← Book details Ana Dara Ga Dare Yayi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 212 OF 337

Sashe 212

Ana Dara Ga Dare Yayi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

ALAJA macece tsayayya mai kiran karfi don garsakace yadda malam bahaushe ke fadin mace mai irin zatin ta zamu iyacewa kuma tsayin nata yayi mata kyau sosai gata farace ita jajir ga jiki daidai tsayinta sai abin ya hade ya bada ma,ana a gareta. Ta karaso wurin tana fadin a a sha,aban wai kayi waya da Walida kaji ya jikin nata kuwa a yadda yake zaune ya mike kafafun shi saman dan stol dake gaban shi. Takai zaune a kusa dashi jikin ta yana gugan nashi tana fadin ya kamata ace la kirata kaji yaya ta kara ji da jikin nata ai don kasan da tana nan a tare damu yanzu haka dukda mahaifiyarta tace zamu hadu dasu can england din. A cikin harshen larabci yayi mata magana ba tare daya dago kai ga abinda yakeyi ba sai ita Alajan ta juyo tana dan murmushi take fadin. Wai laifine ka kira matar da zaka aura kaji lafiyanta tunda da ita muka shirya wanan tafiyan rashin lafiya ya kamata . Murmushi Allah ya ban ikon sakewa ina dan kallon shi jin an ambaci aure a gareshi nace sir gaskiya maama ta fada yana da kyau kakira kaji lafiyan ta. Da mamaki ya dago yana kallona kafin yace I don't no who she is talking for kin dai san bansan wacece ba kuke zance a kanta ba na fada maku ba wanan zancen a zuciyana yanzu. Don haka ummi ki bar zancen nan tun wuri ya karasa fada yana tanke fuskan shi a cikin harshen larabci da bama ji. Dacewan hakan mama ta gani a gareka mune yanzu zamuyi hakan kai muna fada mutum musulmi bai cika cikkaken mutum a idon jama, a sai yana da iyali a gida. Da kyau yata haka nake son ki da fadin gaskiya koda yaushe gara dai ku fada mai ta fada a cikin yanayin damuwa a fuskan ta lokaci guda. Na rasa meye hakan yakeyi kai ba musulmi bane da baka yarda da kaddara Sha,aban nima ai mijina ya mutu danayi hakkuri ba gaku ina kalko ba to kai waye zaka kalla ya debema kewa a rayuwa kowa fa yana son barin baya a duniya ko banza zasu tuna dakai suyi ma addua. Wana maganan da mahaifiyar shi keyi yasa jikin kowan mu yayi sanyi lokaci guda karshe sai mikewa yayi ya barmu mu uku zaune fita yayi zuwa wajen wurin yana shan iska rike da cup din lemu a hannun shi. Felix har yanzu na kasa samun kan yaron nan na dauka zaiyi maraba da wanan dun da muka zabar mashi don yarinyar akwai kyau ga ilimi sanan gata yar manyan mutane a can Nageria din. Nan Felix din yai magana yana fadun mommy kin fa san halin ogana kan wanan magana ko wancan ma kece kika matsa sosai akayi shi a lokacin. Har kuma rasuwan ta bawai wani shiri bane sosai a tsakanin don kin san irin rayuwanta baiyi daidai da nasa ba kinfi kowa sanin haka. Kai kabar wanan zancen don wacan ta riga data rasu ko yanzu wata nake son na nema mashi yana kuma bultse min akan zancen gashi na riga dana fadawa mahaifiyar yarinyar kuma sun yarda da hakan a yanzu. Don haka kuyi min kokarin hakan gareshi ku biyun nan tana nuna mu da hannunta naga ke ya yarda dake sosai a rayuwan shi har wanan abin yana ban mamaki. Yadda ya amince dake haka kina mace koda yake hakan ba abin mamaki bane ga wanda ya sanki kuma yasan kina tare da juju zaki iya juya kowa a yadda kike so. Saidai ina ina rokon ki da kada ki shiga cikin rayuwan dana don Allah duk abinda zakuyi ya tsaya iya aikine kawai kamar yadda da farko shine ya hada ku ta kare tana hada hannayen ta a wuri daya alaman rokona. Duk girma da nauyin Alaja da nakeji sai naji lokaci daya ta zube min idona ya rufe na kirata da sunan ta da Alaja me zancenki ke nufi a kaina yanzu ido babu nauyin ta ko tsoro a lokacin itama din kallon mamaki ta bini dashi a idonta. Ni sahiba ba dan ki ba duk wani da namiji dake duniyan nan ban taba jin wani abu so ba ga kowa don ban taba soyayya da kowa ba a rayuwana balle na fara akan danki . Na mike daga inda nake ina fadin idan ma har zuciyar ki ko wani ya fada maki haka yai maki karya don ni yanzu ba wanan bane a gabana ba. Aikine da danki daga yau din nan na daina tunda har kike zargin wani abu ga hakan ba komai tsakanina da oga sai zalla biyayya da mutunci iri wanda shi ya nuna min hakan. Kada kiyi zaton aiki da nakeyi a katshin danki zai baki daman hasko wani zaton dani koshi bamu tabayi a zukatan mu ba akwai dubun shi da suke jiran hakan ni ba matsalana bane a wurina aikine ya hadamu shi kuma nakeyi dashi ko yanzu din da kika ganmu a zaune. Ina