← Book details Ana Dara Ga Dare Yayi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 50 OF 337

Sashe 50

Ana Dara Ga Dare Yayi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Adduan ku nake nema ga bakunan ku masu albarka yan uwa Allah ya yaye muna matsalolin mu ga baki daya dani daku duka amin. Duk da ba wani sabo mai tsawo a tsakanin su har yanzu a matsayin su na ma,aurata a yanzu hakan bai hana ita ta kawar da komai ba a fili don irin tsananin son da take mashi har cikin zuciyarta ta nuna bata damu da yadda yake daure mata ba. Yanzun ma dakin ta shigo a cikin kwaliyan ta tun bayan fitan ta daga dakin misalin karfe taran safe ta shiga nata dakin waya tayi da yar uwarta kuma aminiyar ta na gidan su tana bata labarin irin gwarzon min mijin da Allah ya hore mata daga sama irin wanda suke mafalkin samu ita da aminiyar nata a kullun. Yau ma dai Nazifa bata barshi ba don itace mai neman shi bashi ke nemanta ba duk wanan a cikin wayen wata yake kuma take nuna hakan cikin rashin damuwa don tasan wata rana daina hakan zaiyi idan sun saba. Aure irin na fulani asali sukeyi a family su wanda kwatsam zakaji an daura auren wance da wani ba tare da sun san juna ko sabiba a tsakanin su kuma a zauna lafiya baka taba jin bakin su ga hakan. Ta shigo dakin a cikin takon izza da isa da gadara irin na yan gidan su da suke jin Naira na motsi a jikin su sun kuma tashi da wanan akidan kaf din su maza da matan su haka suke da nuna isar su acikin jinin su hakan yake masu. Da dan fara,anta a fuskan ta taja tayi tsaye tana bin shi da kallo tare da tsuke fuskanta lokaci guda tana kallon shi a gadarance tace dashi. Wanan jakar da kake hadawa fa na menene shi ta fada daga inda take tsaye fuska daure hakan yasa ya dago jin yadda tayi mai magana a cikin gadara yana kallon ta kai tsaye shima ya bata amsa da fadin tafiya zanyi yanzu. Babu wani shakunta ko firgici a fuskan shi ya bata amsa kai tsaye kana ya juya yaci gaba da abinda yakeyi din. Tashin hankali tace ina kuma zai tafi bayan Abban ta yace zai zauna da ita har na tsawon sati uku a gida yanzu ko sati daya bai rufe ba da dawowa har ya fara shirin wani tafiya can. Zip din dan jakar tasa yaja ya mike gabanta yana kallon firgitatun idanun ta da suka juye tankar tana cikin maye a lokacin. Cikin daurewa yace lafiya dai naga duk kin canza lokaci daya ko wani abune ya faru kuma ? So nake na gaskanta wai da gaske tafiya zakayi kuma a yau din nan bayan Abba ya fada ma sai kayi sati uku tare damu a nan ko zakayi wani tafiya a yanzu. Yayi murmushi tare da girgiza kanshi kadan da daga kafadan shi yace shi Abban naki ya fada maki hakan game dani ? Wata karfafan ajiyan zuciya ta sauke tare da fadin nasan kunyi hakan da Abba don Abba ba zai mun karya ba ka sani idan kuma kace zaka tafi yanzu zan daga waya na kirashi. Ya saki murmushi yana duban ta kafin yace a wanan karon kan ya fada maki ba daidai ba don ni bamuyi hakan dashi ba. Na shiga uku kana nufin ke nan Abba karya yayi min ko me ya Ababakar don haka maganan ka ke nufi a yanzu. Anyway duk yadda kikace haka din ne nidai nasan ba mace nake ba balle har a kafa min doka inbishi dole ina fatan kin gane. Ya sure jakar shi tare da wayoyin shi ya rataya yana fadin sai na dawo da sauri tayi kanshi a rude tana fadin. Wait wallahi ba zaka tafi ka barni ba ni ban gane wanan irin rayuwan ba kullun ace mutum na hanyar tafiya ni kwata kwata sam ban ganewa hakan ba. Hannu yasa ya jayeta a hanyar yayi ficewan shi rai bace bai ko kara waigo ta ba ya fice daga gidan yana jin wani iri a zuciyan shi a lokacin har zuwa lokacin da faruq yakai shi airport ya shiga jirgi suka daga. Duk da yasan ranan babu jirgin lagos haka ya daure zuwa Abuja daga can ya fada na lagos din din kiran da chuku yayi mai na gagawa akan mu. Yanzu kan sai ince faduwan gaba ya zama min jiki har na dan saba da hakan a rayuwa ganin ba abinda ya sameni tun ranan. Haka na fita daga gida sai ras ras nake ji lokaci lokaci ina dauke da dan buhun sassake na ganyanyaki sai garin magani a kule. Apapa na nufa kai tsaye inda nake zaton cabawa ga matan wurin don a gaskiya ina ciniki sosai a wanan erea din idan nakai kayana can. Wata hamshakiyar mace ce ta fito daga motan ta tana kullewa zata shiga wani botiq nake mata