← Book details Ana Dara Ga Dare Yayi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 14 OF 337

Sashe 14

Ana Dara Ga Dare Yayi Part 1 Complete Hausa Novel · about 10 min read

KADUNA
Tsayawa Alh yayi saida yaga fitan hjy karima gidan don bai iya jure cin mutuncin da ta daukowa kanta a gidab nasa yanzu.
Wurin motar ta ta nufa tana fadin Asmau kina ina wai kin san mutumin nan yau korata yayi a gidan sa kuwa ?
Gani nan zan fito wallahi ban san inda zan dosa ba tunda ba gida naje ba dazun din kuma yace lalai dole inje gida a yau.
To ki tafi mana wani wuri zaki ba gidan ku ba tace tana tayar da mota to idan naje gidan me zan fadawa iyayyena shi nake tunane a yanzu.
Ki je gani tafe gidan naku asamu ta fada kai tsaye kafin tace yaran fa yace kada in fita da kowa a cikin su suna can na barsu ciki dole.
Wanan mutumin fa sai munyi da gaske a kanshi wallahi inba haka ba wanan munafukan tsohuwar matar nasa zata fitar dake a gidan kina ji kina gani kibar mata yayan ki ta bautar dasu.
Wallahi basu kai min can ba dukkan su kuwa ta fada a hasale kafin taja tsuki ga maganan da Asmau ta fada a karshe tana kashe wayanta.
Taje gida sai ganin ta akayi kwatsam ta shigo da kukan muna funci hankalin mahaifiyar ta ya tashi sosai a wurin.
Tana tambayan ke lafiya kike kin shigo kinawa mutane kuka haka ai sai ki tsorata mu ga hakan.
Cikin kuka tace mama cewa yayi in zo gida uwar tace ya dawo ne ko daga can ya bugo waya yana fadin haka.
Ya dawo umna don kawai bai sameni a gida ba naje aurin barka shine na dawo yace kada inyi girki inbar masa gidan sa.
Wanan ai daji wani sherine aka kulla a hakan amma haka kawai daga dawowan shi don bai sameki ba zaice wai kizo gida kuma fa mama cewa nayi gida nazo amma bai yarda ba ta kalli uwar.
Keko ya raina gidan namu mana ya manta a dai ya nemeki har ya aura kika hayayyafa dashi.
Kai kai tir da wanan halin mahaifin hjy karima dake fitowa daga bandaki yake fadan haka da buta a hannun shi yana kallon su.
Yanzu ke kande da zaki mata fada kan abinda ta aikata ba daidai bane tunda kin sani amma kike fadan wanan ga yarki da tayo ba daidai ba.
Shin kinsan girman zunubin da kika aikata ga hakan ko karima malamai da masana sunce da mijin mace yayi tafiya ya dawo gida bai samu matar shi a gida ba .
Gara ya samu gawan ta ace ta mutu da yasamu ta fita bada izinin shi ba ya fada yana binsu da kallo.
Ba komai ke damun ki ba karima sai shegantaka irin wanda kikaga uwarki tanayi a gidan nan ya kawo hakan.
Yanzu malam ni meye laifina a cikin zancen nan da zanka dauki laifin ka dora min nima ai idan nasan ita keda laifi nima ba zan kyaleta ba ai tunda mijin ta shine komai namu a yanzu.
Don haka ba zanso ta saba ba saidai a kan wanan dan zancen kawai zai turo muna ya gida da yamman nan.
Shine namijin kwarai malam ya fada yana kaiwa zaune bayab ya gama kallon iyalin nasa yaci gaba da fadin idan bai turota gida ba a yanzu ai ba zamun san abinda take aikatawa ba din.
Tabar gidan mijin ta bada izinin shi ba ta tafi wani wurin da ba wanda ya sani koke kin san inda ta tafi ?
Yarinya tayo laifi tazo gida ta kawo kara ba za a tsaya ayi bincke ba a bata laifin ta don gobe kada ta kara sai kawai a mara mata baya karshe auren ya mutu
Sai daga baya azo ana da an sani mafi yawan auren dake mutuwa a yanzu sakacin kune na iyaye daga dan magana kadan sai zancen saki ya biyo baya an bata goma daya bai gyaru ba irin wanan hasalan banzan da yanzu kikayi.
