Sashe 90
Ana Dara Ga Dare Yayi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Har wani riba zaki samu a wurin abinda akace ba a yafe a kansa ba ki nace sai kin karantashi kamar wani zancen daya yafi karuwa akan addini iyakafa rayuwan zaman duniya ce labari. Allah yasa mufi karfin zuciyar mu mu gujewa duk abinda zai kaimu ga halaka Allahuma amin. Ba kowa banw a dakin Asabe ce mai aiki ta kawo wa umma hira sai fatima da bata da lafiya aka barta a gida wurin umma tana kwance tana barci a dakin namu. Gaidasu nayi na aje ledan da na shigo dashi na nufi hanyar bed room din mu kai tsaye ina jin Asabe na fadin an tashi ke nan tunda ga yar nan ta dawo. Ban tsaya sauraren ta ba na shige ciki kayan jikina na cire na daura zani kana na shiga bandaki na watsa ruwa don nayi sallahna a can. Fitowa nayi na samu Asabe ta fita ta koma part din da take sai fatima dake barci tana jin muryana kuma ta mike ta taso zuwa inda nake zaune tana kwanciya saman jikina. Hannuna nakai na dan shafa wuyan ta har lokacin da sauran zafi a jikin ta na tambaye ta ko taci abinci ta girgiza min kai alaman bataci ba. Na zauna a kasa na bude ledan nace ta taso taci takai idon ta a ledan sai ta dan bata fuska dana matsa sai ta sauko na fara bata drink din milk sai gashi tasha sosai umma dai tana zaune tana kallon mu na bude kajin da kamshin shi ya hade dakin yasha kayan hadi irin na sayarwan su. Yakai kamar sau uku data karba saiga uwar ta shigo ta dawo don yar data bari a gida mukai mata sannu da zuwa take fadin ashe sauki ya samu . Yanzu jin dawowan yarta ta tashi dazun ai har ta bamu tsoro don amai tayi sosai ga jikin nata yayi zafi sosai kuma . Nayi mamaki jin Anty na godiya kan abinda akaiwa yarta matar da take dagawa kowa kai a gidan tana nuna ita tafi kowa da komai kan yarta sai gashi tana muna godiya goran milk din gaba daya da naman na raba biyu na mikawa fatima din suka tafi . Mikewa nayi na rufo kofan dakin na dawo na mikawa umma kayan na zauna a gefen ta da alaman magana a bakina lokacin. Meya faru umma ta tambayeni tana kallona na nisa ina fadin umma na sake ganin shi a garin nan fa yau a gidan nan da zamu fita tare dasu daddy sai kuma a wurin wanan wasan da mukaje yanzu. Wa kika gani umma ta tambaya nace wanda ya kai Amar asibiti da soja sukazo nema a gidan mu rana wanda yake ban kudi idan mun gashi. Gidan nan fa umma ta tambaya nace wallahi umma kuma yau ma yace kada na kuskura na nuna nasan shi a baya idan nayi haka na kyautawa kaina. Innalillahi umma ta ambata kafin tace Sahiba ina tsoron lamarin ki wallahi tun ranan da za, a kashe mahaifin ku irin kukan fitinan da kikayi sai yanzu nake gane hakan nada dalili ashe. Yanzu abinda nake so dake kada ki kuskura ki nunawa kowa cewa kin sanshi kamar yadda ya fada koma me hakan ke nufi ubangiji Allah ya mayar muna dashi alheri. Amin na fada a sanyayye kafin in koma tunane take tambayana wanan fa tana nuna min ledan dana aje da kayan sanyi, nan na fada mata komai daya faru har wayan da naji Nazifa tanayi a motan game dani. Haukan kishi ne wanan shi din ai yasan abinda yakeyi duk da sheri gadon shi tayi abin a jinin su yake masu dama. Washe gari ma hakan na tashi babu walwala duk tunane ya dameni a lokacin bayan sallah asuba na koma na kwanta lokacin na farka da sauri don mumunan mafalkin da nayi na tashi a cikin damuwa. Daddy nayi mafalki dashi mota tanata turnbuling dashi saman hanya ga shi yana neman taimako a cikin motan ba wanda ya kawo mai dauki a wanan lokacin ne na falka nayi wani irin zufa sharkaf na mike zaune. Ina bin falon mu da na kwanta bayan sallah asuba na dawo nan na kwanta a nan na yi wanan mafalkin da daddy din da nayi ya kuma tsorotani. Mikewa nayi da sauri na nufi wajen gidan babu kowa a wurin sai yan aikin gidan dake aiyukan su a lokacin. Na dan bi ko ina da kallo idonane ya sauka kan mai,aiki dake faman wanke motan da nayi mafalki da daddy a cikin sa ya samu wanan hatsarin. Juyawa nayi na koma cikin gida har lokacin gida na tsit kamar babu kowa a cikin sa don kowa na daki yana barcin safe a lokacin. Part din mu dake can kuryan gidan na nufa na tura kofa na shiga sai naga umma a tsaye tana mamakin ina naje a lokacin don bana fita a irin wanan lokacin. Tambayana tayi a cikin harshen yarbanci da ina na fito nace na fita waje ne ina zama ta bini da idanu kawai. Bamuyi wani