Sashe 279
Ana Dara Ga Dare Yayi Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
gida. Mukan sai kallon su da mukeyi son wa zamu kira yayin da Ammar yake tare da Abdul makale tare dashi suke komai don muna zuwa masauki bamu zauna ba su uncle sukace mu fito mu mika gaisuwa gun manzon rahama don haka muka dunguma zuwa masalaci a lokacin. Bamu dawo masauki ba sai tara na dare don haka kowa ya gaji ya nufi dankin shi don hutu a lokacin ida muke daki daya mu ukku da faiza da fatima. Ba wani hira sosai yanzu mukeyi kamar da can baya ba dasu saboda dan dedewana da akayi yanzun ba a tare yasa akwai dan shakku a tsakanin don sai wani ban girma sukeyi ko kuma idan najasu da hiran zasu dan sake muyi hiran. Diba kuma a yadda yanzu wani irin natsuwa da kamala yazo min ba sahiban da wagar wagar suke gani ba don ko a da dai masifa da fitina yafi min yawa sabo da zaman geto yanzu ko duk ba wanan komai a cikin kamala suke kallon ina yinsa. Saida Nagama duk duk wani shirin kwanciya da zanyi a lokacin na hawo mamaken gadon alfarman dake dakin na kwanta dancan karshen gado da suka barmin. A lokacin ne wani irin natsuwa tare da tunanen daya haifar min da ajiyan zuciya yazo min lokaci guda ina sauke shi wanda ba komai ya jamin hakan ba sai ganin Fa,idan wanan tafiyan da yanzu mukayi. Don addua kan mahaifin mu ya samu a ranan wurin yan uwa sosai duk wanda muka hada ido zai dinga kwararo mai addua da fatan dacewa da rahaman ubangijin gareshi. Ido na lumshe a hankali ina jin kaunan wanan mutumin da yayi sanadin yin hakan a garemu yanzu din don ba karamin kokari yayi muna ba kan hakan. Idan fa nace kauna baiwa kauna na son shi ba a, a kauna dai wanda ke nuna kanayi da mutum sosai a lokacin wanda kake jin wani abu har kasan ranka akanshi don ya zama masoyin mu na gaskiya kamar yadda muke jin ya Abubakar a yanzu. Mun bar lagos laraba alhamis oga sha,aban ya diro lagos din da zuman zama dani da wasu daga cikin ma,aikatan a sulhunta tsakanina dasu. Son haka ya baro daulan larabawa dayaje last ya nufo Nigeria saidai tun a airport Felix ke fada mai ai ban kasan mun tafi umurah duk family din mu lokacin. Mutuwan zaune yayi da mamaki yace ita sahiba din yace kwarai jiyan nan suka bar kasan nan nima a wurin oga jimoh na samu labari. Don har da Abdul suka tafi a cewan shi itace ta biya mai tare da wasu yan uwanta su goma ga mahaifiyar ta da kanin ta kuma. Har oga jimoh yasa ayi bincike ko kudin company ta kwasa ba a sani ba tayi wanan abin haka mai bam mamaki ya kare fadi yana kallon fuskan shi don son jin me zaice shima a game da hakan. Da sauri ya girgiza kai yana fadin no no ba zata taba yin hakan ba na sani dole dai akwai wata kila dai dukiyan nasu ne ya fito suka fara da hakan. Har suka kai gidan shi da yanzu yasha gyara sosai ta ko ina don kullun cikin canza mashi tsari ake koda yaushe. Ga abinci an tare shi dashi amma zaune yake ya kasa wani motsi ya kurawa kasan ties ido kawai yana tunane ya rasa me Alaja take nufi dashi a rayuwa. Shigowan felix tare da oga jimoh falon ya katse mai tunanen da yakeyi din nan suka gaisa oga jimoh din ya kara fada mai yadda mukayi dasu a fili inda yake fadin . Yayi iya kokarin shi sosai kan na hakkura na dawo bakjnn aikina amma na kafe bazan dawo ba tunda har mahaifiyar shi tana ganin cewa cutar shi nakeyi ina amfani dashi dan naci dukiyan shi. Kai ya girgiza wanda hajan rashin yawan maganan shi sosai ne yasa ya zama mashi dabi,a a jikin shi idan yaji maganan da bai gamsheahi ba lokacin. Ya dan zakudo ya gyara zama yana fadin i know who is that girl kudi ko wani abin ba zai rude ta ba idan zatayi abune zatayine idan kuma tace a barshi an barshi ke nan. Don haka ba zamu tsaya muna binta ba tunda kun bita da farko taki a dan saurara mata har zuwa lokacin da Allah zaisa ta sauko ko zata dawo. Don haka ayi gagawan maida wani a matsayin ta yanzu kada aiyukan suzo su tsaya