Sashe 302
Ana Dara Ga Dare Yayi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Kamar yadda su baffah suka shirya duk da cewa ba zancen kashe kudi ko wani abu ga auren mu duk shi mukhatar din ya dauke nauyin hakan. Saidai wanan shawaran bai sa sunyi sanyi a gwiwa ba don suma a nasu bangaren iyayyena sun tanadi irin abinda zasu kai koda shiba zaiyi amfani dashi ba yan uwansa su raba a tsakanin su. Don hakane suka yanka kudi a tsakanin su aka hada har da shanu biyu a matsayin garan da za a kai sai buhuhunan abinci na hatsi da sauran abubuwan daya dace. Sai kuma wani shanun da zasu yanka a nan don daddy sun tsayar da cewa a nan kaduna din za, a daukeni zuwa maiduguri don kowa yasan asalina hade da waliman da duk su suka shirya yin shi. Lokacin da labarin wanan shirin ya fara zagaya danki wasu sunyi na,am da hakan da za aimun wasu kuma sin nuna hassada da bakin ciki a ciki kan cewa ai sunsan inda suke abinsu. Nan lagos dai ba wasu kawayen kirki nake dasu ba sai su yemisi ne da saura abokan hurdana da sauran mutane aka danyi buki irin na al,adan yarbawa nan ma dai anci ansha daidai gwargwa don kima tare da raba abubuwa. Kafin a dauka zuwa kadunan inda muka samu rakiyan abokan arziki na mutunci zuwa kaduna din a gidan daddy muka sauka inda a nan za ai duk wani abinda ya dace kagin ranan tafiyan. Zuwa lokacin zuciyana ya gama dakewa sosai da komai na falwala Allah al,amarin ina bin kowa da kallo su faiza suke kai da komo sune yan buki. Ida naji dadin abin shine duk manyan matan da sukayo min rakiya daga lagos wanda yawancin su ta dalilin Abdul muka sansu masu rikon addinine sosai basu wasa da ibada ga su kuma kamilai ba wani zancen watsewa a tare dasu kallo daya zakai masu kasan cewa su din hamshakai ne na fada. Wanan yasa bakuna suka kara mutuwa a cikin dangin mu kuma sun nuna hali sosai yadda ya dace dama su suna girmama buki ko wani irine. Munyi kwana biyu a kaduna ana bidia irin na hausawa ga kumshi na musanman da aka dauko maiyi tundaga maiduguri da gyara irin nasu hjyn su mukhatar ta turo ta nan. Saboda ta samu labarin irin gyaran da uwargida keta faman yi a bakunan mutane wanda mu nan da mai kunshin ke muna hira na dauki hakan ga shirme a wurina. Amma da dare yayi na kwanta ina nazarin zancen saina fahinci ashe abinda su muniyat da wata Aisha da muke shiri sosai tun dawowan mu unguwar mu ta lagos da muke zama sukewa ke nan har kasan ghana Aisha taje ta kwana biyu ta dawo min da wasu abubuwa saida kyat suka samu na danyi amfani dashi. Hakama nan tun zuwan mu kullun safe da yamma sai mommy ko anty amarya sun tsureni nasha wasu abinda ban san kona maye ba saidai suna cewa na daure nasha abin amarene dai. Kai duniya abin tsorone don a cikin yan uwa aka samu wanda ya tseguntawa wata dangin uwargida cewa tayi hankali dani don ni din rikakkan yar sikiroce ta kwarai. Don sun kawo lefe na bazata da ba wanda ya taba tsanin itin sa don komai ya zama na kallo a ciki saboda an nuna bajinta da nuna halin akwaishi sosai inda zan tafi din. Yan uwa sai sam barka da tubarakallah sukeyi wasu kuma fidin na bakin su sukeyi wai dama irin mu ai hakane muke samun maza mu cafke lokaci guda irin su Nabila and coo. To a nan ne aka samu wata munafukan ta samu ta tsegunta masu wanan zance aiko kafin ace meye sun baza labarin cewa ai matar da ya auro din yar tsafice ita. Har dai labari ya dawo kunnen yan uwar mukhatar din a yadda suka zauna suka tsara komai zakace aida gaskene labarin. Haka dai suka dauki zancen wasu na fadin duk sherin kishine idan ma har manyace ita ai itace daidai da Falmatan tunda itama bin bokaye da malamai take sai su kara a tsakanin su yanzu. Falmata ko haukan karya ta hauwa maigidan cewa wurin bakin jaraban shi gashi ya dauko masu wace zata kasheta ita da yaranta harshi din. Dariya kawai yai mata don shi zuwa lokacin fitinan Falmatan ma ya isheshi a gidan don gudun hakan ne baiso tazo ba kuma gashi duk mutane basu yarda da zancen da suke yadawa din ba sai cewa ake zafin kishine kawai suke fadan hakan. Suma din kwanan su daya a kaduna anyi dinner da aka shirya yi dasu washe gari kuma zamu kama hanya zuwa maiduguri saidai sauki abin jirgi zamu bi zuwa Maiduguri din. Karfe tara muna gidan ya Abubakar da mukai mai diran bazata wanan umurnin ummace da tace dole akaini gidan shi shi matsayin jigona bayan iyayyen mu din. Kowa yayi mamakin hakan don irin girman da mukeba shi yaya Abubakar din na musanman ne don a wurin yarbawa haka abin yake dama idan kaine babba. Haka umma tabi wanan al,adan