← Book details Ana Dara Ga Dare Yayi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 178 OF 337

Sashe 178

Ana Dara Ga Dare Yayi Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Bana bada magani amma zan iya kallon ki in abin ya biyo a kaina zan fada maki komai game dake kuma hankalina bai bace a tare dani ba.) In takaice maki dai ranan bamu daga a surin ba saiga manaja mai tafiyan sati daya ya dawo garin ashe baije ko ina ba yana garin dama. Wani bakine mai dan jiki da tsawo sajen fuskan shi yana gauraye da baki da fari da tsaga uku uku a bakin sa. Yo don me zasu shigo muna babu sanarwa haka kawai suce sunzo aiki damu ana ce masa yallabai kayi hakkuri a bisu a sannu tunda sun zo ko ba abinda zamuyi yanzu. Saina ci musu mutumci na nuna masu nan arewane ba ai muna kutse haka shi idan ba yana mutumin kawai ba bazai nemu mu sulhunta a tsakanin mu ba. Sai kawai ya turo muna comitten bincike haka suzo su wani cika muna wuri da guntun turancin su iya wuya don Allah ku bari in shiga muyita yanzu dasu yana fadin haka ya fado offince din inda muke kai tsaye. Kowa daga inda yake zaune yana aiki suka dago kai suna kallon shi Bellone cikin wanda muka dauko daga kaduna yake fadin malam lafiya dai. Bin kowan mu da kallo yayi kafin yace ance kuna nemana kuma kun shigo baku fada muna zuwan ku ba kun fara aiki bada masaniya ta ba? Who is he na tambaya ba tare dana dago kai daga abinda nakeyi a cikin naurata ba yace iam the chairman of this place. And then so what na fada idona kan laptop din na dago ina mikowa na kusa dani takarda yana tsaye ya kura min ido a cikin mamaki. You can go now mr chairman you are not invet here ka barmu muyi aikin daya kawo mu mubaka wurin ka daga inda Adnan yake ya taso zuwa inda nake zaune yana nuna min abu a computer shi nayi masa bayanin komai ke ciki. Ina kokarin dukar da kaina inci gaba da aikinane Felix ya jefo min tambaya na bashi amsa duk yana tsaye kamar an dasa shi a wurin ya kasa fita. Ku bashi kujera ya zauna wanan tsayin yayi yawa haka jin haka ya bashi daman fita yana fadin yana zuwa ya fice da sauri. A kano suna jiran fitowa mu yau su sha kallo kamar yadda Alh ya fada masu cewa zaiyi maganin mu su bari suga abinda zai faru damu a kwana biyu ras. Suna zaman saka idon ganin fitowan mu shiru har sha dayan rana babu alaman mu sai suka dauka ai abinda akace zai faru damu din ne yafaru din. Suna mayar da zance ne kiran chairman din can ya shigo masu a wayan yana sanar dasu muna wurin su munyi kaca kaca muna musu binciken kwakwaf. Yan iska a can suka dura maku yau kuma ashe akwai ta kuwa da wanan shu,uman yarinyar mai kwakwaf da isa. Sundan jima suka kashe wayan suna murnan can kuma iskan namu ya kadamu ke nan mun gama dasu ke nan ashe dama me zamu iya dasu . Abinda basu sani ba shine Alh na can ya shiga wani hali don ya kira bokan su ya fada mashi komai yace ya bari zai kirashi idan ya bincika. Ya binka din ya kumaga abinda bakin sa bai iya fadawa Alh kada su raina mashi wayau ga aikin shi abincin shi ya dakile a wurin su. Yasa yace dasu gaskiya subi aikin nan a sannu don mutanen nan sun wuce yadda ake tsamani don me basu fada mai da wuri ba su san abinda zasuyi a kai. Yanzu aikin gagawa ba zaiyi tasiri akan su ba dole sai an dan bada lokaci kafin a samu yadda ake son samu. Su bashi shanu ayi yanka da bakaken busurai guda uku da kudin da za a sai turaren da za ai aikin dashi yace zai aiko masa zuwa yamma. Ankan sayo shanu wai a hanya haka kawai shanun ya mutu a cikin mota haka kawai ba a san me ya sameshi ba. Jin wanan labarin ya sa Alh shiga cikin wani yanayi na tashin hankalin don ba kudin shi bane shi kadai shi yanzu me zai fadawa sauran abokan harkan nasa akan haka. Bawai shanun yafi karfin shi bane kawai dai bakin haline irin na wasu don yana ganin idan ya sai wani shanun kamar shi kadai ke nan ya biya masu aikin amma yasan abinda zaiyi . Adaren ne kuma yayi mafalki da wata fitsitsiyar yarinya a gaban shi tana bashi warning kan abinda suke shirin aikatawa din a cikin tsawatawa ya ganta tana mashi kashedi. Hannu ya daga yakai mata mari takama hannin wai har hammun shi ya kare a cikin ya falka a firgice yana maida numfashi lokacin ne kuma yaji baya iya daga hannun da yaga an rike masa din a cikkn mafalkin . Duk yadda yaso ya motsa hannun abu ya kiya gareshi tun yanayi shi kadai dole ya bidi taimakon iyalin shi kan hakan. Abu wasa wasa har gari ya waye aka nemo mai duba kariya yazo har gida ya duba yaja masa hannu ai sai abin ya karu mai fiya da yadda yakeji da farko ma. Dole aka danganta shi da asibiti can ma sunyi iya duban su basu gane komai ba suka saka mashi ruwa da alluran kashe zafi don ya samu dan sassauci amma ina . Awanan halinne Oga Bala ya kirashi don ya sheda mai halinda ake ciki babban dan Alh din ya dauki waya yana masa bayani halin da mahaifin nasu yake ciki. Takawa yayi ya kira chairman da manager ya fada masu abinda ke faruwa da Alh din ranan kallon juna sukayi kafin shi oga balan ya basu shawara cewa su isa asibitin suga halinda yake ciki daga can suyi masa bayanin komai. Saidai sunje din abinda idon su ya gane masu babu dadi ga Alh dole sukai mashi sannu suka kama bakin su suka tafi. A hanyane manaja ke fadin anya anya kuwa ba wanan dalilin bane ya jawowa Alh wanan fitinan karo da yarbawa fa ba banza bane. Kai ina sam Alh fa da kuke gani shima shegen kanshine na gaske indai wurin wanan harkan ne yaci gaba da cika bakin sa kan Alh suna sauraren shi. Yanzun mommy wanan abinda kukewa gwaggo baku sakata a hanya ba sai biye mata kuna dulmiyewa shine daidai mommu ku baku sakata a hanya maidaidaiciya ba. Me kuma mukayi don kawai mun je nuna mata farin cikin mu shine laifi kuma yanzu ? Ok kiyi hakkuri mommy idan ranki ya baci amma ni gaskiya na fada maku ai don kawai yana shi kadai sai a diga yin wanan abin haka fissabilillah ? Tau ubana nida abu ke samuna su zo min din fa shiba laifi bane yin hakan ko tunda ni akaiwa ko na fada ma kadaina raina min wayau irin haka. Don ko banza kasan dai hari yar uwatace kuma tare muka tashi da ita kamar kawaye sai yanzu kuma kan danta in kita. Ya mike yana fadin zan tafi dama kayan yarinyar nan da nayi odane suka iso nazo in fadawa daddy dasu din zanje yanzu in samu daddy din. Yana gadin haka ya mike tsaye ya fita zuwa part din daddy din yayi sallama ya shiga don hango daddu din da yayi zaune kasa yana waya hjy karima zaune a gefeb shi..
Chapter 178 · 0% Book details