Sashe 123
Ana Dara Ga Dare Yayi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Kwace nake ban da niyar zuwa aiki duk da yau ya kamata in fita full day nayi aiki dasu amma na gyara kwanciya naja bargona na kara rufa. Umma ce jin shiru ban fito ba yasa ta fito daga dakinta zuwa nawa tayi sallama ta shigo dakin ta sameni ina barcina hankali kwance ba niyar tashi a lokacin balle nayi shirin fita wirin aiki. Kwana biyu ke nan ban zuwa aikin ina gida idan na dawo tare dasu tunda Abdulhamid ya fada min hakan naga kafin su dakatar dani gara na dakatar da kaina aiki dasu din. Sahiba umma ta kira sunana tare da dan tabani kada na dan firgita ina falkawa na bude idona umma tace sahiba yau ba zaki fita aikin bane ga lokaci na tafiya ? Idona na dan lumshe ina fadin umma na daina aiki dasune don Abdulhamid ya tsegunta min kamar zasu koremu a ma,aikatan nan bada dadewa ba. Shiya fada maki haka na kada kai ta sake fadin koda zasu koreku ai zasu baku hakkin ku ko dkn haka ki tashi ki shirya ki fita bana son wani abu ya fito a bangaren ki gaskiya ki bari sai idan sun dakatar dake din tukun. Wani iri nayi da fuska saidai ba yadda na iya dole na dan yunkura ina fadin zan shirya na tafi umma tace Allah maki albarka na amsa da amin. Ban bata lokaci ba don ko banza naji umma tayi min abinda nake so a rayuwana don babu abinda yakai dadi ga yaron daya san kansa koda kuwa karamine yaji uwa ta saka mai albarka kamar yadda umma tayi min. Don yana karawa yaro karfin gwiwa da kuzari ya dinga aiki mai kyau a rayuwa koda kuwa babbane yana son jin kalman Allah yayi albarka daga bakin mahaifa. Wanka nayi na shirya a gurguje kafin in fito har Abdulhamid ya kira umma yana fadin ya ban fito ba kowa na wurin aiki don yau akwai baki da zasu zo muna ma,aikatan. Sai ga umma ina gaban mirrow ina shafa mai take fada min bata fita ba saida ta tsaya har na shirya na fito na samu ta hada min tea dole na zauna nasha na nufi wurin mota na tayar na dan bata wuta kafin inja in bar gida zuwa aiki. Tun daga nisa na gane gaskiya Abdulhamid don akwai alaman baki don motacin da naga iri daya a wurin an jera su har guda biyar manya manyan jeep sai walkiya sukeyi suna daukan ido. Haka na rabasu na shiga da sauri saidai na tsargu lokacin dana samu kowa a haraban wurin tsaye ga wanan matashin na kwanakin baya da akace shine wai mai wurin tsaye yana jawabi kowa yayi shiru. Baka jin komai sai sautin takalmana dake kara a lokacin na ratso wurin daga can baya naja na samu wurina tsaya ina sauraren abinda yake fadi. Turancin shima ko a cikin turawan abin kallone farine sol har yafi ya mustapha fari da kyau da komai saidai tsawone bakai mustapha din ban din shi mustapha har ya dan duka kadan don tsayin shi . Wanan din kam sune tashin falo tutube da remote na gaskiya don baima san wani abu zafin rana ba ko talauci kila a rayuwa. Ba wani abu yake fadi ba sai irin yadda ake sakaci da aiki a wurin ana samun matsala yake nuna baci ranshi da hakan sai a karshe da yace zai dauke wasu daga nan ma,aikatan ya kaisu sabon wurin da aka bude su koma can. Sai kuma ya kara da godiya kan yadda wasu ke aiyukan su tukuru musanman kananan ma,aikatan wurin su yafi yabawa ya kara da cewa su kara karfi ga aikin su yayi hakan ne don a rage zaman banza a gari tafe suka fara yi mai Allah bai ban ikon taba mashi ba ni a lokacin . Don na kagu da tsayin saidai ina dago kai yayi daidai yana kallon inda nake tsaye a takure din cikin shiga na na islama kamar kullun don zuwa kaduna a yanzu ya kara haska min hasken musulunci sosai a zuciyana ba kaman da danake sakaci da ibada ba don talla duk da alokavin ma ina sallah gaskiya. Don umma tana iya kokarin ta wurin haska muna ibada ko lokacin shiyasa bamu sha wani wuya ba a can da mukaje don mun koya a wurin ta. Sallaman mu yayi kowa ya fara tafiya ana kuskus da zantukan da yayi a wurin musaman na kara albashi da yayi alkawari gako wani ma,aikacin wurin har masu gadi don ya yaba masu sosai lokacin jawabin nasa. Nima gyara dan jakar dake kafadana nayi a lokacin naji muryan manager yana tsayar dani ta hanya kiran sunana naja na tsaya yake fadin in sameshi office din shi suna tsaye tare da bakin nasu lokacin. Yes sir na fada na juya zuwa office din mu na aje kayana da yar jakana na fito na zuwa office din su zuciyana cike da zargin dalilin kiran da yake min da safen nan. Har