rike mutum ne yadda ya rikeni tun farko danki ya daukeni kamar yar uwanshi nima hakan yasa na daukeshi hakan kamar yadda shima ya daukeni din. Don haka ki kwantar da hankalin ki kije kai tsaye ki nemawa danki yar shugaban kasan duniya wanan bai shafeni ba ni. Kuma ki sani daga wanan ranan komai ya kare a tsakanin mu dashi na fada ina mikewa tsaye fuuu nabar wurin ina jin Felix na kiran sunana ban tsaya naji abinda yake son fada min ba lokacin. Sai muryan ogan naji yan fadin meke faruwane felix mai kukai matane hakane wai ? Sai kuma ya sake juyowa rai bace yana fuskantar su kafin kuma ya juyo da sauri yakai kallon shi inda nake ina kokarin fita daga inda muke tare dasu din wurin da suka gyace mu din . Wani tsawa ya dakawa Felix a kan ya bini ya dakatar dani kada in bace a cikin garin mutane nashi ya sameshi. Na fada maki gada kiyi wa yarinyar nan komai idan sunzo garin nan ummi saida kikai mata wani zance a yanzu ashe ya fada rai bace yana bin bayan felix din. Sun kai su goma ko fiye da goma a police station din tun safe suke wurin a tsaye su shiga su fita sun kasa yin komai daya dace a wurin don suna neman bellin shine a ranan. Bayan ya kwana har biyu a hannun hukuma nan garin Abuja wanda da kyat suka iya nemo inda yake lokacin kafin su fara wanan shige da ficen na neman bellin shi bisa jagorancin babban abokin shi wanda shi din dan majalisnane a lokacin wanda yaci zabe da taimakon Alh Nuhu din. Sai fada yake da yan kakin wurin kan basu san matsayin shi bane ko basu shedashi bani suke mai yawo da hankali. Dan sandan ya dubeshi cikin girmamawa yana fadin wanan case din Alh daga sama take don haka sai kun koma can kun gyaro don mu kamar ajiyan shi aka bamu nan ai. Nan ya matsawa dan sandan yake fada mai ai case din daga office din sakataren gwaunati ya fito don haka su koma a gyaro komai. Fitowan shi office din yasa sukayo ruuu a kanshi don suji halinda ake ciki, saboda shi kadai ya samu ganin IG din lokacin ko shi dun kuma don mukamin shi da yazo dashine aka barshi ya shiga. A daidai lokacin kuma sauran yan uwanshi Alh Nuhu din da suka biyo mota daga kaduna zuwa abuja suka iso wirin a gajiye. Basu samu labari mai dadi ba a wurin don haka hankalin su sai ya kara tashi fada sosai sukeyi suna fadin haka kawai za a kawo mutum a tsare shi kan kudi a ina zai samu kudin da zai biya yana daure ? Kallon su baffa Hamza yayi a cikin takaici kafin yace nifa na dauka wanan abin anyishine da wata manufa don yarinyar da tayi aikin files din nan harta zakulo su yaya din ba wata bace yar mu ce yar dan uwan mu kuma na uba daya wanda ya rasu shekarun baya . Wani kallo suka jefa mai kafin dayan Alhazawan yace yar kufa kace malam Hamza yana tambaya a cikin mamaki tare da kallon baffah hamza din da yai magana. Kai ya gyada yace kwarai don kusanma ba tantama nakeyi ba don itace tazo daga lagos tayi wanan aikin har hakan ya faru. Yar waye ke nan Alh gyade ya dan tako da sandan da yake dogarawa ya samu ya dan shiga mutane yace yar waye ke nan kake nufi wai ? Baffa hamza din yace yarinyar nan dai yar wurin yaya sambo marigayi data baiyana wancan satin ai itace ashe tayi wanan aikin a company sha,aban din. Wai kana nufin cewa wanan yar da gaske yar samboce ita toshi da namijin fa to ? Shima kwarai danshine don ance kamar su daya da yaron sosai yaron ya kwaso mahaifin shi fiye da ita macen ya fada yana gyada kai. Kai wanan abinda daure kai yake gaskiya a lokacin wani daga cikin abokan su yake fadin tazo da wani manufa ke nan yanzu dai ? Kwarai ba kadan ba sanan tayi tafiya zuwa england sai nan da sati uku zasu dawo kasan nan a yadda mukaji. Duk Alh yana tsare har wanan lokacin sai lokacin data dawo za a jirata ko me ? Shi muke kokari yanzu mu sameta ai saidai wayan ta baya shiga don yaron nan Abubakar da dan wurin harira suna da layin ta su. Kaji matsala babba ke nan yanzu bullowan wanan yarinyar da uwarta har kuma gada namiji ya fada a tsorace hankalin shi a tashe. Meye matsala don sun bayana a yanzu din tunda dama dauka ake sun mutu ne kuma ashe suna raye ba shike nan yanzu abinda ya rage kawai mu jawosu zuwa cikin mu ai shike nan. Shike nan fa kace hamza kai hamza nafa gano me kake nufi daka matsa mutanen nan yanzu su shigo cikin mu bayan wofinta kansu da sukayi a baya can. Ba komai kake kokarin nunawa ba gare mu yanzu sai zalla bakin ciki da jin haushi irin na yan uba da kake kokarin nuna muna. Haba Alh gyade wanan
Chapter 212 · 0% Book details