← Book details Ana Dara Ga Dare Yayi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 284 OF 337

Sashe 284

Ana Dara Ga Dare Yayi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A hankali yake saukowa daga matakalan ya na tsikayo muryan mahaifiyar shi a waya tana yanka salati tare da fadin aure fa wani irin aurene haka kowa bai san da shirin saba ? Kafin ya karaso wurin yaji tayi shiru tana saurare wanda suke wayan dashi lokacin har ya iso ya zauna ba tare da yayi mata magana ba yana dan tunanen shi. Kalman data fada yasa shi dago kai da sauri yana kallon ta taci gaba da fadin dolema ai ita Sahiba din tasan da shirin auren ta dama sukaje can watau sun raina damu nan har zasu gwada muna mu bamu isa ba ko bamu kaiba. Da ansan abindata shirya ke nan da aiko su hamza din kada su tafi balle su dauki wanan rainin hankalin nata. Nina dauka a yanzu muna da kima da darajan da zata kawo miji nan a daura mata aure amma don ta gwada muna bariki auren ma a can saudiya zasu daura shi. Wai sahiba ce tayi aure kowa mami yake tambayanta da zalla tashin hankali a idon shi karara don wanan zuwan ya dawo da niyar yin yadda ya dace dashi da mahaifin shi koda mami din bata soba kuwa. Sai gashi tunda faran safiyan ranan da yake saka ran dawowan mahaifin shi suyi zaman karshe da mami din kan kudirin shi kunnen shi ya tareshi da wanan zancen a bakin mahaifiyar shi. Zubur ya mike yana fadin sahiba fa kika ce mami Sahiba din itace tayi aure a can saudiyan dama aure sukaje yi a can bata sanar da kowa ba sai kuma ya juya ya fita kafin ta bashi amsa. A rude ta kashe wayan tana kwals mashi kira saidai ko juyowa baiyi ba balle ya amsa kiran da take mashi da the boy boy fa dakai nake bakaji bane wai. Don sam ta manta da wani zancen so da yake min abaya motan shi ya nufa kai tsaye bai tsaya ko ina ba sai gidan ya Abubakar da yake zaton da sanin shi akai komai. Wanda baisan shima sai bayan daurin auren da baffah suka nuna isa sukai min ya samu labari ba duk da su baffah sun fada mai yadda zancen ya kasance amma yaji ba dadin rashin sanar mai da kuma rashin tambayan ra,ayina da basu samuyi ba. Don ya fada masu cewa su fara tambayana ra,ayina kan hakan da mahaifiyar mukhutar din tazo masu da bukatan tana son hadin iri a tsakanin mu dasu don abinda danta kawai zai muna ke nan ya rama halarcin mahaifin mu gareshi a cewan ta. Yace su tambayeni suji ra,ayina don yasan halina fiye dasu zan iya tara masu jama,a a can ayi yadda ba,a so a tsakanin amma kuma da suka zauna dasu umma sai a karshe shawara ya tsaya kan cewa gara dai ayi din kamar yadda suka bukata tunda su sun isar min ai suke gani. Da wanan shawaran suka tafi masalacin bada niyar daura aure a ranan ba amma sai kanin mahaifin shi mukhutar din dake cikin su yace ga sadaki gaba daya tunda suna wuri mafi tsarki a duniya a lokacin ai gara kawai ayi komai daga baya sai ayi duk shagalin da za ayi in an koma gida. Wanda ba bata lokaci kuma bayan idar da sallah suka gaiyaci mutanen dake wurin aka tsaya aka daura aure akan sadakin dubu dari kacal a musulunce. Horn ya dinga yi da karfi saida maigadin gidan ya fito a gigice yazo ya bude mai zan iya cewa wanan ne zuwan shi na farko duk tsawon zama shi dan uwan shi a lokacin baisan yadda gidan shi yake ba . Don abinda ke tsakanin su na rashin jittuwa da basayi ra,ayinsu yasha bambam dana juna a yanzu din ma magana yazo ya fadawa dan uwan nasa akan burin shi ya cika sai ya zuba ruwa a kasa yasha. Horn din motan yayi ta dannawa hakan yasa ya Abubakar din fitowa dagashi sai dogon jallabiyan dake jikin shi a lokacin. Yayi mamakin ganin Al, mustapha din gidan shi sam bai kawo akan wanan zancen yazo mashi gida ba a lokacin sai gashi yana dan kakaro murmushin dole a fuskan shi don ganin dan uwan nasa a gidan sa duk da baisan abinda ya kawo shi gidan ba lokacin yasan dai dole akwai wani dalilin zuwan shi gidan wurin shi. Haka ya karaso zuwa inda yake kokarin fitowa a cikin motan shi a fusace shima sai ya daure fuskan shi yadda ya ganshi din. Salamu alaikum ya fada tun kan ya karasa isowa inda yaken rike wanan salaman munafuncin nazo nayi murnane kan sherin da kake bina dashi. Har ya fito a fili haka kayi nasaran rabani da Sahiba a wanan karon saidai ba zaka iya raba zumuncin dake tsakanin mu ba ai. Kaifa baka da hankali duk da nasan ba yinka bane wata kila a buge kake ma yasa har ka fadi hakan in bashi ba nine zan rabaka da sahiba ko wanda ya aure ta