← Book details Ana Dara Ga Dare Yayi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 57 OF 337

Sashe 57

Ana Dara Ga Dare Yayi Part 1 Complete Hausa Novel · about 3 min read

ta kwana da umma sai sambatu take sakewa na fitan hankali a lokacin Ladi tana faman bata baki. Jikin dai na umma yakiya shawara aka ba Ladi cewa takai umma asibiti dole haka suka shirya zuwa asibitin don a cikin sambatun umma tana fadin saida naja kunnen yarinyar nan. Akan mutanen nan da take gani kamar son Allah da Annabi suke mata ni nasan da wata suna neman rayuwan tane kawai ga hakan. Kinsan dan yau da rashin jin magana amma sai yar nan bata yarda da hakan ba take karbo abinda suke bata din. Jin hakan ya karawa Ladi karfin gwiwan su tafi asibiti suga likita kada wani abu yazo ya samu umma din a yadda take kwance haka. Sun fito yan gulman unguwa suka shiga fadin wai akan yarta budurwa take wanan haukan haka yanzu yarinyar nacan tana holewan ta ita tana nan tana hauka haka. Yanzu ma wa zai tsaya wanan haukan kan yarinya ta bata idan ba gawan ta aka gani ba tana can wurin wani ya dauketa suna jin dasin su ko kuma ta hadu da yan Yahoo ta jona dasu a cikin gari. Kowa dai da abinda yake fada akan wanan maganan a unguwar namu don halin da umma suke ciki na tashin hankali. Ladi kan dole itace ta tsayawa umma din tunsa ba kowa ke garemu a unguwan ba daga Allah sai ita ladi din muka sani. Suna adibitin kuma sai gasu sun sameta a can asibitin sun shiga sun fita sunga likitan da umma ke kwance asibitin nasa sun fada mashi dalilun zuwan nasu. Sai gasu an kawo su har dakin da umma din take kwance suka duba jikin ta a haka kuma suke mata tambayoyi kan rayuwan ta take dan basu amsa sama sama. Ganin ba zata basu hadin kaiba ne suka fito fili sukace da Umma din matukar tana son yarta ta dawo hannun ta sai ta fada masu duk wani abinda suke bukatan ji a wurin ta din. Dole umma ta natsu jin hakan ta fara fada masu dan wani abu game da abinda suke tambayanta din da suke son sani. Shi da kanshi ya nemi sauyin asibiti ga umma din ya sa aka kaita wani mai tsada wanda yafi wanan din da take kwance a lokacin. Sai abin kuma yabawa umma mamaki a karshe don yadda ake kula da ita gashi ance sai idan ta kwantar da hankali za a kawo mata yarta. Dole umma ta daure tana shan magani yadda ya kamata a lokacin don dai kawai na dawo gareta gashi har dan sanda aka aje a kofan dakin da take ciki kamar wata mai laifi babba can da aka tsare. Ko wata matar babban dan sanda ko soja a cikin kasan nan don irin yadda ake nuna mata a lokacin. Yayin da ni kuma na rame na koma kamar wata zarara a dakin da aka kullemi din duk da bamu da gata sai na Allah amma sai gashi Allah yasa mun samu kulla daga masu farautan mu din a yanzu da bamu san dalilim halan da ake muna ba. Hankalin shi kwance kuma duk yasan abinda ke faruwa damu din daga umma dake asibiti a kwance har ni dake rufe a wani dakin cikin hotel din da ban sani ba. Umma ta samu sallama don haka suka koma gidan Ladi inda muke da zama a cikin damuwa har lokacin zuciyar ta yake, Hankalin shi kwamce ya gama duk wani shiri da zaiyi ban tsaya jiran wani zance ba sai zancen zuwa gidan da zaiyi gobe din. Kuma da wanan yarinyar zai tafi aje a yita su kare a wuce wurin idan sunje zaiyi duk abinda ya kamata ace anyi akan zancen yaran nan a yanzu. Ya fahinci cewa ita kanta umma akwai wani boyayyen sirin da take boyewa wanda bata son wani yasani a yanzu.
Chapter 57 · 0% Book details