← Book details Ana Dara Ga Dare Yayi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 20 OF 337

Sashe 20

Ana Dara Ga Dare Yayi Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Dagani har umma a lokaci daya muka mike zaune don firgita saboda yadda aka bugo kofan dakin da karfi aka shigo.
Su ukune ko wanin su yana saye da bakaken kaya sai bin mu sukeyi da kallo kamar yadda muma muke binsu da kallon saidai bamu ganin fuskokin su a baiyane.
A cikin karfin hali umma tace masu una de look for somebody here ba magana ko daya a cikin su illar takawan da na tsakiyan yayi zuwa bakin gadon da Amar yake kwance da karin ruwa ya tsaya yana kallon yaron kafin ya kai hannun shi saman ledan ruwan ya dan duba.
Duban yan uwan yayi kafin su tako zuwa gadon su dan dubashi suyi wani magana duk muna binsu da kallo da mamakin hakan a cikin zuciyar mu.
Can dayan ya dago yana fadin mama ur son will be fine very soon my oga say he go live d town today.
May u colect dis money manage am with ur pikins take care of dem yana mikowa mama kudi a cikin wani bakin leda.
Umma ta kalli hannun shi da kudin kafin ta dago tace dashi tellam say me no want his money naw.
D tin wen he do for us is ok for us now, make he cary his money go, Allah will reward him for dat.
Ai mun gode ko hakan wallahi Allah dai ya saka da alherin sa ta karasa fadi da hausa tana zama a bakin gadon don ganin ba cutar damu sukazo ba.
So u servi hausa ma self ki karbi kudin nan don na baki wanan ba komai bane a wuri nayi niyar taimaka maku ne don jin halin rayuwan da kuke ciki a gida a bakin mutanen gidan.
Don haka don Allah ku karbi kufin nan kiyiwa yaran amfani dashi Allah ya sada mu da alherin sa don ba lalai bane mu kara haduwa kuma saidai yarana zasu dinga duba ku lokaci lokaci.
A gadarance gashi duk da bakaken kayane sai kyali sukeyi kayan sun hade da fatan jikin shi chakulete colour .
Yana da tsayi gami da kirji mai fadi kiran zaki gashi da dan tsayi da alaman jiki kuma don Allah ya bashi kyau kira ga zati a gaban duk wanda ya tsaya.
Ga wani saje da mazan zamanin nake ajewa yanzu da suke kira da one million a fuskan shi ya kara masa kyau.
Basai ya fada ba duk wanda ya ganshi yasan shi din wani ko acikin dubu don zan iya cewa komai ya hada ban sanarwa na imani ba da bangani a fili amma kan kudi sun riga girma yawa a wurin nan.
Duk maganan da yakeyi da umman mu idona yana a kansa ina karewa halittan Allah kallo don yawan kallona har saida na gano fuskan shi na ainihi duk yana ganin shi ya rufe don a duke nake har lokacin don haka zan iya ganin hakan daga kasa.
Don da nasan kiyasta shekaru a lokacin wanan ba zaifi ashirin da wani abu ba a duniya don yarone a iya sanin matasan legos da nayi ko tsoho mai hurhura yana dabi,un yara sai in kira wanan din da yaro.
Na sake fadi a raina kyau da kudi ga kwaliya da kwarjini duk Allah ya tarawa bawan Allah nan sai dai kuma ya kaza don miskilin karshe ne shi.
Da gani ga girman kai nan a fili da jiji da kai da yake nunawa a fili yana nuna shi din wani ne a gaban kowa tun ganin farko da nayi masa.
Har ya juya ya fara tafiya bayan ya umurci a ajewa umma kudin a gefen ta a inda take zaune ta zuba masu ido cikin tsoro da fargaban su don basu da tabas.
Kowa yayi shiru umma na ganin sun soma tafiya tace na rokeka kada ka zama min sabon matsala a rayuwa .
Wani irin juyowa yayi har zuwa gaban umma din ya dan kalleta ya sake dan murmushi kafin yace.
Mama nayi domin Allah ne don abinda kike tunane ba hali mu bane iyaka mu muna neman na kan mu ne da zufan mu.
Idan kuma munga mai bukata mu taimaka masa don ya sakawa harkan mu albarka don gaba Allah ya kawo muna sa,a a rayuwa.
Me yuyuwa daga yau na fada maki kila ba zaki sake haduwa da muba balle har wani abu ya biyu baya na asha don haka ki saki ranki niba mugu bane kamar yadda kike zato.
A lokacin ya dan cire hulan daya rufo a kanshi ya kalleta da kyau tare da hada hannayenshi wuri daya kamar mai rokon gafara kana yayi wani abu kamar bissalam da hannu tare da dan rankwafawa daga haka suka juya suka ffice sauran suka bi bayan shi da sauri.
Ina ganin haka na mike da sauri na rufo kofan dakin tare da saka sakata na dawo inda umma tayi mutuwar zaune don ko motsi bata iya yi ba har lokacin sai bin kofa takeyi da kallo inda suka fita.
Umma idan baki yarda dasu ba ki kawo kudin nan yanzu inbi bayan su dashi duk inda suka shiga a garin nan.
Sai lokacin umma tayi wanin irin ajiyan zuciya tare da kallona tana fasin ke din Sahiba kike fatan in barki kibi wa yan nan da suka tsaya gabana kamar mala,ikun duniya.
Maza ki samu wuri ki koma ki kwanta saidai muyi adduan nufin su yazama alheri a garemu amma ba zan barki ki bi bayan wa yanda bansan asalinsu ba ko daga ina suka fito.
Umurnin umma din nabi cike da fargaba a zuciyana na samu wuri na kwanta a makure ina faman tunane sai gizo fuskan shi da ya tsaya min arai ya ke mun a lokacin.
Ina ganin kyawawan maza ban taba ganun mai kyau irin nasa ba a rayuwana har barci ya daukeni a hakan.
Washe gari nikan na makara da sallah saida umma ta tayar dani a gurguje nayi sallah namike ina gaida umma da kwana kafin na fara tattara kayan da muka dan bata na fita dasu wurin wankewa .
Tunawa nayi dana hjy na shiga dakin da sallama na samesu a ciki na gaida su a cikin ladabi nake tambayan mai jiki suka amsa da sauki
Nake fadi nazo na kwashi kayan na wanke masu ne don zan tafi na wanko namu a famfo.
Allah sarki yar albarka wallahi keda ai jiya an tafi dasu gida a wanke a can saidai cup din nan da suka sha tea da dare dashi.
Na duka na kwasa na fita yau kan ban dade ba son yanayin dana tashi cikin sa ba dadi don haka ban kula kowa wirin ba nayi abinda ya kaini na bar wurin.
Chapter 20 · 0% Book details