a yanzu . Juyawa yayi ya kalli yan sandan dake kofan gidan suna gadi wanda suma din su suke kallo daga inda suke kafin ya juyo yana murmushi ya kalli dan uwan nasa yana fadin. Kaci arzikin a gidan ka na sameka da ba haka ba yau dana nuna ma dan drugs nake na gaske saidai ni shana ba kowa ne yasani ba ai don banyi shan da nake zuwa mashaya kamar na wasu tsofin a baya ba. Ido Abubakar din ya runtse tare da hade dantsen hannun shi kamar mai alaman shirin kai masa naushi a lokacin. Ashe kana da wanan labarin kaima saidai wanda ya fadama koya baka labarin cewa tare suke zuwa da manemin matan da har tsufa ya kasa daina gara wanda yayi da kurciya ya daina yanzu ai. Wa kake nufi da hakan ke nan yace wanda ka fada abokin cin mushen sa nake fada na kurciyan da sukai sha,shanci tare ya daina shiko yana ruwa har yanzun. Wani kallo ya kureshi dashi kamar zai dukeshi kafin ya kuta ya juya ya bude mota zai shiga sai kuma yaja ya tsaya yana fadin . Kaci bashin wanan kalman daka fada a yanzu sahibs kuma ka rubuta ka aje cewa saina aureta muddin ina raye. Shirme ke nan don a yanzu Sahiba tafi karfin ka fiye da yadda kake zato don wanda ya dauki garabasan ba sa,an jan wanda ma kake takama dashi bane balle kai a yanzu. Shima jan idon shi ya zubo mai kafin ya kuta yana kokarin murda key din motan ya kara fadin zancen bashi kuma ni Abubakar bana cin bashin kowa a rayuwa. Nan yaja mota a haukace Allah ya taimaka ba kura a gidan dake malale da inter lock a ko ina na haraban gidan daya bata mashi jiki a lokacin da kura. Binshi yayi da kallo tare da furta mahaukacin banza kawai da wofi ka dauka zaka zo min da hauka na kyalekane . Ya shiga ciki yana mai jin zafin kalaman dan uwan nasa a kansa inda yake nasa irin matakin da zai dauka kan mustapha din nan gaba da sai ya raina kanshi. Da sauri saurina dawo dakin mu don haka kawai naji jikina ya mutu kwanciya nakeso kawai gomama batayi ba na bi lafiyan gado tare da kashe wayana na kwanta sai barci. Can cikin dare ba mike na tashi ban daki na shiga na fito da alwala nazo duk suna barci basu san ma na falka ba a lokacin. Na dade zaune ina sallah a wurin kamar yadda na saba yi ko a gida tun lokacin dana samu dakin kaina ina yawan yawaita nafila da dare kamar yadda naga umma na yawan yi a baya can da muke kwana daki daya dasu. Har na idar na dan kishingida a wurin ina tunanen mafalkin da nayi har ya falkar dani lokacin ido na mayar na rufe saiga hawaye yana zubo min a hankali. Yauni da bansan Abbana ba a fili nice ke mafalki dashi har na samu albarka daga bakin shi nasan akan dai zancen yadda na dage na bankado asirin yan uwan shi har na ganshi a cikin mafalkin nawa na yau. Har lokacin da zamu tafi sallah yayi alam ya buga hakan yasa na dan dago na bubuga gado su faiza suka tashi mikewa nayi nima na kara yo alwala zuwa lokacin da muka fita gashi washegari zamu bar madina ina jin wani iri a raina wanda bani kadai ke jin wanan din ba lokacin. Munje an taso kamar kullun inda maza sukazo suna fadin mu shirya kayan mu karfetakwas na safe zamu dauki hanyar zuwa makka da faiza da fatima duk a kage suke aje makkan a lokacin. Kowa sai faman har hada kayan shi yakeyi lokacin su sister kamar yadda suke kiranta har manyan su suka shigo dakin namu. Kallon inda nake kwance ta fara yi tana fadin a, a ina dake akace za a fita yanzu kuma na ganki a kwance haka hankalin ki kwance. Tana kallona take wanan maganan idonta a kaina har ta zauna faiza ce take fadin wai dani take magana fa na dan juyo ina dan murmushi nake fadin. No bani ba sai kuma na juya da turanci ina fadin ba inda zan sake fita sau anjima idan mun fita sallah dai na fada ina gyara kwanciya. Kai matar yaya ba dai izza ba da takama kin kumayi dace kinzo inda ya dace zanso ganin ki keda Anty Battula a gidan ku. Waitin she talk na tambayi Faiza ina kallonta kafin takai ga ban amsa aka turo kofan umma ce ta shigo suka gaisa kafin ta juye min harshe da yarbanci tana fadin . Wallahi wanan tsohuwar ne tazo wai zata fita dake yanzu tana son zaki rakata zaban kaya a wani shago ki daure ku tafi kuma banda , , , Haba umma ga yayan ta nan ai babu zaben da bazasu iya ba daba sai naje bani nifa ban son shigewa mutanen nan na fada ina bata raina don Allah ya gani hakan bai mun dadi ba. Ki tashi kuje tunda ta roka dake zata tafi kina son in fada mata bazaki bane ko in mata rashin kunya kikeso nace ban yarda kije ba tunda kina yata.
Chapter 284 · 0% Book details