Sashe 320
Ana Dara Ga Dare Yayi Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read
Allah ya kaimu ya fita don ana jiran shi a waje nagane dai koda yaushe shi busy yake da mutane da aiyukan shi dama na saba da ganin irin hakan tun wurin oga Shaaban . Ranan kuma nayini yin baki suna shigowa ganin amarya don haka ban wani zauna a daki ba lokacin saidai masu zuwa idan sun fita zasu fara fadin ance bayerabiyace amaryan gashi bamuga zubin yarbawa gareta ba ai. Akan lokaci nayi sallah na shirya har fatima don yayi min waya mu hadu a can din driver yana nan ko yaushe a gidan idan muna da bukatan hakan. Hudu daidai ba saba lokaci muka dauki hanyar gidan hjy har me aikin nan nawa da yanzu mun dan fara sabawa da ita. Gaba daya yaranta da yan uwanta suna gidan lokacin hakan yasa na gane abu mai muhinmancine ya kawomu gidan ke nan wanan zuwan. Mun shiga an kuma taremu a cikin mutunci tare da jagoran sister muka isa falon hjy suna zaune su hudune a falon har kasa nakai na gaidasu suka amsa muna gaisuwan a cikin mutunci. Kafin na samu wuri nan kasan na zauna da sauri suke fadin haba sahiba a kasa ga kujera dai kya zauna kasa kuma no nan din yayi Mah, na fada. Baifi minti biyar da zaman mu ba muna nan zaune cikin ladabi sai gashi ya iso nan naga irin so da kaunan da yan uwa ke nuna mashi sisters din shine su hudu suka sakashi tsakiya sai shagwaba suke zuba mashi. Haka harya zauna suma iyayyen kamar zasu lasheshi kowa dai mukhatar kaina na sade kasa shima idon shi a kaina yake duk hiran da suke da babban yarsu lokacin. Dan dago kai nayi na gaidashi fatima ma hakan ya amsa a cikin sakin fuska da jin dadi tare da tambayan mu ba matsala ko kai na dan girgiza mai alaman ba komai a lokacin. Sukaci gaba da magana da yan uwanshi wanda mu bamu san me suke fadi ba din ba yaren da muka iya sukeyi ba su can ya dan ja tsuki tare da fadi yana kai fuskan a kan Duban agogo yayi yaja tsuki tare da fadi a cikin yare ita falmata me take jirane bata karaso ba kuma na fada mata yanzuma da zan taho. Sai wajan kamar minti goma sha biyarne sai gata ta iso a cikin kasaita da isa da takama da izza suka shigo falon da yan uwanta dake mara mata baya. Kowa dake falon ya bita da kallo waya takeyi a cikin isa da takama ta kai zaune ba tare da gaisawa da kowa na falon ba, suma yan uwan suka zauna saman sauran kujerun suna gaidasu hjyn a cikin isa. Kaina nadan dago na kallesu kafin na sada kan nawa yadda nake zaune ta gama wayan ta dago tare da fadin gani yare ya fara yi wanda dagani har fatima bama jin me yake fadamata lokacin . Amma kana gani kasan fada yake mata itama amsa ta bashi tare da kallonsu ta gaidasu a cikin yare zaka fahinci akan gaisuwa ne wanan maganan idan kana da hankali yadda abin ya faru lokacin. Fatima ki fita ki jiramu a wurin sister na fada ta amsa da to da sauri ta mike zuwa waje din kowa ya gane me haka ke nufi a cikin turanci na fada. Falon yayi shiru na dan lokaci kafin ya kalli yan uwan nata yace dasu su bamu wuri zamuyi magana fuskan shi a daure. Kamar ba zasu tashi ba don sai wanan ta kalli wanan wacan ta wani ya mutsa fuska tana kawar da kai gefe daya sai karamar ta fara mikewa ta fita. Idona ya tsaya akansu duk abinda sukeyi ina kallonsu lokacin kafin su mike don kallon da yar uwan nasu taimasu suka mike da sauri suka fita ko a nan ma na samu wani hit daga garesu ke nan . Boyayyen ajiyan zuciya na dan sauke tare da dukarda kaina kasa a daidai lokacin muryan hjy mama ya ga hjyn su uncle take sallama ga kowa na falon. Aka amsa mata taci gaba da fadin mun taru a nan ne don murna da samun karuwa yar uwa a cikin kuma abokiyar zama tare da yin nasiha ga juna son a zauna lafiya a taru a rufawa juna asiri tare dayin zama na amana da juna. Excuse me ta fada tana mikewa da waya a hannunta da alama wai wayan zata karba da sauri ya dakatar da ita da fadin koma ki zauna. Wani irin kallo ta watsa mashi kafin tace zan karbi wayane a ban yan mintuna indawo shima a hasale yake fadin a magana kike fadin zaki karbi waya yanzu? Wanan ai abune da muka sani gabaki dayan mu ba tashigo cikin muba a yanzu zata iyane yasa ta shigo don haka meye na wani zaunar damu a nan kan wanan maganan da mama ta fada. Kowa nan yasan me ake nufi da zaman aure ai don haka ita ai ba yarinya bace idan tazo da zaman lafiya matsalan tane udan kuma tazo da wani manufa duk a daidai muke so ni ina da abubuwa a gabana yanzu . Wanan ba zai zaunar dani nan ba muna batawa juna lokaci tashigo gidan ka fine shike nan mu zuba kawai a kan ka nida ita . OK haka kikace tace na fada saita juya wurin yan tsofin tana fadin mama kuyi hakkuri ni zan tafi wanan ba maganan da zaku zaunar damu nan bane yanzu. Tunda baku iya zaunar dani ba kafin ayi auren ku fada min zai kara aure kuji ra,ayina ba yanzu da komai ya faruwa ba ace za a zaunar damu tare ai muna wani nasiha. Zaiyi magana kanwar maman shi ta daga mashi hannu tare da fadin barta ta tafi Allah ya bada hakkurin zama ke sahiba ki zauna lafiya da mijin ki jeki Allah yayi maki albarka ya baku hakkurin zama sauran aka amsa da amin. Kaina dago tare da fadin nagode mama na yunkura na mike tsaye tare da masu sallama na fito na barsu a falon. A yadda na samu su sister a wajen rayukan su a bace da alama sun ji yadda ta fadawa iyayyen su maganganun banza a falon. Gaidasu da zama nayi kafin nacewa fatima mu tafi mukai masu sallama muka fito zuwa gida wurin mota muka nufa kaina na a duke yake ina kallon hanya. Sai naji a dan firgice fatima na fadin gasu fa a wurin motan mu anty ta fada a dan firgice na dago kai sune tsaye suna magana a hasale. Saidai suna hangomu duk hankalinsu ya dawo garemu wani kallo suke muna tun daga nisa har muka karasa excuse me na fada don su jaye a wurin. Sai duk suka juyo suka kalleni lokaci guda a cikin rashin damuwa na karasa wurin jikina saye nake a cikin wani dogon riga ja baja sosai ba rigan kamar feated yake don yana da dan sharp da dogon hannu sai v neck da akaiwa aikin zare na yafa dan kwalin rigan a wuyana. Sai takalmana masu tsini sosai high hill mai tsawo da igiya kana ganina kasan nasan ta kan lagos da kyau ko daga shirina ya nuna hakan duk da gidan saruka danazo Kai tsaye na nufo inda suke din fuska ba sauki zan bude motar saidai basu jaye a wurin ba har lokacin, , , , ,