga su basu wuri ko idan sun san da zancen ba zasu fito ba ma . Yayi kuri ya rike haban shi da hannayen shi yana kallon kasan dakin da idanuwan shi a lokacin yaji muryan mommy na fadin wai kai lafiya kake kuwa ana ma bayani ka yi shiru haka meke damun zuciyar ka kuma ? Har lokacin bai dago a yadda yake ba saida hauwa tace yayan mu dakaifa mommy take magana sai lokacin ya nisa da dan karfi ya juyo yana sauke ajiyan zuciya lokaci guda. Lafiya kake kuwa ta sake maimaita tambayan ta tana kallon fuskanshi tare da kara nazarin shi lokaci guda. Fuskan shi ya shafo a cikin yanayin damuwa kafin yace wallahi mommy zancen su daddy ne dai yake daure min kai wai mutanen nan suce abar zancen har su daddy su yarda da hakan ? Ma,ana fa sun barsu da Allah kuma sun yarda da hakan ya fada a cikin wani irin yanayi na damuwa sosai a lokacin a fuskan shi har zuciyar shi. Wai su Sahiba kake zance dama yace wallahi mommy to nima nayi ta tunanen hakan ai saidai ba yadda zakayine tunda mahaufin ku yanzu na kula ko zancen baison ajemai dashi. Nima abindana gani ke nan mommy toba sai mu saka mai ido ba nidai yanzu nasan mutanen nan basu rikemu da komai ba wallahi. Ko mutumin nan daya fito neman Faiza ta dalilin tane faiza tace min ya santa har suka kulla dashi to akan me zata faman rike bayun Allah a raina su suna bin nawa da alheri. Jiyan nan hjy karima ke fada min ko tana ganin nasani ne tunda nafi kusa da su oho ? Wai sunyi waya da sahiba din akan zancen baby dake gida ko haka bai ishi mutum ba don Allah ? Ta juyo tana kallon dan nata amma mommy ai daddy yayi masu shima akace inji Nabila da tunda aka fara zance ta hade fuskanta wuri daya. Babu abinda ke cin zuciyar ta sai zalla bakin ciki da takaicin jin an ambaci wanan yar rainin wayau sahiba don hassadan Sahiba ya fara yawa a zuciyar ta har yakai yanzu tana kokarin cusawa yan uwanta wanan akidar. Saidai a kullun ta dauko zancen batacin riba a wurin yan uwan nata don sai su nuna su basuga wani illa ga Sahiba ba gaskiya wanan yasa yanzu take yi iya ita don kawai Sahiban da sunan nata a yanzu yake yawo a cikin dangi dama wa yanda ba dangi ba duk sun fara sanin ta. Shiyasa yanzun ma da taji an dauko wanan zancen yasa ta saka bakinta saidai bata sha da dadi ba a gurin mahaifiyan nasu da yayan su don sun zageta tas. Abinda yasata tashi a cikin fushi ta shige zuwa cikin daki tana magana ciki ciki don katsetan da akayi kan hakan a yanzu ta rasa meyasa mommy din ke ra,ayin duk wani zancen daya shafi sahiba a yanzu. Meya kawo haka ta tambayi kanta tana jan tsuki tare da kara jin tsanar yarinyar a zuciyar ta aai meya dama haka wani lokaci abu ks kasancewane ? Wai yau sahiba ce take taka duniya yarinyar da abaya can saima sun bata wani abubuwan take amfani dashi wai itace yanzu ta koma haka lokaci guda. Ba abinda ya kara ja mata takaicin yarinyar sai irin yadda har iyayyen su a yanzu suke nuna ita din fa ai watace don kawai suna takama da cewa dukiyan hannun iyayyen su nasune kome ? Tsuki taja tana lumshe idanu tare da fadin shiyasa tun farko sam yarinyar bata kwanta mata a raiba ita balle yanzu data koma wata yar kabila sosai ga ba nauyi ko kunyar kowa a idon ta sam. Saidai shi Abubakar modibbo na fitowa daga cikin gidan ya samu motan baffah hamza danasu baffah Abdullahi sun shigo ashe suna wurin daddyn su lokaci. Bai tsaya ta kansu ba yaja motanshi ya fita gida bai dade da fita ba sai gashi suna neman shi an kira wayan shi yace yanzu yabar gidan gashi ya kama hanyar zuwa kano. Sun nemi ya dawo don haka dole ya juyo ya dawo don amsa kiran su saidai yana shiga falon ya samu basu biyu bane tare da daddu din kamar yadda ya zata ya samu harsu baffah buhari dasu baffah gyade sunan gidan wurin daddy din a falonshi. Yan mintuna bayan shigowan nasane baffah hamza ya fara magana kan haduwan nasu yana fadin duk da wanan tarom a yanzu kai modibbo bai shafeka ba namene mu iyayye zallah. Amma a wanan zaman dole mu nemoka don kai kasan abinda ya dace ga abinda muke tattauna a yanzu din wanda ba komai bane sai zancen auren yar uwanka tace lagos watau sahiba. Duba ga yadda abin ya taso haka lokaci guda ba tare da masaniya ba ko wani shiri don haka mukeson a bangarem mu mu iyayye musan irin gudun mawan da zamu taimaka dashi a wurin wanan sha,anin duk dashi mijin ya nanata muna cewa shifa matar shi kadai yake so baison wani abu daga garemu. Dan murmushi kusan kowa ya sake kafin tsohon nan yace don ya raina da kuran mu ko me ya fada a dan bacin rai. To nima dai na fadi hakan a gaban shi amma saiya nuna min koda bashi bane yana da hakki da nauyi akan yarinyar shima. Baya ga haka zai zama kamar barnan dukiyane tunda shi sam baya zama a kasan na kuma duk da haka gidan ko yaushe a cikin canza sauyi ake mai. Don haka don Allah kada muce zamu wahal da kanmu wurin yin wani abu yanzu din haka kuma itama yarinyar da mahaifiyar ta na dan tuntubesu kan hakan uwar tace basu da damuwa a wanan don irin bukin suna lagos zasuyi kawai a can shike nan. Lagos kuma ba a nan zasu kawota ba ke nan daddy ya tambaya sai baffah hamza din yace dashi kudidi ma tayi wanan maganan. Shine mairon tace a dole gida ai za a kawota daga nan sai a wuce zuwa maiduguri din da ita bayan sun gama nasu abinda zasuyi ke nan acan . Kai kowa ya gyada tare da gamsuwa da abinda baffah din ya fada yaci gaba da fadin yanzu kai modibbo mun kirakane muji mu a nan me yakamata muce munyi mata yanzu ?
Chapter 300 · 0% Book details