data koyo a can din sai suke ganin hakan a sabon lamarine a wurin su don ba kowa yasan ma,anan hakan ba lokacin. Durkushe nake kasa a falon nasa inda gwaggo kudidi gwaggo Amina dasu anty Amarya da sukai min rakiya suna zaune saman kujerun falon gidan nasa . Inda sai bin ko ina suke da kallo suna mede baki don yadda aka bar komai na gidan ba gyara ko kulawa wanda wanan aikin macen gidane gyaranshi . Kota gyara ko tasa a gyara din amma ga komai dai an saka na alatun zamani a falon amma ba kula yadda ya dace duk kura ya rufeshi na hammatern da akeyi a lokacin. Yana zaune suna gaisawa dasu gwaggo din sunawa juna yaya dawainiya da baki da sauran abubuwa kafin can ya juyo inda nake zaune ya dan kura min ido na dan lokaci. Kaina yana kasa ni kadai nasan halin da nake ciki a lokacin ko macen da tayi auren soyayya ta kwatanta dani da akaiwa auren hadi na bazata kwatsam banda masaniya a wanan lokacin. Muryanshi naji can cikin kunnena dawani irin kasalalen murya ya kira sunana da sahiba wanda hakan yasani runtse idanuwana a lokacin. Ban iya amsa mashi ba amma haka yaci gaba da fadin yanzu zaki bar umma zaki barmu zaki shiga sabon rayuwa a cikin mutanen da baki taba sanin suba a rayuwan ki. Wanan yasa ni sake wasu irin hawayr masu dumi a lokaci guda karo na farko tun bayan dakewa da bushewan zuciyana kan wanan zancen auren. Ya kara fadin althoug sahiba a wanan fanin nasan baki da matsala saidai shi rayuwan aure wani rayuwane dake tafiya da ilimin zamani na lokacin da ake ciki a karnin da kai aure a lokacin. Mace bata samun riban aure kin sani sai akwai fahinta a tsakanin ta da wanda zata zauna dasu musanman mijin data aure da yan uwan shi. Daya daga cikin matan da mukazo daga lagos dasu da aka hadomu da ita cikin wanan tafiyan tace kwarai kuwa (Na true you talk ) Idoshi ya lumshe a hankali kafin yaci gaba da fadin kina da hakkuri da hangen nisa ga tausayi saidai duk wanan sai kin kara ga wanda kike dashi don shi zaman aure abune na daban ga masu yinshi. Abinda mijin ki baya so kada kiyishi Sahiba wanda yake so ki kara sama da yadda kika iya nayi bincike mai zurfi mijin ki baya da matsala ko kadan a cikin tarihinshi. Don haka ki kwantar da hankalinki ki natsu ki zama dasu na tsakani da Allah don ki samu riban auren ki ki zauna lafiya da kowa kiyi biyayya ga al,adun gidanshi matukar bai kaucewa addinin ki ba. Zuwa yanzu kukana na kasa danneshi don sautin shi ya fito fili wanda shima yanayin muryan shi a yanzu din ya sauya ga yadda yake magana da farko a lokacin. Kije ubangiji ya albarkaci rayuwan auren ki da komai naki ai ba rabuwa mukayi ba tunda zamu dinga waya dake lokaci lokaci. A lokacin na kara karfin kukan nawa ina son in magana saidai ba zan iyaba a lokacin amma sai naji muryan shi yana fadin zamu baki Amirah ku tafi tare na dan lokaci kafin ki bar kasan nan. Don ance zaki dan zauna da mahaifiyar shi kwana biyu kafin ki tafi muma kuma zamuzo insha Allah don muna son zamu dan zauna dasu a kanki insha Allahu. Bayan hakan bai kara fadin komai ba naji yayi shiru da kyat gwaggo Amina dake kokatin dagoni daga zaunen da nake ta iya daga ni sai lokacin na bude dan guntun gyalen dana rufe fuskana kafi suyi aune na fada saman jikin ya Abubakar din daya riga ya mike shima a lokacin ina sake wani irin kuka mai ban tausayi. Tare da fadin brother na fasa wanan aure bana so bana iya barin umma da dan uwana in tafi i don't want dis marrige at all. Bayana naji yana dan bubugawa tare da fadin you most to marry Sahiba haka shine cikar imaninin ki a cikin al,umma aure dolene ga musulmi don sunace mai karfi garemu. Ba abinda zai samu umma ko Ammar don suna tare damu nayi maki alkawarin kara saka ido ga duk wani lamari nasu daga yanzu. Kai na girgiza ina sake fadin No i don't want zamana a gida yafi min wucewa na barsu idan na wuce wani wajen dawa za a barsu yanzu nice komai nasu a rayuwa Ammar ba lafiyane sosai dashi ba hakama umma din. Saida kyar suka samu na yarda na barshi a lokacin muka fito tare dashi yana kara min nasiha jin su kawai nakeyi don takaicin daya rufe min zuciyana. Nazifa dake tsaye bayan kujeran da yake zaune saida taga fitan mu daga falon nasu ta sauke ajiyan zuciya tare da fadin yar iska. Ashe iskancin naki iya nan ya tsaya aje a iske kanuri can suci muna magininki da kyau ai zaki gane kuren ki yar iska kawai ance maki aure wasane dama. Daga gidan ya Abubakar gidan tsofin nan biyu aka kaini dake zaman iyayyen su a yanzu kannen mahaifan ubanan mu ke nan daga nan muka dawo gidan daddy din .