← Book details Ana Dara Ga Dare Yayi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 323 OF 337

Sashe 323

Ana Dara Ga Dare Yayi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Komawa tayi ta zauna tana binsu da kallo basu zo inda muke zaune ba sai yawo suka fara a falon suna tabe tabe da yatsune fuska haka yasa nasan ba arziki ya kawosu gidan ba lokacin. Har zuwa lokacin da suka nufi dakunan kwanan dake cikin gidan suna iskanci in ka debe daya daga cikin su da taja ta tsaya a bayan su . Juyawa nayi na kalli fatima nace go and close the door for me, ki kawo min key nan ta juyo da sauri tana kallona bansan meta gani a kwayan idona ba ta mike da sauri ta wucesu zuwa kofan tayi abinda nace tayi din jikinta sai kaduwa yakeyi a lokacin don tsoro. Suna wani tafiyan isa da takama suna harare harare suka karaso tsakiyan falon suka tsaya. Ganin hakan yasa na mike tsaye remote na dauka na rage karan tv dake aiki kallona sukayi tare da fadin ehh lalai samun wuri anga komai abanza dole ayi yadda akeso ba a saba da ganin daula haka ba ba. Dan murmushi na sake a fuskana ina dan karkada farin kafana da duk rabinshi yana waje sai takalman zaman gida na roba shima pink kalar wandon dake jikina anyi mai addo daga sama kamar gashi an rufeshi. Dama kwadayin arzikin ne ya kawota cin banza saidai yarinya kin tabka babban kuskure da kika yarda kika shigo gidan mijin yar uwan mu da sunan kishi da ita. Ohh Realy na kalleta na fada naci gaba da fadin ita yar uwar taku diyar waye a kasan nan da ba,a shiga gidan mijinta itama din ba shiga tayiba. Ji wanan banza muna fadi kina fadi ke din yar waye diyar bararon daji kawai kilama rufa rufa akaiwa mutane ba a san asalin ubanki ba. Keko taga arziki ido ya rufe yanzu anzo aci banza dole ta dauka daidai take da kowa tanzu banza kawai masu bin arziki da gudu kinyi kuskure wallahi. Har lokacin wani murmushi na sauke tare da fadin No warder naga kowa da kowa naku kun maida gidan mijin yarku gidan ubaku har uwarku da kowa naku kun dawo kun tare a gidan mutumi kun hanashi shakat a rayuwanshi. Kun hana danginshi su morewa dan uwansu kun hana kowa nasa ya rabeshi yaji dadin a innuwarshi yanzun kuma kuna bakin ciki da hassada nazo nima naci arzikin nasa. Koda yake talauci yana saka hauka ba mamaki ga irin rayuwan da kukeyi na dabbobi ko wani dabban ma yafiku tunane da sanin ya kamata don dabba baya abinda kukeyi harda yar taku jaka. Ehh lalaima yarinya wanan kin tarowa kanki much yau, dama gargadi kawai mukazo muyi maki ashe kina takama da karamin barikinki a hakan kema. Kinyi gaskiya wanan dama nasan karamar yar iskace ta lafene kawai don ta samu shiga dayar ta fada daga gefe tana wani tafa hannu kamar taga abin mamaki har lokacin duk basu farga da mun kule kofa ba fatima da suwaiba mai aikina suna tsaye daga kofa a cikin tsoron abinda zai faru. Amma gaskiya kunsan in munyi wani abinda ba daidai ba a gidan nan ran ya mukhatar zai baci damu wallahi don Allah ku bari mu fita lafiya yadda muka shigo karamar daga cikinsu ta fada a dan tsorace ta kara da fadi a cikin yare Gila gila. Ayyah sorry sister ki barsu suyi abinda suka zoyi zasu samu duk kala abinda suka zo dashi gidanan a yau na fada sai ta tsakiyan datafi fitsara tayi wani shewa tareda tafi tana kara matsowa inda nake tsaye. Kamar ban san me take ba a lokacin ina kallon biyun dake gabana a lokacin tana zuwa kusa dani hannu na daga saijin saukan mari tayi kawai a kumatun ta saida ta sake wani kara da karfin Allah lokaci guda. Kafin suyi wani abu nasa kafa na tadiyo babban nasu sai gata a kasa ta buga goshi da baki a saman ties ya fara fitar da jini lokaci guda. Dayan tayo kaina kafin ai haka tayi kasa na bita na haye muka fara fadan mata biyun sukayo kaina duk da ina saman yar uwan ban kyalesu ba suma don ina kai masu nashi da shuri duk wace na samu sai dayan dake tsaye tana kurma ihu duk abinda muke wayana a kunne yake yana dauka tunda nayi saitin shi lokacin da suka shigo suka fara iskanci. Danbe sosai nayi dasu duka hudun lokaci guda amma Allah bai basu galaba a kaina ba lokacin jin wani irin karfi nayi yazo min sai bugun mai uwa da wabi nake kai masu a lokacin. Dukan kofa da akeyine yasa muka dan dakata saboda na sheda muryan sister ashe Fatima ce ra tura mata text massage suzo ba lafiya gasu sun kawo muna attack a gida. Duk yadda akayi na kyalesu na kasa sai binsu nakeyi muka fara zagayen gida cikin tashin hankali an rasa wanda zai rabamu a lokacin . Har yakai sun