girkin abinci ba tunda aka fara sha,anin bukin nan daga gida gwaggo Asiya ake shigo da abinci don yan aiki dake girkawa. Don haka na koma nakai kwance a inda na tashi din umma zama tayi tare da kuna tv tana sauraren azkar din safiya da sukeyi a tv kullun . Barcine ya kara daukana a wurin na danyu nisa kuma na sake yin maka mancin wanan mafalkin da daddy din sai dai wanan karon wani mutum na gani yana kwasan dariya irin na kyata muryan shi babu dadin ji. Wani irin falkawa barci nayi tare wani irin zabura da har umma saida ta dan razana dani yadda na falka din fita nayi irin na dazun din . Saidai wanan lokacin motar an gama wanke ta sai sheki takeyi hasken ranan daya fara fitowa yana haskata . Juyawa nayi na koma cikin gidan da shigana part din mu nace umma suna son su kashe daddy a yau din nan. Sahiba kanki daya kuwa nace wallahi umma na gani har sau biyu a cikin mafalki sai akace maki mafalki kuma gaskiyane ko ? Wanan gaskiyane idan har daddy ya shiga motar shi baka a yau zai iya halaka subbahanallahi ta fada tare da mayar da hankalinta a wurina. Kada ki yarda kiyi wanan zancen da kowa ta fada min a cikin daure fuska idan banyi ba duk abinda ya samu daddy din kece da laifin hakan umma . Na fada ina komawa na kwanta tare da runtse idanuwana mafalkin yana dawo min kamar a lokacin nayi sa. Mikewa naga umma tayi ta fita daga part din namu na mayar da idona na rufe sai can naji muryan mommy a kusa dani take fadin. Sahiba meke faruwane wai dake idanu na bude a hankali nace mommy ban sani ba nima amma dai wani abu mara kyau zai samu daddy a motar shi yau idan ya shigeta. Kallon umma tayi jikin ta ya fara rawa umma ke fadin yanzu ya za,ayi hjy dole in fadawa Alh mommy ta fada kada ya dauki zancen da wani manufa amma ? Bari dai inje mommy ta fada ta mike da sauri ta fita zuwa part din daddy din ankai kamar awa daya sai gasu tare da mommy din har part din mu. Ina zaune a cikin damuwa nayi shiru na kurawa kasa ido ina tunaje yayin da duk kafana na dora saman kujeran na dunkule a cikin light pink din hijjab dina da yaya ya saya mun. Ummace da take zaune ta kurawa tv da ake bayani akan sallah ido tana kallon yadda malamin ke bayani ta amsa masu sallama. Tun daga kofa daddy ke fadin yau meke faruwane diyana ance kinyi mugun mafalki dani hankalin ki ya tashi ko ? No ba mafalki bane daddy gaskiya ne na fada mai ina dagowa a cikin damuwa zama yayi a kusa dani yana fadin meya faru fada min inji. Sai hawaye na kasa magana a lokacin umma tace tunda asuba fa ta fita ta dawo ina tambayan ta tace min ba komai. Ta kwanta kuma sai gashi ta tashi a tsorace tana firgita take fada min wai zasu kashe ka yau din nan idan har ka shiga motar nan taka Baka ta waje. Ba abinda zai samu daddy ki da yardan Allah kinji Sahiba yana dafa min kafada na na girgiza kai nace don Allah kada ka shiga daddy. Yayi murmushi irin na manya jin haka da sauri na mike tsaye na nufi dakin kwanan mu don bamu raba daki da uwata ba har yanzu a gado daya muke kwana tare. Wani ruwa na dauko na fito dashi hannun shi na kama na shafa mai ruwan yana dai kallona bai ce min komai ba suma duk ido suka zuba min suna kallona. Alh yarinyar nan fa akwai abubuwa a kanta gaskiya baiyana daine basuyi ba har a gane hakan don wallahi ranan itace hana muci naman nan dana kai ma ya canza kala . Sahiba din daddy ya tambaya mommy tace kwarai kuwa Alh tace kabar yar nan wurin nan kawai inda ka ganta abubuwa da dama wallahi in sahiba ta fada duk sun zama gaskiya zuwanta garin nan. Kin san maza da karfin hali don daddy din murmushi yayi yana mikewa yace ashe tarihi zai maimaita kansa ke nan don haka mahaifiyar Attu take ai itama sai bayan mutuwan ta aka samu galaba a kan zuri,an ta. Ba komai kada ku yarda da wanan abin kinji idan kana yarda da irin hakan imanin ka ne ke samun rauni ya fada a karshe ya fita mommy ta bishi da fadin kada dai ka shiga motar nan yau Alh gaskiya tunda har an fadi hakan. Bayan fitan shine mommy da hankalinta bai kwanta ba ta daga waya ta kira yaya Abubakar din tace bayan sun gaisa kazo yanzu ina neman ka ta kashe wayan nata. Sai gashi ya kira hankali tashe da alama a barci yake lokacin yake fadin mommy lafiya meke faruwane i hope dai kowa na lafiya a gidan tace kadai zo nace maka yace gani tafe mommy. Ba a dauki lokaci ba sai gashi su Nabila ke fada mai muna part din mu