← Book details Ana Dara Ga Dare Yayi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 165 OF 337

Sashe 165

Ana Dara Ga Dare Yayi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Bayan fitan su dole nina tsaya don dama hakane muke dan shirune ya biyo office din kafin can na dago kai da sauri ina fadin breakfast Oga ya gyada min kai alaman a kawo mashi. Ruwan tea ne sai cake na kawo mashi don nasan ko cake din sai kila yaci hakan da nayi mai yasa ya dan ji sauki a zuciyat shi sosai don rabon shi da abinci tun karyawan da yayi gida kafin ya tasone a cikin shi lokacin. Ganin ya kurbe dan ruwan shayin sai dan kadan ya gutsuri cake din ya barshi nan nake fadin na kara mai ruwan zafin ne yace no barshi da sauri yaci gaba da aikin da yakeyi a cikin computer shi. Jimo ya kara dawowa da wasu takardun dayayi aiki a cikin su sun dan dade tare suna magana kafin ya fita Felix ma ya shigo da nasa. Bayn fitan felix din ne na shigo na samu ya hada kanshi da tafin hannayen shi biyu ya dukar da kai da gani yana cikin damuwa sosai. Sai kuma hakan nima ya dameni don ban taba ganin shi a cikin irin halin nan ba haka mutum ne mai nuna jajircewan shi ga komai lalai wanan abin ba karamin abu bane a wurin sa. Dan satan kallon shi na sakeyi har lokacin bai dago kan shi yana a yadda na sameshi zaune din sai nayi tunanen ko barcine ya samu a hakan na juya zan fita naji yace kina son wani abune ? Ya dago manyan idanuwan shi ya sauke a kaina dama nace ko ayima odan abincine ka danci na fada cikin sanyin murya. Murmushi naga ya dan sauke irin na gefen fuska din nan mai nuna ina cikin wani hali yace tea din da nasha is ok don ban iya cin komai a yanzu suna son suga bayana Sahiba . Yau laifine don nakai abu a kasan haihuwan mahaifiyana suma su karu damu su samu ashe hakan yin laifine a garesu. Sun mayar da dukiyana abin wawaso an rasa gane inda kudin ya dosa ko ya shige har suna kawo min shawaran na sayar da wurin ga wasu ki duba min mutanen sahiba. Nayi mamaki kwarai da karfin hali irin na dan arewa a nan shiya nemesu da abin arziki don kasa ta karu dashi sukuma suna neman ganin bayan shi a yanzu din. Tausayi ya ban sosai ganin yau yadda ya tsaya yana ban labarin abindake damun shi kamar wata yar uwanshi naji a lokacin. Yasa har na kai ga bude baki ina fadin halin dan Adam ne oga ko naka sai a hada kai dashi a cutama indai dan arewa ne don haka sukaiwa mahaifin mu yan uwan shi na uba daya suka kashe muna shi kan dukiyan sa shine mafarin da mahaifiyar mu ta gudo damu zuwa nan lagos tun muna kanana basu san muna raye ba son kawai kada mu taso muce muna son dukiyan mu. Da yardan Allah zamuje muyi aiki sosai insha Allahu sai mun gano inda suka shiga maka da dukiyan ka su fito dashi idan mutum nason kansa da lafiya. Kodana gama magana na dago kallon da yake min na mamaki ne ya dan ban tsoro yace yes Sahiba na manta shaf da zaki iya sam raina bai kawo kan hakan ba da farko. Amma yanzu hankalina ya fara kwantawa sosai wallahi saidai kuma naji kin jefo min zancen sun kashe mahaifin ki akan dukiyarsa wanan maganan da gaske kuma haka yake ? Ban taba karya ba bazan fara ba yau abinda na fada ma hakan ne ya faru a gabanahaifiyata sukayi ta daba mai wuka har ya mutu su kuma suka handame dukiyan da baya. Yaya akayi kuka tsira nan ma na bashi labarin komai daya faru a lokacin kamar yadda naji umma tabawa daddy dasu ya modibbo labari a ranan. Shiru yayi ya zuba min ido yana kallo haka Yemisi ta shigo ta samemu kallona tayi kafin ta dauke ido ta mayar a kanshi tana mamaki. Zan iya shigowa tace tana kallon shi zaki iya mana ya bata amsa ko kinga wani abune ta dai nemi wuri ta kai zaune saida ta seta kanta ta fara maganan daya kawota office din. Nikan fita nayi na barta a ciki tana masa bayani aikina naci gaba dayi har ta fito tana dan watsa min harara a raina nace kinyiwa banza din ban san kinayi ba ma. Da dare bayan mun ci abinci na fara ba umma labari saicewa tayi ai sun rigaki zuwa nan sun rokeni da rana kuma na tausaya masa. Na nuna masa tausayi sosao kan hakan ubangiji Allah yasa hakan ya zamo silar fitan arzikin shi a gano inda suke a sanyayyena amsa da amin umma. Amma umma zuwan mu kaduna din ba zai kawo wani matsala ba tsakanin mu da yan uwa a can na tambayi umma din ina kallon fuskan ta. Sahiba aikine fa ya kaiki can ba wani shashanci ba sanan kuma kari da dadawa tare duk zamu tafi yadda sukai min bayani har Abdulhamid