← Book details Ana Dara Ga Dare Yayi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 190 OF 337

Sashe 190

Ana Dara Ga Dare Yayi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ranan kan na samu barci sosai yadda na fara hakama saukan shi yazo min don saidana shaki barci kusan wuni daya ina abu daya sai yamma na tashi. Gidan ne yayi min shiru na mike zaune ina duban wayana da ban gani ba a gefena dana san ina ajewa din a hankali na fito zuwa falon sai dai banji motsin umma ba a falon na bude labulen dakin ta a nan ma bata cikin dakin lokacin. Haka yasa na nufi kofan gidan namu na bude dagani sai dogon wando light brow da riganshi kala daya kaina a hargitse duk da na daure shi da ribon ta baya. Ummace a tsaye tare da Abdul suna magana jin budan kofa yasa su juyowa suka kallo inda a cikin mama umma ina wayata na fada. A cikin dan tsorata da i,iniya take fadin wayan wayaki na wuri a dakina na saka maki chagi jin hakan yasa na juya na barsu tsaye suna mamaki. Ba komai sukewa mamaki sai tun farkon faruwan ciwona na umurci da adauke wayan a kusa dani bana son ganin ta yasa umma ta boye wayan a wurin ta duk tsawon kwanakin tana kuma saka caji a cikin ta. Dakin nata na shiga na dauko wayan dake saman filon ta nafito zuwa falo ban zauna ba na nufi kofan sai gasu sun shigo nace umma yunwa nake ji sosai a cikina. Kallon inda Abdul yake tsaye shima din ni yake kallo a cikin mamaki wai yau nice ke tambayan abinci da bakina wace kwana da kwanaki bana cikin komai sai diyan icce a cikina. Da sauri umma tace abinci bari a dauko maki abinci kici ta wuce zuwa kitchen da sauri ta hado abinci ta kawo min. Sune zaune sun zuba min ido har na kusa tashi da leda daya na sakwara da miyan yauki dsyaji nama manyan yanka a cikin sa. Saida ya saura kadan na dauki goran ruwa na kwankwade shi saura kadan shima na aje tare da lumshe ido sai lokacin ne na tuna da suna tsaye a kaina dan murmushi na sake a cikon kunya kafin kuma na mike zuwa dakina da sauri fitsari nayi sosai a lokacin naga ai gara na watsa ruwa naji dadin jikina a lokacin. Wanka nayi na dauro alwala kodana shirya na fito nasamu Abdul baya gidan sai umma zaune a falo tana ganina tayi min sannu na amsa Ammar dake kwance shima ya dago yana gaidani. Wai umma wani abu ya farune halan ina barci kadin umma ta girgiza min kai tana fadin ba komai Ammar ya dago yana fadin . Baki da lafiyane fa almost one week ke nan yau ni na tambaye shi da sauri sai umma ta mika mai dakuwa da hannu tana zagin shi. Maida kaina nayi jikin kujera ya dan lumshe idona ina tunane saidai na kasa tuna komai a lokacin yadda ya dace in tuna din. Ammar dauko min laptop dina a daki na fada don sam bana jin karfin jikina ko kadan ya mike da sauri ya dauko min tana da full charge don haka na fara duba abinda nake son dubawa. Date din ranan na duba da sauri na dago kaina don ya nuna min rabona da yin aiki ga lokacin kafin in magana muniya ta shigo dauke da cool abinci tana ganina ta washe bakin jin dadin ganina zaune ina aiki. Ta shigo da murnan ta tana fadin oh mun godewa Allah sahiba kin tashi ogana yayi kuka sosai kan rashin lafiyan nan naki ranan shida Adnan a gidan mu. Barin aikin nayi na dago kai ina kallon ta cikin mamakin jin abinda ta fada sai kuma na juya na kalli umma na dukar da kaina. Daga inda yake tsaye yaga yana neman faduwa kasa a lokacin hakan yasa yakai kasa zaune saman dandaman wurin tun baiyi nisa ga karanta abinda ke cikin ba ya fara cin karo da tashi hankali. Tsab ya gama karanta komai yanayi yana share gumin dayake tartso mashi saman goshin shi da hannu daya kafin ya mayar da file din ya daure kamar yadda ya sameshi a wurin saidai wanan karon bai bar file din haka yadda ya sameshi ba a wurin saida yayi itin nasa dabaran ya musaya komai ya canza wurin sallon ajiyan. Ya fito ana sara mashi sanin koshi waye a wurin daga nan yayi sallama dasu yafito ya shiga motar shi yabar wurin hankaki tashe Allah ne ya gyara ya isa lafiya don baya ko ganin hanya da kyau a lokacin, Haka ya shiga gidan suna falo a zaune don uinin ranan bata leks asibiti taga yan uwanta ba acewan ta tagaji da zuwa mutane suna nunata. Don haka tayi fushi ta daina zuwa da rana a cewab saida dare zata dinga lekasu da niyar yau tayi masu dafuwa taje dashi ko don gorin da akai mata a safiyan yau din. Saiga mijin nata ya shigo a yanayin data ganshi ta fahinci ba lafiya gareshi amma hakan baisa ta tashi ta bi bayan shi taji meke damun shi a lokacin. Sanyine ya rufeshi lokaci guda jikin shi