← Book details Ana Dara Ga Dare Yayi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 108 OF 337

Sashe 108

Ana Dara Ga Dare Yayi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ni kaina yau dana tsaya a gaban mirrow nasan kayan dana saka sun karbeni sosai don yadda suka mayar dani wata preety girl kamar wata cerlebrity din lagos dani saidai inda na rago su na dora dan hijab dina da nake sakawa iya kafada na. Turare idan an min biya shagon nan nake sayen oud a wajen don na koyo shafa turare zamana na kaduna idan ina kusa suka murza zasu miko min in shafa nima a lokacin. Rigan bakace har kasa ta sauka min sai dairin mai fitar da sharp din nan ce ya fitar min da surana fili na ya mace sosai duk da ban damu da hakan ba tunda a ganina ai na suturta jikina ke nan ni ina shiga ta musulunci ke nan a can. Jakkana na ratayo nazo nayiwa umma dake kokarin fita ta bude shago sallama ni kuma na leka dakin Amar na ce dashi mu tafi. Tare dashi muke jerawa mu shiga mota ya sauka a hanya ni kuma na wuce zuwa nawa wurin mun sauke shi ya taka ya dauki hanya muka tafi ina bayan Nape kamar ance dani in dago kai mukai arba da dan gwaggo hari a inda go slow ya tsare mu . Da sauri na kawar da kaina kamar ban ganshi ba lokacin, don wani irin faduwan da naji ga tsoro ya idda kamani sosai da ganin shi din danayi a wurin ina Allah Allah kada shima ya ganni . Duk da nasan ganin shi alheri ne a garemu saidai yanzu da nasan ko shi waye bana son haduwan mu dashi a yanzu gaskiya. Don haduwa zai iya saka ya tunawa mutanen kaduna damu har su dawo su nememu abinda kuma ban so ya faru a gare mu ke nan yanzu gaskiya. Don nafi son sai na fahinci meye dalilin su na sharemu da kowan su yayi don daddy ma bai ko gari da muka bar kaduna din kuma bai nememu ba yanzun da ya dawo. Allah ya taimake ni aka bayar da hannu motocin suka fara tafiya don barin wurin nace wa driver keken da nake yai sauri. Na sauka ina mikawa mai keke kudi naji ance a bayana hello ban juya ba don ganin dawa meshi ke magana balle insan koda ni yake maganan. Na juya zai wuce aka kara fadin hello miss jin hakan yasa na juyo don ganin mai maganan motar suce ta dazun da muka hadu a wurin yanzun ma a bayan mu ashe wani kallo kada ka raina ni nayiwa driver din . My oga de talk to u, wanda ke wajen yace min wani kallo na watsa mai kafin in ce who be ur oga ? Go tellam say , me i don't have business with him, nd i no be those gurl dey are chassing on d street sha . Daga haka na juya na wuce ban yarda na daga kai ko ido na kalli inda shi yake zaune ba din kada yasani zuwan dole wurin. Da dan sauri na bacewa ganin su na shege inda muke daukan lecture na nemi wuri na zauna abina ina dakon malami ya shigo. Har malamin ya shigo ina zaune ina tunanen me yake nema a wurinane wai da yake bibiyata a yanzu don bai rasa sanin dililin da yasa aka jafar damu nan inda muke yanzu. Ina murna na huta tunda nayi masu haka ashe ban huta dashi don kuwa ina sauka bus din school da nakan biyo mu sauka a jaction sai ga motar na sake gani kuma a wurin again. Inda Allah ya taimakeni driver ne kawai shi kadai a motar ba maigidan nasa madam my oga send me to pick you, i dey follow you since u no see me. Wani banza kallo na watsa mai ban tsaya bi ta kanshi ba na nufi wurin da yan nape ke tsayi suna shiga da mutane cikin unguwa direct nace ya wuce dani shagon da nake tsare kaya son kada inje gida ya bini har can. Exacuse na basu na rashin sako uniform dina kuma suka daukan min hakan basu koreni ba a ranan nayu mamakin hakan don basu yarda a zo masu aiki hakn. Na samu an kawo masu kaya shagon conteners suna ta sauke masu haja sai na dauka don shine suka barni na zauna haka ranan dai munsha aiki ga kyauta kuma da muka samu sai sha daya saura muka samu komawa gida da taimakon motan shagon daya kai kowan mu gida a lokacin. Nayi duba a hanyar banga wanan mai bibiyana din ba waishi driver don haka na sake raina na isa gida lafiya da yar jakar dake dauke a hannu na na kayan da aka bamu a wurin. Da shigana gida na samu umma a falo tana jiran dawowana hankali tashe nayi sallama ina cire takalmana tare da fadin umma na dawo sannu da gida umma. Ina kika tsaya yau haka sahiba umma ta tambaya rai bace tana kallona a cikin daure fuskanta gareni dama nasan hakan zai faru nace wallahi