Sashe 332
Ana Dara Ga Dare Yayi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Kwana biyar nayi asibiti ina hutawa kafin na dawo gida nan ma sun bani doka kada inyi wani dogon motsi don yanzu cikin yana barazanan zubewa ne daga jikina. Wanan yasa yake kara nuna min wani irin kulawa da kauna yana kuma kafa kafa da zancen cikin kamar yadda na gargadeshi tun a asibiti da kada ya sake yayi wanan maganan ko a gaban fatimane sai idan bukatan haka ya taso ayi din .. Wanan kuma ya samo asaline kan sanin halin hjy Falmata da nayi don kasancewar ta shu,uman mace mai karfin hali da shige shige akan duk abinda tasa a gabanta. Tunda har ta iya tura min asirin da yayi tasiri a jikina ya zama dole in kiyayye duk wani siri a yanzu duk a kanta kuma don babu abinda bata iyawa a rayuwa. Anyi azumi lafiya inda nagodewa Allah har Allah ya ban ikon samu nayi fiye da rabin azumin shine baya zama wuri daya ko yaushe a cikin tafiye tafiye yake wanan ya ban dama idan bai gari sai na dauki azumina in kuma kaishi lafiya. Kamar yadda na rabawa dangi kayan azumi wanda daga wurin shi komai ya fito don dama haka dabian shi yake zai bawa hjy falmata abinda zata rabawa dagjn da mabukata a wanan lokacin amma sai ta soke kudinta taki rabawa kowa. Yadda ya bata haka ya bani nima hakan kuma na aikawa baffah hamza ya rabawa yan uwa zanuwa da shadda masu kyau da kudin abin sallah kowa yana samin albarka. Har cikin Maiduguri na aika da alheri wa yan unguwan mu ta hanyar wata malama da muke dan hurda da ita nan ma sun saka min albarka sosai tare da addua dama shi nake nema a wajen mutane addua a wanan lokacin. Babban sallah a duk inda yake gida yake komawa yayi sallah shine kuma watan haihuwana ga Fatima ta fara karatu dole sai su kadai sukazo Nigeria sallah duk da yaransu. Saidai kafin su dawone Allah ya saukeni lafiya a daren ranan sallah din na haifi yarana duk maza tagwaye sai lokacin na gane hikimar sayen abu bibiyu da yakeyi idan zai sayo kaya a duk kasan da yaje aiki. Watau ashe tun kwaciyana asibiti likita ya fada mai cewa yan biyune a cikina yake yin hakan labari ya riskesu na cewa na haihu a bazata banda shi da yasan da zancen cikin a lokacin. Duk wanda aka fadawa haihuwan nawa saiya musa hakan yace sahiba fa ta haihu cikine da ita dama wai har labari ya samu hjy falmata a lokacin suna tare da kawayen ta gidan nasu yana cike kamar ana buki wata yar uwanta tazo. Bayan sun gaisa take fadin barka fa ashe amaryanki ta sauka kuma yanzu nake ji nima na biya gidan su mariya take fada min. Wacece hakan take tambaya a yatsine tana wani bata fuska lokaci daya don daukan mara hankali tayiwa matar duk da tasan tana da hankali amma kuma baya bayada kadan ai. Da sauri matar data fahinci katobaran da tasoyi ta dan wayance da fadin au jini bafa abinda naso fadaba ke nan dama ? Sai kuma ga wani kanin ta ya shigo shima bayan sun gaisa yayi mata murnan sallah yake fadin ashe maigida ya samu karuwane haka amarya ta haifi tagwaye maza ? Zaune take saida ta mike tsaye ta fara fadin wai a ina kuka samo wanan zancen banzan haka dazun nan wacan tazo min da wanan zancen karyan yanzu kuma kai kazo dashi mutane sai ku dinga kirkiran labaran karya kawai kuna yaddawa. Shigowan kaunanta da waya a hannu falon a kuma gigice yasa ta dakata da zancenta a cikin yare take fadin dubi abun mamaki nan anty. Ta karbi wayan ina zaune a gadon asibitin dana haihu saye da rigan asibitin a jikina sai hularsu a kaina ga yaran biyu sun sha kayan sanyi masu tsada likitoci farare biyu sun da duko mukayi photon dasu. Aikin fatima ne data turo wanan photon a lokacin dama abinda nake gudu ke nan tun farko yasa na boye zancen cikin yanzu kuma ba zancen boyo ga kowa. Duk da sanyin Ac biyu dake falon bai hana goshinta tartso da zufa ba a lokacin yayinda ta kafawa yaran dake hannuna ido wa yanda kamar ubansu yayi kankisune don kama. Photocopy ke nan wata kawarsu ta fada daga gefe sai lokacin ta nisa kafin ta fara ganin duhu duhu ta lumshe idanunta a hankali tare da fadin mukhutar. Bata gudun abin kunya don haka nuna react dinta bai dameta ba lokacin ta fara fadin ni zakayiwa haka ka boye min zancen cikin matar ka ? Ku rage a falon nan yarta ta fada kafin su fara fita daya baya daya sai aminanta mutum uku suka rage ta kalleta tana fadin zaki fara haukan ki ? Zaki hanashi abinda Allah ya halasta mashine falmata ki natsu ki dinga daukan girman ki duba yadda yaranki suka fara girma yanzu fa. Wani malolon bakin ciki ta hade lokaci guda da taji ya rufe mata kan zuciya har bata iya ganin kowa a lokacin don bakin ciki wai ita