Sashe 310
Ana Dara Ga Dare Yayi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
lokaci guda. Yana yuyuwa streas ke damun ki tunda baki huta ba tun last week kuke event kinga hakan zai iya jawo maki ciwon jiki a yanzu daki daure muje din likita ya duba min ke ? No don't worry your self iam OK now na fada a kasalance sai ya bini da kallo kawai kafin naji yace wanan ne dalilin da zaisa na barki ki huta nan na dan lokaci sai daga baya zan dawo in tafi dake. Nima zanso a barni nan na zauna zaifi min zuwa wancan kasan don na zaifi min zama kusa da mahaifiyata da dan uwana a saukake. Sau nawa zan fada maki cewa ba zan barsu su zauna a nan ba suma ko kina daukan hakan wasane zamu tafi da farko daga baya zan turo a dauke su lokacin kin saba da can. Kara lumshe idona nayi a hankali kafin nace dashi kana ganin hakan ba zai jawo wani matsala gun mutanen ka ba ina nufin yan uwanshi ya kuma gane me nake nufi din yasa yace. Ina ruwan wani da family dina yanzu ko mahaifiyata itace ta zabi zama nan kasan nasan kuma saboda sister dinane dake nan zaune. Don haka kuma ba zan tauyewa wani daga cikin kuba hakkin zama da kowa nasa tunda Allahbya hore min abinda zan ciyar dasu din . Ban kara magana ba illa matsua da ya tashi ya bar min dakin dana matsu yayi lokacin saidai kuma naga baida niyar yin hakan shi asalima kamar dadin zama yaji a dakin shi. Saima naji yana fadin da safe zasu tafi an riga da anyi masu bucking din jirgi karfe takwas na safe shine nazo na sallamesu saidai zanso a bar Faiza da wata babba a nan tare dake idan hakan zai samu . Faiza tana aiki a kaduna na fada don haka dole ta koma aiki saidai Fatima da zamu zauna tare da ita zasu bari ina gani dan shiru yayi kafin yace anyway zanyi magana da uncle hamza idan na fita yanzu asan abinda za a yi akai. Sai kuma yakai hannun shi saman goshina yana fadin don't be a lazy tun yanzu kin fara rakin barin gida umma will be with you soon nasan shine damuwan ki dai yanzu. Dan lumshe idona yayi banyi aune sai naji yakai min kiss a gefen fuskana yana fadin take care zan tafi saida safe ya mike tsaye ya fita da sauri daga dakin. Nan ya barni cike da mamakin wai meyasa maza basu da kunya ne wai mutumin da yake a matsayin yaya a gareni ko mahaifi amma shi sam ba kunya ko wani nauyi a idon shi sam a kaina. Har barci ya daukeni bangama tunanen zantukan mu dashi ba ga kum yan uwana sun shiya barina da farko ban dauka zanji komai ga tafiyan su ba amma yanzu dana tabbatar haka dinne sai nashiga damuwa. Haka su sister suka kawo masu alheri har dakina suke suna min ba,a haka baisa nayi magana ba lokacin suka tafi. Barci barawone shine ya daukeni har na rage jin irin yanayin da nake ci washe gari kuma aka tashi da wuri kowa yayi haraman tafiya duk da sammakon mu amma saida aka kawo abun karyawan su daga gidan mahaifiyar mukhatar din. Bayan sun karyane mota tazo ta kwashesu hardani a rakiyan su don mukhatar din da nake kira da Uncle a yanzu don na rasa sunan da zan kirashi dashi wanan lokacin. Ga manyana nata karfafa min cewa nayi biyayya na girmama duk wanda ya dace nabashi girman shi haka in zama mai tausayi da taushin zuciya ga kowa koda maigadin gidane. Wanan huduban abokan arzikin mune na lagos da sukayo min rakiya su hudu har maiduguri daga cikin su tare da muniyat da makwabciyan mu Aminat suke yawan fada min hakan damun kebe dasu. Dagani saishi a motan muna baya driver yana jan mu a gaba sai motar dake bi muna su faiza ne kadai a cikin ta ko wani mota biyar biyar aka dauko su a cikin lafiyayyun motaci masu kyau da tsada. A gaskiya ko don wanan karamawan danaga gun mutanena ya isa zuciyana ya sassauta abinda nakeji anty muniyat ce ke wanan maganan lokacin da muka fito zamu shiga motar dan bamu san shima zaizo mu tafi tare dashi ba. Gaskiya kan an karamamu sosai anty Amarya ta fada na dan yi dariyan yake wanda shine dabi,ata kawai ba yawan magana. A daidai lokacin Motanshi ta shigo gida ta tsaya daga dan nisa kadan damu ya fito da sauri da alaman yaso makara yake gani. Inda su gwaggo suke ya fara isa da sauri yakai kasa gwiwa bibiyu a wurin yana gaidasu suka amsa mashi suma a cikin mutunci da girmamawa zaku tafi ke nan ya fada a cikin gurbatatcen hausan shi don ba hausan yake ji sosai ba yare ya amshe harshen shi sai turanci. Eh mukhatar sannu da dawainiya mun gode kwarai Allah yayiwa aure albarka ya baku zuria masu albarka ya amsa da amin nagode kafin ya