Sashe 133
Ana Dara Ga Dare Yayi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
irin takaicin ta da nake ji a raina yanzu don gaba daya ta zube min ga gani. Itako ko a jikin ta bata dauka ta fadi wani abu mai muni ba ga hakan sai kokarin jana da hira takeyi nayi shiru ban bata amsa take fadin wai kinsan irin tsadadun mazan nan kaza da kaza can abakin ta dai ita ta iya fadan maganan banzan ta. Gabin ba zata fita ba yasa na mike ina kokarin shiga bandaki take fadin naje na fito zata zauna ta jirani nan kan duk da ta girmeni da komai. Na rufe idona na nuna mata hakan ba zai yuyu ba ta fice dai kawai don ni bana yarda da irin hakan itama mamakine ya kamata take tambayana don ban yarda da ita bane ko me yasa na fadi hakan. Nace no sirinane haka kuma addinina bai yarda da hakan ba gaskiya don haka ta fice kawai zai fi na shiga wankana. Fushi tayi ta mike ta fice fuuu na mayar da kofana na rufe ina jin takaicin ta har kasan raina. Wankan na shiga nayi bayan nafito na shirya a cikin wani dinki half atamfa gaban kuma material ne sai duwatsun da akai kwaliya yana daukan ido ina jiran inji sunce mu fito mu tafi sai ga sako wai ba jirgi a ranan da zai tafi lagos sai gobe. Da sauri na dauki waya na kira umma muka kara gaisawa take tambayan ko zamu tasone nan dai na bata labarin abinda ya faru garin ta dafe kirji tana fadin mun godewa Allah bai shafemu ba ashe. A karshe sai cewa tayi dani sai ki shirya kije gida ke nan ki gaidasu don kada inja zancen nace to umma idan naje zan kiraki ai. Barci na kwanta nayi a dakin na kuma samu nayi sosai don sai bayan karfe biyu na tashi nayi sallah jin fita daga wajen wurin nayi na dan yafa gyalena na fita. Wurin shuke shuke na hango da farararen kujeru na nufi wajen hankalinane ya dauke a wayana dana zauna ina karanta sokonni. Naji ance dani a bayana hello na dan dago da sauri don ganin waye Adnan ne a tsaye ya saka hannayen shi duk biyu cikin aljihun wandon shi. Ashe kema kina nan ke nan ya fada na fito yanzu ne ina kallon garin garin yana da dadin yanayi sosai zanso na dan shiga garin na zagaya sai dai ban san inda zan tafi bane. Muje mu taka kaga garin na bashi amsa muka fito daga cikin hotel din muna takawa kawai sai na tare taxis yaji na fadi sunan unguwa nace a kaimu as a drop ina hausa da mai Napep din. Yace sai dubu biyu nace zuwa da dawowa 1500 idan zaka kaimu Adanan ya kura min ido har muka gama magana da mai a daidaita din muka shiga naji yace so you can speak that language abi nayi murmushi. Wani shago na hango daga nisa nace my adaidaita din ya kaimu can muka fito na shiga na sayowa Fa,iza fatima da Amira kaya kala bibiyu da kayan kamshi. Muna barin wurin na ciro memo na rubuta sunan kowa don haka kawai naji hankalina bai kwanta da in shiga gidan daddy din ba don ban san manufar su akan mu ba. Da kwatance har muka kai gidan daddy din gidan nan da kyaushi yarda na barshi a baya daga dan nisa kadan muka tsaya na sauka na nufi get din gidan na kwankwasa maigadin ya leko ba malam Adamun dana sani bane a baya wanan din. Mun gaisa nake tambayan shi don Allah ko Faiza tana gida Amira yace suna ciki nace ka karbi wanan sakon ka basu ina gaidasu ina saurine ba zan samu shiga ba. Na bashi dubu biyu sabbi nace ka karbi wanan ka rike ina gaidasu na juya yace boyar Allah ince waye idan an tambayeni nace kace Sahibace daga lagos. Muka juya muka wuce nace mubi ta gidan ya Abubakar gidan yaso bace min don sauyin da akai masa amma muma duk da haka na sheda gida. Kofan get din gidan a bude yake na ja gyalen kaina na rufe fuskana dashi ganin wata mota zata fito a gidan shima bin mu yayi da kallo ganin muna kallon gidan nasa ya fito ya nufi gidan su su gaisa da mommy da daddy. Nake cewa Adnan gidan blood brother dinane wanan gashi nan ma zai fito na fada shine kallon daya kamamu muna masa din. A can gida kuma daya isa ya samu duk ilahirin gidan a waje har iyayyen su mata suna mayar da fadi ya shigo da motan shi yai parking ya fito. Sin kasa hakkuri Fa,iza da hauwa da Fatima suka tako har inda yake suna fadin wallahi yaya Sahibace tazo gidan nan taba da sakon nan akawo cikin gida ba zata samu shiga ba ita. Kai nifa na fada maku kila fatalwane ko aljannun ta sukayi shige da ita suke son su rudemu kawai. Aljannun kuma mommy Sahiba dince dai tazo koni na ganta jiya da dare wurin comferences din nan da