nufi wurin kofan nabisu haukace suka fara ihu a cikin tashin hankali suna neman taimako ranan kan basu ba duk wanda ke wajen yayi mamakin ya akayi na iya masu dukan wulakaci haka su duka uku. Dabara Fatima tayi ta samu bude kofan har aka samu shigowa gidan da kyar da bani aka samu kwatansu a hannu na da kyar aka jani zuwa dakina aka samu fita dasu. Sai kuma ga yar nasu hjy Falmata tazo wai a barta tashiga tayi maganina don me zanyiwa kannenta haka kuma ace wai mutum daya tayi masu wanan dukan haka kai ina gaskiya da sake. Kafin ace hakan har labari ya fara karada gari an fara fadin abinda ya faru ana kari a kai ga kuma video da fatima ta turawa Sister suka sake a median ya fara yawo nan zancen ya karade ko ina ko lokaci guda. Hankali a tashe ya shirya zuwa Nigeria sai hjyn su ta dakatar dashi akan kada yazo don in yazo ba za,ayi mai dadi ba wanan yasa ya fasa zuwa saidai munyi waya dashi ya bani hakkuri kan abinda ya faru. Tare da jamin kunne kan kada in kara irin haka da kowa na bari idan sunzo sai na kirashi yasan abinda zaiyi shi ko yanzun ma ba zai kyalesu ba. A haka dai har maganan yazo ya lafa bayan tayi barazanan ta da borin sai tayi karana kan wanan matsalan shi kuma da taji yace tana karana daga can ta tafi gidan su. Naje gidan mu fa kace baban yusura yace kwarai ki tafi gidan ku daga kotun sukai dan sa,insa dashi a karshe yace idan bata dawo ba ta zauna kuma kada ta dawo mai tare dasu gidan shi gaba dayan su. Tashin hankali da jidalin ya karu ta dauki haka da wasa suma sai hankalinsu ya tashi sosai da jin abinda ya fada nan dayan take fadin aina fada maku kada kuje gidan da fitina kukace aje a saka mata tsoron a zuciya. Yanzun ga abinda ya biyo baya mu din ai bamu san haka take yar daba ba da bamuje ba sun rasa yadda zasuyi gashi itama yar uwan nasu ta fara juya masu baya a yanzu . Don yarsu hafsat data zaunar da ita ta lurar da ita kuskuren da suka tafka daga ita har yan uwan nasu takuma bata shawara kan su yarda girman kai suje gidan da sunan sunzo ba hjy hakkuri kana su suce zuwa har gidana daga nan. Da farko sunso suyi mussun hakan har ita hjy falmata din amma kowa yace hakan dai zasuyi ai aidukawa wada ba rage tsawo bane ga mutum a faki gaba dani dasu ai yanzu aka fara wasan. Da wanan shawaran suka bi sai gasu har gidan da misalin karfe biyar na yamma a lokacin tare da ita hjy hafsat din data kawo su saidai ba hjy Falmata a cikin su. Wani tasha na yarbawa da nake bin season dinsu tun a tv duk ranan laraba ina zaune a falon gidan nake kallona hankali kwace sai ga sun shigo anyi nocking suwaiba ta nufi kofa ta duba ta samu ai sune sukazo. Don dama mun sanda zuwansu shiya kirani sister kuma ta kira duk sun sheda muna zuwan su ya fada zasu zo su ban hakkuri ne kan abinda ya faru tsakanin mu. Don haka banyi wani abu na nuna masu rashin hankali ba don mutuncin matan da suka shigo dasu gidan a lokacin muka gaisa dasu cikin mutunci da girmanawa. Ta fara koro magana na katseta da fadin do me, i do you so no base me i no wan wahala gyare . Duk kallona sukayi na nuna masu cewa banda tsoro ko fargaban fitina koda da namijine don haka fada dashi na bude ido da ban iya ba ban amsa suna yar geto ba a yanzu. Ke na nuna dayan ai kafin kuzo nan sai da friend dinki ta fada maki cewa kada kizo amma kika nuna kinfi karfin barin fada maku ko sister din ku aiken da tayo min yana nan dawowa gareta indai ni sahiba ce bata san ko wacece ni ba ta barni a inda ta gani kome tayi zai koma a kantane. Allah dai ya sauwaka yar nasu ta fada tare da kara bani hakkuri na nuna ai komai ya wuce a wuri suka fita bayan sunyi muna sallama. Kallon naji ta fita raina a lokacin don haka na mike na shiga dakina ban kara fitowa ba sai washe gari don ba yadda fatima batayi dani ba kan na fito naci wani abu naki fitowa a ranan. Haka hjy Falmata ta shirya ta koma inda ta fito tare da tawaganta da sukazo bayan taga duk wani abinda take ganin zatayi wanda zai min katanga da maigida. Data sani ta barwa Allah idan muka zulunce ta sai Allah ya isar mata tun a nan duniya amma ta kasa hakkuri ta barwa Allah lamarin tayi ta addua a gare shi. Sai ubangiji ya dorata a kaina idan nazo mata da wani cuta ko ha,inci a cikin rayuwana idan kuma babushi sai yasa mu zauna lafiya a tsakanin mu. Amma gagawa aikin dana sanine daga baya idan kana da rabo a wajen ubangijin ka sai kayi daka sani baka kaucewa Allah ba. Sai labarin tafiyansu naji a bakin Fatima ita da take waya
Chapter 323 · 0% Book details