mike. Wurin su faiza ya nufa suna ba,a tunkan ya karaso yake fadin kedai badake za a tafi ba sai kin kwana muna biyu a nan zaki koma . Bayan ya gama dasune ya nufo inda nake tsaye tare dasu muniyat din ya gaidasu nan manya suka sake addua daga inda su gwaggo suke tsaye gwaggo kudidi tace ashe mutanen nan haka suke da yawan ibada ? Suna da ibadan kan saidai shirme yafi yawa a cikin sa don dai suna hadawa da al,ada sosai idan ba yanzu suke gyarawa ba. Shine yasa ai nasan ba wani aikin banza su mairo suka aikata ba can da diyanta don dan zaman umuran da mukayi da ita na fahinci tana da rikon ibada da kamun kai sosai wallahi gwaggo Amina ta fada. Aiki a zahirance ai bashi bane zuciyar mutum wayasan abinda suke aikatawa a boye tunda ba mijine dasu ba can rayuwan lagos fa idan ka shigeta sai a hankali gwaggo hari ta fada tana yamutse fuska. Kai haba hjy hari koma meye ai tunda sun samu sheda haka ya wadatar don Allah ki iya bakin ki akan mutanen nan yanzu tunda Allah ya wanke muna su yar uwanta hjy Asiya ta fada. Shiru tayi bata tanka ba don ta fahinci me yar uwan nata ke nufi da zancen ta akan ta daina maganan haka kada zancen ya dawo kunnem mu ba abu mai wuya bane yanzu inji. Yana isowa inda muke tsaye ya dago ya kalleni tare da daga min gira yana fadin yaya jikin ya kika kwana ? Not bad na bashi amsa ina gyara rufin lafayan dake saye jikina lokacin don shi anty amarya ta ban shawaran na dinga yafawa tunda an zuba min su da yawa a kayana. Lafaya din yayi min kyau sosai a jikina sai kamshin turare da nakeyi wanda yanzu kan ya fara zama min jikina duk da rashin son kamshi da ban so ada. Kana yin abinda baka so don ka kyautata rayuwan na tare dakai don kawai farin cikin maishi haka anty amarya ta fada min a karshe da take bin jikina da kamshi. Zo naji lafiyan jikin naki kunnena yaji lokacin da banzata yana fitowa dags bakin uncle mukhatar din lokaci guda. Yi nayi kamar banji me yake fada sai na basar da fadin antashi lafiya ya mutanen gidan suka kwana lafiya ya fada yana cusa hannayen shi a cikin aljihun shi ya kara kallona yana fadin mu karasa airport din kada su makara. A nan kowa ya shiga motar kamar yadda sister ta tsara komai don tana wajen shine muka rakasu airport din ko a motan ma da zamu hannun shi yana sagale a cikin nawa yana dan matsa min su a hankali har muka kai airport din yana dan jana da fira ta hanyar tambayoyi su masu tafiyan ina masa bayanin wanda na sani. Saida muka tabbatar tafiya ya kankama don muna zuwa aka kirasu muka fara sallama lokacin ne naji wani irin yanayi kamar kuka zaizo min saga muniyat ta fara abinda yasa nawa saukowa ke nan. Rugumoni naji yayi a jikin shi tare da kama hannun fatima dake tsaye a gefen mu don mu kadai muka rage sai sauran yan uwanshi da suka rakosu suma da sauran mutanen shi a wajen. Bai bari munga tashin su ba muka dauki hanyan wurin da motan take aje ya shigar damu muka koma gids har lokacin kuka bai tsaya min ba. Muna shiga dakina nayi kokarin shiga kai tsaye sai naji ya rikeni ta baya haka yasa dole naja na tsaya na fada a jikin shi naci gaba da kukan da nakeyi fatima ma ganin ina kuka yasa ta fada saman kujera ta makure tana nata kukan. Bayana ya dan fara bubugawa yana dan murmushi kafin yace why are you crying ko zama nan ne bakyaso na mayar dake kaduna yau din nan, idan zama can ne yafi maki nan din ?. Kaina girgiza ba tare dana furta komai ba nayi kokarin zare jikina daga nasa amma sai naji ya kara rikeni tam a jikin nasa ya kwatar min da kai saman fadadan kirji shi. Na dan lokaci ina lafe sai sheshekN kuka nakeyi a hankali ki duba fatima ma kin sakata tana kuka kamar ke don tags kema kinayin abu kamar karamar yarinya. Sai kuma naji yayi murmushi anyway kina da right na kuka a yanzu nasan irin pain din da kike ji a zuciyar ki game da hakan don bakya so na ko Sahiba ba zaki iya zama da tsoho kamana ba. Hakan baisa na dakatar da kukan da nake danyi ba a lokacin sai ma kara dan sautin shi danayi a lokacin haka ya rike hannu zuwa part din dake gefen nawa din. Key ya dauko daga wani wuri da bazaka san akwai ma,adana a wajen ba ya bude kofan sai lokacin ya dan sassauta rikonnda yayi min din yana fadin key din part din ki na wanan waje but is a secret kada ki bar wani ya sanda hakan don tsaro . Yana budewa wani dan karamin falone ya baiyana a gaban mu shima dai kusan komai da akwai a nawa a kwashi nan din saida kala daya banbanta don nan din