Sashe 34
Ana Dara Ga Dare Yayi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ganin irin kayan da driver ya jibge min a kofan dam gidan namu na ciro kudin shi na bashi yayi min godiya yana fadin daga yau na karbi lambam shi har in muna da sako a cikon gari sai mu baga ya sayo muna ya kawo mu bashi kudin shi tunda yaga mu mutanen kirkine shima bahaushe ne dan uwan mu mutumin jahar sakwato ne shi. Umma tayi mai godiya ta karbi dan katin shedan daya bata mai dauke da layin shi a ciki yaja keken shi ya wuce. Kayan na fara dauka naji umma tace dani Sahiba wanan uban kayan a ina kika samu kudin sayen shi don ba zan fara zargin ki akan wani hali da ban sanki dashi ba a baya har yan amin su amsa min. Wallahi umma duk abinda kikaga na sayo da kudina na sayo shi na sana,an nan sai kuma wanan hjy ta asibiti data ban kudi na hada na karo dashi don kayan ya dauke mu wani dan lokaci. Wani irin kallon mamaki tayi duk da duhun dake akwai saida na gane hakan muryan yan gidan ne da zasu shiga suke fadin ur daughter don come back ? Ta amsa a sanyaye tana fadin ehn she don come back naw thank u for d care suka shige abin su ni kuma na fara kokarin jan kayan zuwa cikin gidan don mai keken ya taimaka ya kai min buhu ukun ta dan cikin gidan kadan ya aje ya tafi. Haka nayi ta wahalan jan kayan zuwa cikin dakin mu har Allah ya taimakeni na kwashe su kaf nakai ciki na zauna ina haki. Muryan Amar ne ke fadin u no buy some tin for me sister i no eat anytin since i de wait for u to come back. Nasan da hakan don son junan da mukeyiwa juna guntun juice din da nasha gidan hjy tace in tafi dashi da naman data saka min a cikin ledan na ciro na bashi sai take away din da na hado muna idan na dawo muci duka na aje a gaban shi. Daga nisa Ladi data tun karo kofan tana fadin yar ta dawo ko umma data amsa mata daga ciki tana fadin gata nan ta dawo wai mota ne bata samu ba ashe sai yanzu. Ta karaso dakin ta hankade labule tana fadin sannu yar nan ya kasuwan da hanya ai dai an godewa Allah tunda kin dawo lafiya. Na amsa mata ina mikewa take fadin yar umma yau umman ki ta shiga wani hali na rashin jin inda kika shiga haka tun safe ? Daga ita har umma dariya sukayi umma ke fadin uhm ina da gaskiyana Ladi kada yar mutane ta bata a hannu na gashi ba mutunci ne ga yan uwan mahaifinta ba. Ladi tace lalai kan a raina nace komai rashin mutuncin su a haka nake son sanin su waye su na bude ledan dana dawo dashi na dauko mata take away daya na bata tare da dan sauran tsaraban dana sayo muna Ta karba tana washe baki tare da saka min albarka buta na dauka na nufi dan wurin da muka kewaye don wanka da zagayawa na yo tsarki nafito na fara alwala har saida nayi rabi ne naji suna wani zance daga dakin don haka na tsaya ina sauraren su Ina alwalan nake jin suna ci gaba da magana ladi na fadin amma dai kinsan yanzu ya kamata ace gida sunsan inda kika shiga da yaran nan don ko baki fada masu yanzu ba nan gaba dole su sani saboda yar nan taki. Don kinsan dai ta fara girma gata da zati kwana biyu zaki fara ganin maza suna sallama a kofan nan din ko yanzu sun fara yi min magana a kanta. Don haka gara ki san nayi tun lokaci bai kure maki ba abinda kike faman boyo a fassara maki shi a wani hanya na daban. Sauu nayi na kasa ci gaba da anbin da nakeyi don ina son inji amsan da umma zata bata a lokacin saidai umman a sanyayye tayi magana don haka banji me ta fada wa ladin ba a lokacin. Haka na shigo dakin jiki ba karfi suna ganina suka canza wani magana har na tayar da sallah nakai rabi ladi tayi mata saida safe ta fice a dakin. Bayan na idar ne na juyo ina gaida umma da wuni ta amsa min tare da fadin ke kinci abincin ne nace yanzu zanci ina son in baki sakon da hjy ta bayar a baki ne. Yanzu Sahiba gidan wannan matar kika je nace eh umma naje naji ya jikin danta don bamu samu komawa asibitin ba a lokacin. Sai na samu dan nata ya rasu ashe a take naji umma na salati a wurin tana fadin yanzu dan nan ya kare ashe Allah ya rahama masa yasa iyakar wahalan sa ke nan na amsa da amin a lokacin naji karfin gwiwan dauko ledan da ta ban na bude ina nunawa umma din kayane na jikin ta da na wanan budurwan dana gani a gidan suka hado muna sai kayan yaron nan daya