akayi har aka dasa bom a wurin. Saidai kawai a yanzu dahiba ba Sahiban da muka sani bane a baya gaskiya koni ta bace min kama dai nayi amfani dashi na gano cewa itace sai yanzu kuma da naji wanan din na kara tabbatar da hakan ita dai din nagani jiya ashe. Cabdijam Nabila ta fada daga inda take tsaye ta rike kugunta da hanayebta biyu tace hala yaya ta zama rikakkan bariki ne yanzu ko yasa har ka kasa gane ta. Dama na fada ai wallahi yar barikice sosai bata da kunya ko tsoro ko kadan wallahi daganin Sahiba irin yan iskan lagos din nan ne dama. Ke ja can da maganan banza kina zargin yar uwan ki ga banza to bari kiji indai sahibace a yanzu duk ta fiku aji da sanin duniya don banga wani abin asha a wurin ta. Mamaki na daya yanzu shine yadda akayi sahiba ta samu wanan matsayin haka babba na sakatariyar wanan mutumin da suke aiki dashi dana gamsu jiya don ba karamin matashi bane a cikin kasan nan shi . Ita Sahiba din mommy ta tambayeshi a cikin mamaki yace kwarai mommy wallahi sahiba a wani matsayi take yanzu dako mu maza sai anyi da kyar zamu kai hakan . Aikuwa dai don ga alama nan ya nuna hakan cikin wanan sakon jifa wanan uban kayan masu tsada data aikowa yaran nan yanzu dashi. Kada kayi mamakin hakan tunda mace ne ita kuma ko banza dama sahiba mace ce sosai idan ta samu wuri wahalane dama ya boye siffanta na kwarai. Kai haba haba mommy bai kamata aji irin wanan kalamin a bakin ki ba yanzu don Allah a kan yaran nan don kusan daya take damu ai a wurin ki. Yana fadin haka yasa kai ya shige cikin gidan ya barsu nan tsaye wajen kafin Nabila tace dashi mu kara ganin kayan Fa,iza tana karban ledan a hannun ta. Mommu kan ta juya ta shiga ciki ta samu danta da take nema ruwa a jallo akan maganan shi da matar shi da aka sake samun matsala akan fitinan su. A waje muka samesu tsaye suna neman mu don an duba dakunan mu bamu ciki sai gamu mai adaidaita ya sauke mu Adnan ne ya biyashi kudi yana godiya ya wuce. Mr Jimone ya tare da fadin ina muka fito ba tare da sanar da mutane zamu fita ba hankalin mutane ya tashi ga rashin ganin mu. Kai tsaye nace dashi sorry sir na tafi wurin yan uwana ne da mr Adnan dayace bai san gari ba lokacin kuma ba kowa a wajen da zamu fadawa zamu fita. Cikin mamaki yake kallona kafin yace yan uwa ke kina da yan uwane a nan kaduna din ya sake tambayana a cikkn mamaki yana kallona. Kafin inyi magana Felix ne yace ai ita din yar nan garin ce mahaifiyartace ta fada min haka jiya da naje daukata gidan su har tana fadin sai ta kwana a gidan su idan ba matsala. Shiru yayi ya juya cikin bacin rai yana fadin don't repeat dis mess again kun tayarwa mutane da hankalin kun kuma san garin ba lafiya ana ta fada a kafafen labarai tun daren jiya. Lokacin da muka juya muka hango ogan mu tafe wurin da muke yemisi tana bayan shi tana mashi surutu ya iso mr Jimo ke fadin sir wai ashe ita din yar wanan garin ce dama. Really kawai ya fada ya nufi wurin motar shi kai tsaye yana fadin zai fita ba zai dade ba zai dawo budan bakin yemisi sai cewa tayi sir can i follow you ? Bai ko kallota ba ya shiga mota ya fita mu kuma muka shiga cikin hotel din kowa ya nufi dakin shi don yin laluran shi. Sallah nayi na fito sai ga Felix ya turo sako akan mu shirya zamu wuce zuwa jos mu kwana a can daga jos zamu wuce lagos gobe da safe akwai jirgin lagos a can. Haka muka shirya a gurguje muka dauki hanyar jos da yamman nan wai ashe mahaifiyar ogan namu yar jos ce ita dama saidai tana waje a lokacin. Sai mahaifanta kawai ke zaune jos a yanzu wanan tafiya kan gaskiya an dai yishine ba a cikin dadin rai bakan don tafiyan yazo muna da akasi kuma bamu ba duk wanda yai tafiyan alokacin ya samu matsala arewa ke nan abinda suka sabayi a kaaashen yare ayi lafiya a watse lafiya an kawo arewa an watse baram baram kowa yana neman mafita a lokaci ya tsere. Mun isa jos ana sallah magariba kai tsaye wani gida naga mun nufa mun samu taro sosai a gidan wajen masu gidan da alokacin bamu iya tantance su. Mu mata cikin gida aka kaimu direct mazan bamu san isalin su ba a waje na daiji ana kwalawa wata kira da mallam gasu sha,aban din sun iso a cikin hausa. Daga cikin dakin akace au har sun karaso sannun ku da zuwa wace ta fito din tsohuwace sosai ta tsufa amma gata ya hana ta duka irin na tsufi. Ganin mu, mu kadai yasa taja ta tsaya tana fadin ja,irin shi yana ina shi kuka