Sashe 333
Ana Dara Ga Dare Yayi Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read
ba. Sai labari ya samu cewa sun tafi ita da diyanta da kannenta da sukazo gida yin babban sallah kamar yadda suka saba zuwa duk shekara a wanan lokacin sukan yi ziyara su gana da yan uwa suyi masu alheri . Sai gashi wanan karon haihuwana ya hanashi tsayawa don tun washe garin da yamma ya koma ya barsu a nan su. Sai gashi taji cewa itama hjyr tasa ta juyo ta dawo turai a wanan lokacin gashi ba zaman lafiya tsakanin shi da ita tun lokacin dayayi aure suke kwasan fitina da ita sai hakkuri da juna sukeyi tsakanin su. Wanan yasa ko zancen haihuwa sai a waya ya kira ya fada mata ya kuma kashe wayan shi gudun kada bacin rai ya biyo baya tsakanin su. Sun iso lafiya sun samemu kuma lafiya inda yara sukaci sunan mohammad da Ahmed sunan mahaifina da nasa zuwan su umma yasa yanzu na samu hutu sosai banda aiki sai barci ko wani lokaci. Haka yasa jikina yayi kyau sosai da alaman jegon ga karbi jikina idan ka shigo ba zaks taba cewa nice na haihu ba sai idan ka samu ina ba yaran nono. Yanzu ma barci nake tun safe dana shige daki bayan mun gama karyawa sai wajajen karfe biyu gwaggo Amina ta tayar dani in basu nono shine fitowana lokacin. Kowa na falon zaune suna hira mukaji ana nocking Fatimace ta fita duba ko waye muryan hjy falmatane a kofan take fadin kauce ki ban wuri don Allah. Fatima ta kauce da sauri ta basu wuri ta tun karo inda muke zaune din ni inabawa yara nono a cikin yare na fara fadin su boye min yaron dake hannun gwaggo kudidi tun kan ta karaso haka akayi . Suna mata sannu da zuwa ko kallon arziki basu samu ba sai kokarin shigewa takeyi zuwa dakin shi suna kallon ikon Allah. Suka shige sai gata ta dawo tana tafiya takalmanta na basa sauti tun kan ta karaso take fadin (ke ina makulin wancan part din ?. Ban kallo inda take ba naci gaba da abinda nakeyi ke bakya jin ina magana ne ta kara takowa zuwa har inda nake zaune a cikin wani isa da takama. Mrs may i know who are ? Kin shigo gida bakiwa kowa magana ba yanzu kuma kina tambayana key din gida haka kai tsaye ? Itama din kallon mamaki take min kafin tace samun wuri ni kike tambaya ko wa nake nace kwarai kuwa son banga alaman hankali ba a tare dake. Naso baki girmanki na shekarun ki da matsayinki na babba a gareni gidan miji amma naga sam ke baki san girman na gaba dake ba balle harni mm a girmamaki. Don haka ba zan bada key din gidana ba don bai fada min cewa zaki zo nan ba nima kuma ba zuwa inda kike zanyi ba don haka ki fice min daga gida yanzun nan kafin rayuka su baci. Au ashe har gidan ya zama naki ko ban sani ba ko dan yaran da kike takama kin kwaso sun zama naki a yanzu kike son ki fara mallake gidan ? Zaki iya mayar dasu inda na kwaso su ai tunda shine bakin cikin ki dama kada na haihu da mijinki gashi kuma na haihu din kamar yadda baki so haka ba. Haba Falmata ana zaune kalau zaki zowa yarinya da fitina haka tana fama da jegon ta kanwar mahaifiyar shi ta fada . Kune baku sani ba don babu mai labarin cikin wanan yar iskan saijin haihuwa kawai akayi don ta rainawa mutane hankali taje gidan marayu ta dauko rainon diya . Salati matar ta saka tare da fadin falmata sherin har yakai nan kina son batawa yara suna ga banza kiwa Allah ki bar wanan sherin tun bai fita ba . Yara kowa yasan na mijinkine don gasu kamar kakinshi wurin kama har wanan cindon dake dan yatsan shi duk basu ragoshi ba a wurin kama. In ma wani abu ya kawoki sai ki zauna har maigidan ya dawo saiku yita a gabab shi zaifi amma haka ba daidai bane gaskiya. Zama kan ai dole inyi a gidan nan har na kare kwanakin da zanyi kasan nan amma saina tonawa wanan yar iskan asiri kafin in wuce. Bako a cikin gidan nan ba don ko yini bakya yi a cikin gidan yau balle kwana sai ta jefo min wani kallo nace kwarai kuwa In kina musu ne mu zuba dake ga key nan na mika mata ina kallon ta.