da iyalinsa meye na matsala a wanan kuma ? Wanan fa wani hikimane na ubangiji idan kin kula da hakan saidai kawai a barwa Allah nasa sanin yanzu don shi yasan abinda ya shirya ga hakan. Ba gidan kowa ko a karkashin wani zamu zauna ba kila har mamu kare wani baisan mun shiga garin kaduna din ba tunda ba sanin ki akayi ba a can dama. Dole muka fara shitin tafiya saidai umma ta dan koka da sana,anta saiga Abdulhamid ya kawo shawaran cewa kanin shine zaizo ya zauna tare da matarshi su kula muna da gida idan umma ta yarda sai a barwa matar shago su zauna muna. Yadda umma ta yarda da Abdulhamid ko dan uwantane ya tsaya a nan don haka a take ta amince da hakan. A shiga a fita kan tafiyan sirin namu ba tare da kowa yasab da hakan ba ranan mun kusa tashi aikine sai ga kiran oga ya samemu lokacin muda zamuyi tafiyan duk muka hallara . Office din yayi tsit kafin ya dago kai yace damu Alhamdullahi duk wani shiri ya kammala akan tafiyan mu din saidai matsalan daya fara hangowa a tsakanin mu yanzu kuma. Ba wani matsala bane sosai sao rashin hadin kan da babu shi a tsakanin yemisi da sahiba don haka zai iya kawo muna rashin nasara a can idan muje can muna hakan. Don hakane zai raba tun nan yemisi zata zauna kano tare da felix sai su zauna a can da sauri Filix ya dago kai yace ahh, why now oga ? Yace hakane zaman lafiya aida sauki don dole kamar a wuri daya ake tunda ba nisa sosai kuma a karkashin abu daya kuke dukan ku a can. Har ya kare zancen shi yemisi koni bamuyi magana ba an dai wayi gari kawai anga dukkan mu bamuzo aiki ba a ranan sai suka dauka mun fita wani aikine. Munyiwa kaduna shigan dare ne dukkan mu sai wanda yazo taron mu dinne ya dauke mu ya kaimu kwatas din a unguwar GRA. Tuncan kowa yasan nomban gidan shi don haka nuna muna kawai akayi nikan da umma mun tsaya addu,a hakama naga saura musulman sun tsaya addua. Amar tun shigan mu yake bin gidan da kallo yana fadin wai dama ace nan din shine gidan muna lagos daya dinga jawo abokan shi nan ai. Gidane madaidaici da dakuna hudu plat dai irin na zaman family din nan ginan shi maikyau an saka gadaje da kayan kitchen a ko wani gidan bamu da matsalan komai da zaman nan. Su Felix da jimo Adnan da Abdulhamid ne suka fara fita don ranan ni na tashi da ciwon kai ban fita ba ita kuma yemisi wai ta kwana gudawa. Zuwan su tare da gabatar da kansu a sabbin ma,aikata ya dan kawo tsegumi a wurin sosai hakan ya kawo cecekuce wai ya kwaso yarbawa daga kudu yanzu su zasuyi aiki a wurin kuma. A yadda suka dawo suna bamu labari komai na wurin ance ba tsaro mai karfi kamar yadda ya fada masu wurn ya samu matsala. Kwana biyu suna fita ga rana na ukune na samu fita duk da naso makaran fita din haka na shirya na daure na fita a cikin motan da sai ranan na fara shigan shi tunda aka ajemin shi a kofan gidan. Jikina yana saye da buje da rigan les pink maidan ado da blue din filawa sai gyalen dana saba saman kafada na da jakka shige da kayan. Kayan sun kara fito min da kyauna a fili sosai tun shigowana nake bin ko ina da kallo a wirin a daidai inda naga motar Adnan na parker nawa motan na fito. Na dan tsaya nayi nazarin wurin sosai sai hakan ya dawo da hankalin ma,aikatan dake waje a haraban wajen tafiya nakeyi a hankali ina waya da adnan dake min kwatancem wurin da zan samesu idan na shigo. Duk wanda na wuce ina jin abinda suke fada game dani wanan itama din tare da sabbin oganin take kai wanan yarinyar karama haka ? Kila dai ire iren yan matan su salman ne da suke daukowa aikun saba da ganin irin su a nan suna sintiri wani ke fadi. Na wuce kamar banji su ba saidai maganan ya tsaya min a raina lalai dole mu saka ido ga irin wa yam nan da suke maganan su din. Ina kaiwa tsakiyan wurin naja na tsaya wuri daya ina duban ta inda zaifito min sai gashi ya fito a sani dan karamin lungu yana min sannu da zuwa tare da nuna min hanya yana gaba ina binsa a baya na samesu a office din da suke ciki. Har gida taje takaiwa yayan nata dogon list din da uwar nata ta zauna ta tsara matashi waiduk abubuwan da takw bukatane duk. Duk daya gane sai ya karba yana fadin wai yan mata duk wanan ke kadai ke dashi da fatan dai kina iya amfani dasu bana son zancen daukan yar aiki ki zage kiyiwa mijin ki bauta ki samu ladan aure zaifi maki. Ta dan yi murmushi na yarinta tana kawar da kanta gefe daya tana dan jin kunyan abinda ya fada mata din mika mata takardan yayi
Chapter 165 · 0% Book details