a samu matsala ya fada yana mayar da bayan shi ga kujeran daya dan dago din don yayi magana. Ya dora hannun shi daya saman goshin shi yana dan murzawa a hankali tare da lumshe idanuwan shi daya rufe su lub a lokacin. Wanda ba komau yake tunane ba sai irin matakin da yakamata ya dauka yanzu kan wanan abin na Alaja ya kaishi makura ta yadda ba zai iya kyale hakan yaci gaba ba. Da ace Alaja tasan irin matsayin da yarinyat nan take dashi a cikin zuciyan shi da batayi gangancin daukan wanan shawaran da zuciya ta yabata ba. Tana da kirki tana da mutunci haka tarbiyan ta yayi daidai da irin tarbiyan da yake son samun mace dashi ga aiki tukuru babu ha,inci da cutarwa a cikinshi kuma a duk lamarin ta. Ai baki sani ba Addah ni har yanzu wanan abin bai daina ban mamaki ba kai abin abin daure kaine fa ace wai wanan yarinyat ta kwashi mutane haka zuwa umura kawai gaskiya da sake. Dagowa yayi ya dan kalli mahaifiyar nasa daga inda yake kwance ya mimike saman kujera ko zaiji dadin jikin shi. Don daren jiya ya sauka kasan tsawon wata biyu ke nan baya Nigeria don haka akwai gajiya a jikin shi ga kuma gwaggo hari data tayar dashi wai sai ya fito ya saka wani abu a bakin shi tunda tun shigowan shi yake kwance yana barci. Daga inda yake kwance yana sauraron wayan da sukeyi da mommy hjy Addah baisan me Addah din ta fada ba a lokacin ya dai hasaso zancen don yaji mami din shi na fadin. Kwarai kuwa irin halin sa ta kwaso na son yan uwa Addah saidai ina jiyo masu abinda zai biyo baya gaba sun samu dukiya yanzu sun fara banzatarwa a banza shifa kudin gado haka yake kamar an kyasta mashi ashana dama kafin yazo hannun magada. Sai a lokacin ya fara fahintar ko kan wa suke zancen su saidai bai tabbatar da hakan ba a lokacin kafin yaji tana fadin. Ni fa yanzu a kan wanan maganan ko waya mun daina yi dasu yanzu nikan ai yafi min ma don kada azo ace dama don gadon nasu nakeyiwa wanan rawan kan a kansu . Sun dai jima suna magana inda a karshe ya fahinci a kan wa suke zance bayan sun kashe wayan ne ya kalli mahaifiyar nasa ya jefo mata tambaya da fadin. Mami suwa Sahiba ta daukane kuma ina suka jene da mutanen da kuke magana a kai saita juyo tana fadin kaidai bari the boy. Kaga abinda dama nake gudu ke nan tun wuri ku kuma baku fahinceni ba mutane su fara fadin don naga kudine nake kokarin cinna maka ita ka aura. Kasan ko zasu fada irin wanan facakan arzikin da suka fara haka wai ace sahiba ta dauki mutum goma zuwa umurah lokaci guda haka kai tsaye ai wanan abin akwai ayan tambaya a cikin shi. Shima jin tayi shiru ya jefo mata tambaya da har an mika masu dukiyan nasu ne ko haka ya tambaya yana kallon fuskanta ? Wanan kuma ban sani ba har in an basu gaskiya banda labari kuma da an basu din aida naji kuma koba gaskiya ba wanan abin nasu aiba a boye yake ba kowa yasani. Haba mami kin gani gashi kin ba kanki ansa yanzu cewa ba a basu ba amma kuma kuke masu wanan zargin haka why don Allah mami kika canza hakane yanzu ? Ya kamata ku tausayawa mutanen nan da ace kunsan irin kaskancin rayuwan da mutanen nan suka gani a rayuwan ba zakuyi masu wanan abin ba yanzu. Kudai maza haka kuke ga gaskiya mutum na gani amma sai ko rufe kuce mutum baiyi daidai idan bashi ba ba za a tsaya aji inda kudi ya fito ba sai a hau murna cewa wai tayi kokari. Na fahinci yanzu don na furta ina son yarinyar nan kika taane su hakan ga amma idan ba haka ba ai da can naga kina tausayin su sosai ba kamar yanzu ba. Duk abinda zaka fada ni ina nan bisa kan zance na ba zakasa mutane su zage a banza ba ko ka dauko min magana a cikin zuria ta. KLlin mamaki yake jifan ta dashi don ya kasa gane mai take nufi har yanzu don kawai yace yana son sahiba din ne wanan abin ko kuma wani zance ne a kasa daban ? Shiru yayi ya mayar da hankalinshi wurin tv dake aiki saidai zuciyar shi fam yake da tunanen me hakan ke nufi har zan dauki mutum goma zuwa umarah.