Yar kice mai laifin amma kina kokarin daukan laifin ki dora akan wani can da baiji ba gani ba har kina fadin wai ba banza bane wanan abin .
Idan ba banza bane shegan takane ko me yanzu yarinyar nan bata rasa ci ba bata rasa sha ba a gidan mijin ta amma don jin dadi har zata sa kafa ta fita bada izinin shi ba.
To ai malam ni ba nabi ta nata bane ganin zancen nayi dai ba wani zance bane wanan ya dago yana fadin agareki yake ba komai ba shi da yasan kansa ai kinga ya dauki matakin daya dace.
Nan dai yayi ta fada har akai kiran sallah ya fita ya barsu a wurin kamar jira asmau keyi ya fita sai ga sallamanta ta shigo gidan.
Da sallama sama sama tana fadin shi wanan tshon me yake nufi da zai turo ki gida a yanzu don kawai kin fita baya nan.
So yake ya mayar dake matar gida matar kulle irin kidahumar matar shi ko me da zaizo ya tayarwa mutane da hankali haka ne.
Nima shi nagani yar nan amma malam ya tatare don yana na miji dan uwanshi yace kada ai maganan wai karimar ce bata da gaskiya.
Humm baba baisan komai ba wallahi mama idan kinji tarihin uwar gidan nan nasa sai kin san karima bata gane ma koma a gidan nan.
A ko banji ba ai naga yadda take shimfida iko da idona don ko yayan data haifa iko take da abinta balle wani.
Indai zaku tashi tsaye idan kuna son zaman ta gidan nan wallahi ku tashi don in ba haka ba kuna kallo zata koma bora da karfi da yaji a gidan.
Aiko ba akai ga hakan ba don duk inda zan shiga in fita a gidan nan sai nayi don yata ta kafa nata gwaunatin a gidan.
Mama ni ba wanan ba kinga wanan dan nasu da suke ji dashi kamar kwai duk ilahirin zurian su yanzu kowa jinsa yake idan yana wuri ba a kallon kowa bayan shi.
Ba kinji ba mama dama irin matan nan ai ba kansu suke asircewa ba har da diyan da suka haifa sai sun nema masu farin jini.
Amma idan kaji Allah a bakin ta sai kace yar wani shehi ce ita wurin kawowa mutum Allah kusa.
Sallah da basuyi ba ke nan akan lokaci daga uwar harsu suna zaune suna kullin sheri a daidai wanan lokacin kuma hjy Addah tana can saman sallayanta ta mika bukatan ta a wurin Allah.
Har aka kira isha,i ta tashi ta mike ta gabatar ta dan dade a zaune tana addua kafin ta fito don shiryawa maigidan abincin dare akan lokaci tunda tasan baici kome mai nauyi ba tunda ya shigo gidan.
Saida ta gama shirya komai ta koma dakinta ta yi wanka ta tsula kwalliya kafin ta fito daga dakin.
Lagos Ajagule ruwa sahiba ta mika ma Amar dake kwace ya hade maganin data bashi kafin ta juyo kan mahaifiyar nasu da ledan maganin da ruwa tana kokarin barewa umma din nata.
Duk uwan na kallonta tana faman sake sake a zuciyar ta kafin Sahiban ta juya ta dauko ledan abincin da aka bata din ta fara budewa a gaban kanin ta data tayar dashi yasha magani ga abinci kuma duk da bata san wani kalan abinci bane a cikin ledan.
Tana budewa wani kamshi ne ya daki dakin sai da kowa ya kai idon shi kan miyan kafin itama ta dago kai ta kalli mahaifiyar su tana fadin.
Umma wanan abincin zaikai dubu biyar fa ko yafi haka ji irin girman naman dake cikin umma ta dago tana nunawa uwar miyan.
Kallon da mahaifiyar ke matane ya dakatar da ita daga maganan da takeyi din Sahiba uwar tace sai diyar tayi kasa da kanta cikin ladabi.
A tunanen ki idan naso mu rika cin wanan ko yanzu da banda lafiya na gaki ba nasan zaki iya kawo muna abinda yafi wanan din ma idan munso hakan.