talla ina fadin, madam come buy local medecine for pink, Ta dan kalloni a yatsune taci gaba da tafiya nace madam try,am nd see ego work for u well,well sai taja ta tsaya wuri daya na sake fadin may try my medecine and see ma god go give u fine fine pikin i swear. Da mamaki take kallona na sai ta karaso har inda nake din tace dani how d u no, dat i no born ? nd i de looking for dis medecinen ? Emm, i just look at u and saw u problems in ur face na fada yadda masu magani ke fadi idan zasu sharota ga mutum. Tace Surprise u small pikin u know all dis tins in ur life ? d u have d that my ogo no look anoda worman again after me. Na shiga kiciniyar bude leda ina fadin if u use dis one e no go see any woman again i swear ina daga hannu. Mukai ido biyu da chukuma dana fara zargi a yanzu don sau uku ke nan ina yawan ganin shi a inda nake yawon tallana. Dan rudewa nayi na shiga yiwa matar bayani a gurguje ta karbi na haihuwa dana kama miji a cewan ta . Ta miko min kudi mai yawa na karba ina godiya tare da fatan maganin ayi nasara abinda ake nema tana fadin Amen ta hanyar daga hannuwan ta. Ina sauri nake tattara kayana in bar wurin naji muryan a baya na ana fadin i wan buy local medecine for my pikin. Ba tare dana juyo ba nake fadin i no go sella,am for men ina sauri naga an tare min hanya bayan wanda ke bayana din. Waitin u wan do for me now, comot for d road , or i will shout oley for u naw, na fada a dan hasale . Katin shedan su ya ciro ya nuna min ban fahinci na meye ba sai kayan kakin dana gani na gane me hakan ke nufi. Waitin i do for u, see me see wahala woo, me i no do antytin wain solder man wan cach me naw, . Motan dake gefen shi ya nuna min da hannu na dan saci kallon bindingan dake gefen shi da ido ba musu na nufi wirin motan ina waige ko zan samu mai cetona. Allah da ilon shi kuwa a take yan wurin suka taso suna fadin ogo waiti dis gurl do for u she no fait with any body here. Why you go arest her naw, waitin she do for u ? suna kallona suke tambaya daga inda nake tsaye da naji sun fara magana naja na tsaya inacewa , me i no do anytin for dem broda. I don't no dem, nd even who dey are ma self, still card din shi ya ciro ya nuna masu sai suka fara darewa daya bayan daya suna sulalewa daga wurin don ba mai son wahala ta ritsa dashi a cikin su. Tare da buhuna suka turani motan suka bar wurin kamar walkiya har mukai nisan tafiya ban kula da wanda ke kusa dani ba a lokacin. Duk ina sake sake a cikin zuciyana na yadda zan samu in kubuta a garesu shine kawai abinda nake yi lokacin. Don nasan idan Umma na bata ganin ba ranan zasu shiga wani hali na tashin hankali su dauka an sace nine. Duk a yanzun din ma ba zan iya cewa ga wa yanda suka dauke ni ba ma don ban san abinda nayi masu ba suka sakani motar su haka. Saidai idona yana kyankyashe ko dar din hawaye ban sake ba sai bin titin nake da kallo naji an jefo min tambaya da what is your mother's name ? Na dan juyo a dan firgice na kalli mai maganan saida na dan kadu da ganin shi lokaci guda haka a gabana . Shiru nayi don ko bindiga suka saka min ba zance ga sunan umman mu ba a rayuwana saida na bayan yace min u no hear he de asking u. Nace a cikin e,e niya i don't no her realy name we de call her with umma by name. Dan shiru ya biyo kafin yace which tribe are you nace, my mama told us we are hausa fulani by tribe. Okay yace ya dan gyara zaman shi kafin ya sake fadin, from which state nace she no tell me that i only know we come from north side dat what she told me. Yace so ke baki san sunan gari ku bama a rayuwan ki yana gyada kai na dan bishi da harara muka shiga go slow daya fara marance. Allah maijin kan bayin sa a haka yana min tambayoyin ina bashi amsa daidai gwargodon sanina wani yazo ya daki motan nasu sai wanda ke gefena ya fita fada da maishi. Ban tsaya jiran wani abuba na balle motar nima na fita na yanka a guje sai gani na bullo wani unguwa da ma ban taba shigan shi ba. Haka na tare me keke na hau zuwa wani titin ina zuwa na fada motar da zai kaini unguwar dake kusa da namu do ba,a samun mota daga nan . Har lokacin gabana sai faduwa yakeyi Allah yasa kudina yana jikina can na barsu da buhun maganina na gudo har nakai gida ina tunanen hadina dasu da suke
Chapter 50 · 0% Book details