falmata guda a gidan mukhatar yau akaiwa yaranta yan uba ? Bama kishiya da takewa fathting din ta fita ta bata wuri ba har da karin wasu yara maza biyu da yanzu suka shigo cikin file dinta. Amma mukhutar ya shammaceta ya gama da rayuwanta da har yaiwa diyanta yan uba a yanzu dama shi take gudu kuma ya faru. Wanan abin kunyar da zubar da mutuncin dayaja mata ina zata kaishi a cikin kawayenta dake mata kallon ita ogace ta tare gaba ta tare baya a gidan mijinta bayan cika bakin da tasha yi masu a baya ? No warnder ya fita da yaranta yau tunda safe da sunan zasu ziyara ashe yasan abinda ya shuka ke nan dama. Lalai wanan yarinyar takai shu,uma itama tunda har ta gagari rayuwanta ta kwana mata da miji har da samun rabo a hakan ? Muryan daya daga cikjn matan ya katseta dake fadin waiko ita ta haifesu ko kuwa sunyi aducting dinsune da sunan haihuwansu donsu batarwa mutane da hankalin su ? Da sauri ta juyo tana kallon matar itako matar saicewa tayi yes kina mamakin hakane meye ba za a iya yiba a yanzu aikibar mutum kawai da makircin shi. Shiru tayi tana nazari kafin ta mika hannu ta sake karban wayan tana nazarin fuskokin yaran kafin ta nisa ta fara fadin wanan zai iya zama gaskiya. Saidai akwai inda zan gane gaskiyan hakan don duk illahirin zuri,an su suna da dan cindo a karamin yatsan hannunsu idan hakane ko dole ya kasance suma a sameshi a hannunsu. Kwarai kuwa da kyau mun samu abinda zamu dogara dashi na farko da zamuyi challanges dinsu dashi bayan haka dole mu kara samun wani evedence da zai nunawa duniya yaran ba diyan mukhatar bane . Ni duk ba wanan ba a gabana duk suka mayar da hankali suna saurarenta lokaci guda din suji meye damuwanta dake ci mata rai. Ta nisa tana gyara zama tacesai wai ace yauni Falmata mukhutar yakeyiwa wanan irin halayen haka kan wata mace macen ma karamar yarinya. Au bakisan mazaba ke nan hajaju ai idan kina son kiga true colour dinsu ki bari sai sun kara maki kishiya kiga tabara da tsiyataku a wajensu kala kala dama abinda matakewa gudu da karin auren ke nan ai. Kina zaune kalau da mijinki daga sama wata tashigo ta bata maku tsarin zaman ku Idan baki kai zuciya nisa ba har a aikata abinda ba, a so a karshe. Falmata ki natsu ki yarda da kaddara kinga irin abinda yasa tun farko suka boye maki wanan zancen cikin ke nan don irin wanan halinda kike nunawa. Ke yanzu duk abinda ya faru dake a baya kin manta ke nan a yanzu keda aka samo rayuwan ki da kyat daga ballewan jini da ki kasha fama dashi. Ace wai mutum dan musulmai, amma baya tawakkaki da duk kalan kaddaran da Allah ya aiko ma bawa dashi. Mikewa tayi fuuu ta wuce zuwa sama inda dakunan kwanansu yake tabar kawayen nata tare da yan uwanta a falon. Yadda kowa yaji zancen haihuwana yake shiga mamaki kwarai don sam ba wanda zaice yana da labarin cikin jikina hakanema yan uwana har ummana dukda tasan akwai cikin saidai bata san yaushene watan haihuwan nawa ba. Lokacin daya kirata yana sheda mata zancen haihuwa da ace wanine ke fada mata wanan maganan ba mukhutar ba da ba wasa a tsakanin su. Da sai tace maishi wasa yake mata ko yana zolayanta akan hakan wai Sahiba ta sauka lafiya ta samu babies twin's maza haka maganan yazo mata a bazata . Har yaushe Sahiba din tayi cikin daya isa haihuwa ke nan koda mukazo sallamanta zamu tafi cikin na ajikina har ya tsufa a lokacin. Gashi ya fada matacewa zuwa tuesday zasu tafi daga ita har Ammar da gwaggo kudidi sai gwaggo Amina wanan tafiyan nasu ya kawo muhawara sosai a cikin yan uwa. Don sun fara fadin yanzu ke nan su gwaggo kudidi nafi dauka a matsayin yan uwa a gareni fiye da sauran yan uwa don me komai ya taso nawa sai ace su gwaggo kudidine kawai zasu tafi ? An rigada an masu komai na tafiyansu a yanzu don haka dole kowa yayi hakkuri da zancen zuwa tunda su ta zabi zuwansu tun farko don haka ke hari da Asiya dake Addah sai kuyi hakkuri a faki gaba kuma, ai yanzu aka fara. Don dole suka jaye zancen tafiyan don sun kula cewa sune zasuyi wanan tafiyan donsune ya cancanci sujeshi sai gashi waisu gwaggo Aminane zasu tafi irinwuce an wajen dasu ya dace ace sunje. Ranan kuwa suka shirya zuwa lagos inda a can zasu hadu dasu umma su wuce a tare dasu zuwa Hong Kong din su samemu kamar yadda aka tsara tafiyan. Akwai kanwar mahaifiyarsu da kuma wata dake zaman gwaggon shi daya da zasu tafi tare nan ma gida maiduguri an kashe kudi sosai ma anan don taro zasuyi tankar maijego da yaran suna kasan. Ana gobe zasuyi taron suna Maiduguri hjy falmata ta shirya da tawaganta suka bar kasan ta koma inda ta fito ko maigidan baisan zata koma wanan lokacin