har yana karkadawa don tashin hankalin daya tsunci kanshi a ciki ranan. Yana kwamce shi kadai a dakin sai rawan sanyi yakeyi shi daya yana kuma faman tunane abinda ke karasa hauhawan zazzabin jikin nasa yake kara karuwa a lokacin. Lalai duniya baki da tabas don mutum gaskiya ba abin yarda bane ashe ko kadan a zamanin nan koda kuwa kun fito tsatso daya dashi kada kayi saurin aminta dashi kai tsaye sai ka fahinci shi waye a zuciyar shi. Idon ya kara rintsewa lokaci guda yana maijin wani irun zafi a zuciyan shi bayan na jikin shi dake fita a lokacin. Ba ita tashiga dakin ba sai bayab isha,i data fito wai zata asibiti a lokacinne ta sameshi a dakin ya rufe ruf a cikin wani yanayi na tashin hankali. Amanatace ta raya hakan a zuciyar ta kafin ta kirashi tare da fadin zan tafi asibiti na dubosu dakyat ya iya budan baki yana fadin. Don Allah kashe min Ac din nan gaba daya ta wani kalleshi shekeke kafin tace tou fa a cikin wani yanayi ta nufi wuri makunnin wutan ta rage Ac din har ya rufe jikin shi ya kuma bude a daidai lokacin da take fadin na tafi yaran suna gun mai,aiki idan kafito ba tare da nuna damuwa da halin da yake ciki ba a lokacin. Dan miko min ruwa mara sanyi ya fada a wahalce nan ma saida ta dan kalleshi kamar zatayi magana sai kuma ta wuce tana fadin kada dare fa yayi min ban fita ba. Takawo ruwan saman table ta dangware mai tun bai dago ya kara fadin wani abu ba ya tsayar da ita don haka ta fice a gidan kai tsaye. Acan asibitin ma samun mahaifiyar ta tayi ta cika da ita tana jiran zuwan ta don rashin jinta da kuma rashin kirasu su san halin da take ciki kamar ba yar uwan haihuwanta matsala irin haka ya sama ba a lokacin. Idan sauran yan uwan nata sun nuna ko in kula suna goyon bayan dan uwansu itafa da suka fito ciki daya da yar uwan nata. Iein fadan da uwar ta dingayi ke nan lokacin tana zaune tana taunan cingan tare da duban wayan ta jin uwar tayi shiru ta karasa da Allah dai ya sauwa irun wanan abin haka kamar masu bakin uwa aka. Mama konazo din da haka mutane zasu dinga gulma suna nunani ni kuma haushin hakan nake ji wallahi. Kuka kanwar dake saman gado ta sake lokaci guda don jin zafin abinda yar nata tafada a lokacin ita ke nan taji kunya a nunata a matsayin yar uwanta inaga ita kanta ke nan. Kiyi hakkuri Allah zai kwato maki hakkin insha Allah in suna ganin kamar kece kika gaiyatoshi zuwa wurin ki kamar yadda suka juye zancen a yanzu gaba dayan su. Bata kai wani lokaci ba don tagaji dajin irin wanan zancen dake kara mata takaici a zuciyarta ta mike tana fadin tau mama zan tafi nabar yara a gida da mai aikina. Cikin makoshi uwar ta furta Allah bamu alheri tafice suka bita da kallo alokacine kuma uwar tasake kukan takaici haka yayi daidai da shigowan yayanta maza suke tambaya. Lafiya mama wani abune ya faru kuma tace ba komai sai kanwar tasuce ke fada masu abinda yayan nasu tazo tace a wurin. Saida ya falkane yaga goran ruwan data aje masa a wurin duk yadda yaso tashi ya dauko jikin sa yayi masa nauyi ya kasa tashi a lokacin haka ya mayar da barcin a wahalce sai cikin dare ya tashi daya dan lafamai ya samu rama sallolin dake kanshi dabai samu yiba. Anan kuma ya zauna yasha tunane akan abinda ke addaban shi a lokacin ya dade yana rokon Allah da neman yafiya daga Allah kafin ya samu ya rarafa ya hau saman gadon ya koma kwance ringingine yana faman sakawa da kwancewa. A haka gari ya waye masa baikai ga mafita ba da kyat ya iya samu yayi sallah ya koma ya kwanta yana jin zazzabin na neman ya dawo mai a lokacin. Washe gari yakama asarbar ne don haka babu zancen fita aiki a wurina hakan ya ban daman samun gyaran gidan mu duk daba wani dattin dake cikin sa amma na daure na gyara don jikina ya kara sake min. Ammar ne yake labarta min abubuwan da suka faru dani da yadda na kasance ba magana wani iri naji a zuciyana take hawaye ya fara silalowa daga idanuwana. Sai tunane nake menayi suka zaune akaina duk yawan mu sai nice nake da wanan laluran mai matsala da batarwa a cikin yan uwa. Muryan ummace data fito daga bandaki take fadi to mai surutun tsiya watau dana hana ka fada saidai ka faki idona ka fada mata komai tana kokarin kai mashi rankwashe a kai nace umma don Allah ki barshi. Idan bai fada min ba waye zai fada min umma shi kadai nake dashi a yanzu shinake gani yake ganina a matsayin dan uwa na shikiki a gareni umma. Dole duk abinda ya shafeni ya shafeshi shima umma kada ki hukantashi kan abinda ya dace yayi yayi din kuma zaki hukuntashi kan
Chapter 190 · 0% Book details