zuciya ta fara raya min cewa shike nan zancen korana din ya baiyana ke nan a yanzu tunda manager ya kirani har office din shi. Na isa na dan tsaya daga waje duk da nasan zasu iya ganina daga ciki tunda glass ne wurin ko wani office din dake cikin wurin. Shigo mana yace min daga ciki na dan tako na bude na shiga da sallama sabo da yin hakan ko ina zan shiga babu kowa a office din sai shi daya yana hada takardu a tsaye na karaso ciki. Kara gaidashi nayi ya amsa yana nuna min kujera in zauna nakai zaune din cikin mamaki kafin ya dago yace dani congrat miss Sahiba. Na dago kai da mamaki ina kallon shi don ban san abinda yake min murna akanshi ba a lokacin sai naga ya miko min wani farin takarda yana fadin. Nayi maki murna sahiba zaki bar wanan aikin damu na dan lokaci duk da dai ana tare din saidai zaman ki ba zai kasance nan na sidin din da kikeyi a yanzu ba. Don idan oga yana gari zaku kasance dashi keda Adnan na dan lokaci don, kun san shi ba mai zama kasan nan bane sai udan yazo bai kuma yin fiye da sati daya ya koma sai dai idan wani abu ya tsayar dashi. Saidai ba wani aiki mai yawa bane ke zaki koma a matsayin sakatariyan shi adnan kuma PA din shi zaku fara aikin ku a goben nan ko ince yau da company n an namu zaku fara zaiyi aiki damu idan kin duba takardan gobe kuma haka har jibi. Shiru nayi ina jin wanan bayanin nasa kamar a mafalki yake min wanan bayane din don gaba daya ban san me zance ba a lokacin. No kada ki shiga damuwa Allah ne ya zaboki ya baki wanan daman don kin cancanci hakan gaskiya mun yaba kwarai da irin kokarin da kike muna wajen warware muna matsalolin da sukaso taso muna har sau biyu muka samu saukin komai daga bangaren ki. Wanan shine ya bamu daman karfin zaboki daga cikin ku don ki taimakawa masana,antun shi da yake dasu a kasan nan . So congrat onces more again da wanan daman da kika samu da kowa yake fatan samun shi a rayuwa son zakiyi aiki da babban mutum a kasan nan kuma matashi. Innalillahi na fada don ga baki daya kaina ya daure ga abinda duk yake son fahintar dani a lokacin. Yanzu suna office don Adnan har ya tafi sun soma aiki a office din shi ko tun dazun a hankali na dago kaina na dan kalleshi zanyi magana ya sake fadin . Idan kina da wani bayani saiki bari daga baya zamu zauna muyi maganan daya dace amma yanzu akwai aiki sosai a gaban ki. Mikewa nayi a hankalin jiki ba kwari kamar kazan da kwai ya fashewa a ciki na fara takawa sai kuma naja na tsaya wuri daya tare da dan juyowa na kalle shi na bude baki da zuman tambayan shi. Ya dago yana fadin you can go now nasan yanzu sun fara aiki ko tundazun bai kai ga rufe baki ba sai ga wani ya shigo yana fadin wai ance ina new sectrery din take tazo ta fara shigar da komai. Muka kalli juna ni da manager kafin naji yace gata tafe yanzu ta tsaya ina mata bayani ne dole nabi bayan shi zuwa inda suke. Daddy ya jijiga kai bayan hjy Addah ta gama mashi bayanin komai yana sauke nunfashi kafan shi ya mike daga yadda yake zaune a kasan. Tsawon dan lokaci bai iya furta komai ba sai can yace yanzu me kike son nayi akan zancen nan ko kin manta da zancen mu na baya ne da mukayi lokacin da kika zo min da zabin yar Nuhu a matsayin matar da moddibo zai aura nace ki dai sake dubawa kikace ai itama din yar gidace ko ban son zumuncin ku da dan uwan ki ya kara kulluwane daga haka na goya maki baya ban kara furta komai ba. Don haka yazu ma runda a gidan kawun modibbo take zaune ai nan da can duka gidane sai ta zauna mana menen ? Wani irin kallo hjy din tayi mai na mamaki don jin abinda ya fada tasan zancen yana da ma,anoni masu yawa ke nan a zuciyan shi. Can yace dama shi modibbo ya kirani ya fada min komai na bashi hakkuri don haka kuma ina nason ku fita zancen ku kyale su a zuba masu ido aga me suke nufi da hakan. Sai lokacin hjy ta dan sauke ajiyan zuciya don jin abinda daddy din ya fada ta koma cewa saidai yaran da ba wanda ya sansu a nan bangaren fa Alh ? Murmushi daddy ya sake yana fadin yara ai dole komai dadin dadewa a kawosu gidan nan idan kunyi hakkuri da hakan. Don ta kan yaran ake son bi a aiwatar da nufin da ake kokarun aiwatarwa a kan mu yanzu nasan waye Nuhu nasan duk wani shirin shi na shirme da jahilci Kai innalillahi hjy ta fada na dauka wanan hadin zai kawo zaman lafiya a tsakanin ku idan anyi sai gashi kuma hakan yana son kawo wani babban matsala