Sahiba bata gane inda uwar ta dosa da zance ta ba sai da taji uwar mu matane kuma cikin bariki muke rayuwa muna da hanyar yin hakan ko karfina ya kare ga naki a yanzu.
Saidai ni ba abinda ya kawoni nan ke nan jin dadi na banzatar da rayuwaba da naku ba nazo nan ne nabaro yan uwa da kowa nawa don wani dalili mai karfi a garemu baki daya.
Saidai me idan kin fara ganin irin hakan dole ne duk ki yarda wanan tsarin namu na baya tunda naga kinga wanan kina farin ciki a yanzu.
A , da farko naso na hana ki cin wanan abincin amma daga baya da nayi tunane sai nagane gaskiya Allah ne ya tsaga hakan yau a garemu ya kawo muna wanan kyautar a matsayin abincin mu.
Amma said, sa hakan bai kwantar min da hankali ba don na kula a yan kwanakin nan abubuwa sun soma faruwa dake Sahiba.
Don tun ranan da kika zo min da kudin nan hankali ba a kwance yake ba yanzu dake don gaba daya na shiga rudani duk da ina da yakini kan irin tarbiyan dana taso dake a cikin shi sai dai dan adam ba ai masa sheda da sai ince ke din ba rokon shi kikayi ba don kinga halin da muke ciki.
Ki tsare kaki ki tsare mutuncin ki tsare marta ban gidan da nawa don Allah kin soma girma sahiba ki kula da rayuwan ki sosai fiye da yadda kike tsare a da can baya.
Jikinane yayi sanyi na kai kasa dabas na zauna ina sauraren umma din tana fadin garin nan duk yan kazo nazone a cikin sa kinga ba wani kwaba a nan .
Ni kaina maza sun sha kawo min hari Allah na kareni da yake sun iya dadin baki idan suna da bukan mace sai i lokaci guda duk zokimmm.m..m. n da nakeyi inci wanan ..... mmm. abincin ya kuma fice min a raina.
Sai da kyat na iya dan cakula muna ci umma na kara muna nasiha a bayanen akan zaman duniya a garin lagos din karshe na tsame hannuna a hankalin dan yanayin da nake jin kaina a lokacin.
Hannu na tsame na mike umma ta bini da kallo sai a lokacin na tuna da zancen kudin dana samo wurin tallan ruwa.
Tsorone ya kamani na yadda zan nuna mata wanan kudin dake hannu na a yanzu ba yadda na iya tunda ba yadda zanyi dasu na ciro kudin daga cikin aljihu tare da kiran sunan umma din sai kuma nayi shiru.
Kudin dake rike a hannuna ta kalla kafin ta mayar da wanda bakon fuskan gidan hayan mu ya bani suna aje saman tabarma a gefen ta.
Nan dai nayi mata bayanin komai akan kudin ta karba taba bina da kallo kamar na tuhuma hancin ta takai kudin kafin inga ta cire da sauri tana fadin.
Wanda ya baki wancan kudin ranan shine ya kara baki na yau din kuma don kamshin turare daya sukeyi da wancan din.
Cikin dan marairaice nace wallahi umma bashi bane asalima wanan din ba bahaushe bane kuma yana cikin mota mai kyau sukace na bayar da sadakan ruwan ga mai bukata .
Ya akayi idan bashi bane kudin suke kamshin turare daya da wancan din daya baki dole maishi bibiyan ki yakeyi ke nan sahiba.
Idan ko hakane ya zama dole mu bar wanan unguwan mu koma wani unguwa can mai nisa mu zauna ta yadda ba zai gane inda muke ba kuma.
Bakina yayiwa umma wani tambayan da banyi niyar mata shi ba a lokacin take yanayin umma din ya canza a lokaci guda har cikin ta yana dan shock don tambayan don cewa nayi.
Idan hakane umma ki kaimu Arewa gidan uban mu zaifi muna wanan yawon hayan muna zama da arna.
Sai kuma na koma dana sanin yi mata wanan tambayan don ni kaina abindake cin zuciyanane ya fito fili a lokacin.
Don legas din garin kazo nazone da ai daba haka ba da yanzu na fara shan gorin hakan a wurin mutane sunan babu abinda ya damesu da zancen wani ina ubanka can wa mutum.
Chapter 14 · 0% Book details