umma daga can kada in makara shago na tafi don nasan idan na dawo gida zan iya makara kuma basa son ana makara haka su. Amma ai ya kamata ki sanar dani kafin ki fita ba wai ki barmu haka hankali tashe ba tunda baki saba yin hakan ba. A dan marairaice nace umma kiyi hakkuri don Allah ba zan sake ba insha Allahu tayi shiru tana kawar da kai gefe daya. Anty ekabbo Amar ya fada na dan kalleshi nace dashi how are u Amar ya amsa da fine yana gyara kwanciya inda yake yana karatu ya zube littafi a gaban shi. Ledan shango da na shigo dasu na zube a gaban umma kafin na mike zan shiga dakina in cire kayan jikina. Muryan umma ke fadin yau yaron nan yazo gidan nan bakya nan da sauri na juyo ina fadin wani yaro ke nan umma ? Dan wajen hjy harira kanwar daddy ku na kaduna kece kika nuna masa gidan nan har yazo ? Umma wai ya mustapha kike nufin yazo gidan nan ko wa don dai ban taba nunawa kowa gidan nam ba wallahi ko abokan karatuna kuwa. Shi din nake nufi mana diya nawa kega hjy harira din idan bashi kadai ba shi nake nufin yazo nan muke zaune dashi a falon nan ya dan jima nan kafin ya tafi. Dawowa nayi na zauna nayi shiru ina dan tunane kafin can in dago kai ina fadin umma tun ranan da mukaje wurin wanan Alfa din idan kin tuna munga wani mota baka kusa da itaciyar dake wurin da mutane tsaye suna magana . To sune muka gani a wirin kuma ranan ce na fara ganin shi tun dawowan mu garin nan a ranan na fara ganin shi sai kuma yau da hold up ya tareni hanya mm a gansu suka bini har school din mu ban kuma tsaya ba. Don gaba daya bana son kowa daga wanan bangaren a yanzu gaskiya da kuma irin kashedin da yai min kada na kara nuna nasan shi a ko ina . Shi din ya fadi hakan nace kwarai umma shiya fada min da bakin shi ranan da a kai bukin dinnan diyan gwaggo Asiya din nan . Oh Allah kai kadai kasan dalilin halittomu a cikin wa yan nan mutanen da suke yan uwa a garemu kuma basu rike zumuncin nasu ba a kan mu. Ban iya ba umma amsan komai ba illa dai nayi shiru ina nazari na dade zaune a wurin kafin in mike zuwa ciki na cire kayan jikina nayi wanka. Ban fito ba saida nayi sallah na saka kayan barcina wando da riga sai bakin hula a kaina na cusa gashina aciki na dora zani a sama na fito kitchen na shiga na debo abinci na fito. Cibi biyu nayi sai na kaaa cin abincin saboda tunanen daya dameni a lokacin muryan ummace ke fadin yace zai dawo weekend don haka zaku hadu dashi ke nan kuma ai Saidai idan son samune umma mubar gidan nan kafin weekend din ko don ni yanzu tsoro mutanen nan suke ban baki dayan su . Gara mu kara gaba can inda babu wanda ya san mu, mu zauna kuma zai fi muna don na fahinci gaba dayan su ba kaunan mu sukeyi ba. Kallon da umma keyi mun saina dauka cewa shawarana ya karbu a zuciyarta na har zanci gaba da fadin kinga ai idan sun, , , , , Ashe har yanzu baki da wayau sahiba ban sani ba na dauki wayau na dora maki ashe ke har yanzu da sauran ki ban sani ba To bari kiji sahiba daga wanan gidn babu inda zan kara tafiya kuma sai dai yanzu duk abinda zai faru damu ya faru. Boyon ya isa hakana don na dauka yanzu lokaci ya kusa da zamu baiya a garesu su sanda sanin muna raye a duniya. Bukata na kawai dama ki samu karatun da idon ki zai bude ko kiyi wayau da zaki iya tunkaran su su gane koke waye a cikin su. Har idan ma basu nememu ba muda kan mu zamu nemesu nan gaba idan lokacin hakan yayi a garemu kedai kawai ki kara maida hankali kan karatun ki a yanzu kiyi hankalin da zaki iya tunkaran su akan hakkin ku. Zaman mu a nan shine rufin asirin mu don yanzu idan kin kula bana cikin fargaba irin baya daku haka shi kanshi wanda ya kawo mu wanan wurin nasan yayi hakan ne a bisa wani shiri da yake muna nan gaba . Bawai haka kawai ya kawomu nan ya zubemu ba dole da akwai shirin da yakeyi shima da zai samu mafita a cikin maganan nan. Kuma ina sane daya dauke mune daga can ya gudo damu nan da yake ganin shine maboya a garemu don nan din kusan zagaye muke da gidajen security duk unguwan nan idan kin kula da hakan. Dan nisawa nayi kafin na runtse idanuwana na dan lokaci Allah ya gani duk da tunanen umma na nufin haka ni dai sai hakan bai mun gaskiya. Abincin na dan fara cakula da cibi ina laiwa bakina badon dadi ba ko dandanon shi sai dai kawai don in kawar da yunwar dake damuna
Chapter 108 · 0% Book details