rasu masu kyau nasan na Amar ne sai da suka ciko min ledan ghana most go baka da kayayyaki a cikin sa. Kayan umma ta shiga budewa tana dan haska dan tocin mu da baida haske sosai saidai haka muke amfani dashi wurin gani da dare koda asuba idan na tashin yin wani abu na sana,an mu rayuwa ke nan. Tun bayan komawan shi masaukin shi yake faman tunane a zuciyar shi wanan yarinyar kamar ba mutum ba duk inda zaka ganta sai tayi ma walkiya ta bata. Towai me ye hadin su da daddy ne ma dayake neman su haka ruwa a jallo ya juya ya gyara kwancinyan shi yana fadi a fili dole akwai wani abinda ban sani ba da su suka sanshi kuma suke boyewa a tsakanin su . Don ga sanin sa ai inma har yan uwane dasu yadda daddy yake zato sun fi kusa da hjyn su ke nan don hjy ce yar gidan ga baki daya bisa ga daddy din dashi su ukune kawai mahaifin su ya haifa kafin ya rasu. Kai abin dai ya daure mai kai a karshe ya yanke shima zai fara bincike alakan da wanan matar data bata da ya"yan ta wace daddy ke nema a yanzu ruwa a jallo. Wayan shine yayi kara daga gefen shi ya dauka hjy ce ya dauka murya a dakushe kamar mara lafiya yana fadin Allah ya bar min hjy ta . Ta lumshe ido tana jin dadin addu,an shi gareta tare da kiran sunan shi ya amsa ya fara gaida ita da wuni. Bayan ta amsa a cikin kawaici da alkunya irin nasu na fulani don a gaban mutane bata sake jiki tayi hira dashi don idon jama,a. Hjy tace mudibbo dama na kirakane akan zancen auren ka kamar yadda kace in duba in zabama wace ta dace dakai . To na zaba na kuma fadawa Alh zabin nawa yakuma yi na,am da zabin shima yaba da goyon baya ga hakan. Ya dakatar da mahaifiyar nasa da fasdin hjy ban fahinta ba don zancen ya daure min kai gaskiya. Uwar tace ai kasan halin family mu dama basu bari a fita a auro matar farko a waje sai a cikin gida don haka a cikin gidan na zaba ma yar wurin Alh Nuhu yayan mu dake zaune a nan kaduna ina dai kasanshi ai. Abubakar ya tsuke fuska kamar mahaifiyar nasa na kusa dashi yana fadin mommy na fada maku ni banson wanan auren hadin naku tun farko. Kuma ko zanyi irin sa hjy sai a rasa gidan da za a nema min mata sai wanan gidan da basu da tarbiya da hankali. Hjy Addah ta dakatar dashi tana fadin wanan ba hujja bane idan ma har bata da tarbiya idan ta shigo gidan ka sai ka koya mata mana. Mommy dan Allah ku bar wanan zancen ku bari ni zan zabo da kaina don ba tsarina bane yan gidan nan. Kai dakata hjy tace dashi don aikin gama yagama ko don Alh ya kira yaya din ya fada mai kuma ya amince da hakan . Don haka yanzu babu wani zancen da zaka bullo muna dashi mu yarda dakai indai ba kasa zaka watsa muna a idon jama,a ba kuma. Mommy ba zan taba hakan a gareku ba insha Allahu kawai dai kiyi tunane akai don yaran gidan nan sam basu dace dani ba. Don sam basu san girman mutane ba basu da tarbiya ko kadan gashi basu da addini na tabbatar ko auren yar gidan nan nayi ba zamuyi zaman lafiya dasu ba. Don abinda sukaga dama shi sukeyi a rayuwan su mommy kinga ashe ban isa in sata ko in hata ba ke nan wani riba ke nan zan samu a karshe ? Don yayan mu ba zasu samu kyakyawan tarbiyan daya dace uwa taba diyanta ba don ko ita bashi ke gareta ba. Mommy nifa ban damu da wayewa ko wani ilimi ba can nafi burin auren mai ladabi da biyayya da natsuwa tare da kamun kai. Jikin hjy ne yayi sanyi tana sauraren dan nata don tasan duk abinda ya fada game da yaran gaskiya ya fada ba karya ko kare kai acikin zancen shi din. Don yaran dan uwan nata sam basu da tarbiya ko kadan tunda tana zuwa gidan itama tana ganin irun rayuwan su da rashin girmama na gaba dasu. Don ko sunje gidan idan ya kama sai iyayyen nasu sun ce dasu halan bakuga wance ba zasu dan gaida mutum a tsaye kamar wani sa,an su can. Dama shi mahaifin nasu ne ya nuna yana son ayi wanan hadin a tsakanin su don itama sam bata da ra,ayin hakan a ranta itama. Ta numfasa har yana jiyo hakan a cikin wayan tana fadin yanzu kai dama wacece wace kake so kuma a ina take ? Duk da ya danji sanyi a zuciyar shi da alama zai iya shawo kan mahaifan nasa kada ayi wanan hadin da suke shirin masa a yanzu. Yanzu kan likafa taci gaba kamar yadda na fada maku mun samu abokan hamaiya a wurin sana,an mu sanin halin yarbawa umma tace na