← Book details Ana Dara Ga Dare Yayi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 290 OF 337

Sashe 290

Ana Dara Ga Dare Yayi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ba yadda na iya don abu biyu zuwa uku na farko yin biyayya gun uwata sai nabiyu zanyi biyayya gun magabatana kamar yadda umma tace dani haka al,adasu yake gada na yarda na karya ga hakan sai kuma don ita mahaifiyar shi mukhatar din da sukace ta roki hakan kada in nuna bata isa ba a gareni. Gashi abu kadan zakaji tana faman yabon mahaifin mu ta mashi adduan samun rahama a wurin ubangiji duk muka hadu da fatan muyi koyi da irin halin mahaifin namu. Nima zan nuna mata yace kamar kowa zan nuna masu na gado mahaifin namu a wani fanni na rayuwa saidai kwakwalata da zuciyana ta kasa daina shi mukhatar din a wurin yaya nake ke nan ? Na gyara kwanciya badon naji dadin shi ba lokacin ina tuna irin alkawarin dana gama daukarwa iyayyena a yanzu suna saka min albarka. Akan wanan auren shina tuna na lumshe idona cikin takaici da kunan zuci ban taba kawowa kaina wani laluran aure ba a yanzu kusa. Asalima ban taba kallon wani da namiji naji ina son shi ba da sunan aure amma sai gashi kaddara ta a yanzu tazo min da abinda ban shirya mashi ba a lokacin. Hawayene masu zafi n aji suna bin fuskana a lokaci guda daidai lokacin da wayana sako ya shigo min ke nan ban yi yunkurin dubawa don yanayina daba dadi a lokacin. Jin sako na biyu ya kara shigowa lokaci guda yasa na dan juya ina kallon wayan nawa sunan ya Abubakar nagani rubuce ya turo min sakon. Nakai hannu na dauki wayan na bude gaisuwane tare ban hakkuri yana tausan zuciya na yarda da kaddara duk yadda yazo mi n shine cikan musulmi mutum na gari a wurin ubangiji yana da tabbacin mukhatar zai rikeni amana da mutunci kuma kada in yarda a samu matsala a bangarene har ya daukeni mara tarbiya. Baki na dan mere don jin kalamin shi na karshe don kaman yasan na shirya yiwa wanan mutumin daya biyo ta baya don kawai ya hadani fada da iyayyena a yanzu. Don haka na shirya rashin zaman lafiya ko kwanciyan hankali a bangarene da wanan mutumin da ya wuce sa,an aurena a yadda na dauka. Idan ma aurene sir Sha,aban nake iya aure a yanzu koda yin hakan ya taso min a yanzu idan banda zancen Alaja da ya bata min rai da dukkan su a yanzu. A rayuwa naki jinin kai min gori kan abin hannun ka ko wani abu daya shafi dai ka nuna abinka yasa nake tare dakai shiyasa ban shiga mutane don nasan mu ba masu shi bane sosai don haka daga aiki sai gida saiko wani wuri na musanman. Idan nace nayi barci a ranan karyane don haka ko da asuba da zasu tafi sallah ban bisu ba ganin haka itama fatima tace su tafi kawai ba zata tafi ba. Faiza da tafito ban daki ta samu fatima kwance take tambaya sai cewa tayi bazanje nabar anty sahiba a cikin wanan halin ba haka ku tafi kawai. Ita kuma sai tace a,a ku dai tafi nina zauna da ita zaifi zaman kike tace ba zan iya wuce na barku ba gaskiya gara dai mu zauba din dukkan mu a nan hankalina zaifi kwanciya. Duk sai sukaki fita karshe sai mama kudidine ta shigo tana fadin mufa ake jira a waje sukace su tafi kawai yau ba zamu tafi ba. Duk abinda sukeyi ina jin su amma ko motsawa alaman najisu banyi ba har mama ta fita daga dakin suma suka koma suka kwanta suna jiran lokacin sallah suyi a daki. Felix ne ya kira Sir Shaaban yana fada mashi abinda dake faruwa zaune yake tare da mahaifiyar shi da duk kwanakin suna dan sama sama da junan sune da shi da ita. Nan ya fara maimaita Sahiba fa kace tayi aure a madina yace kwarai Abdulne yake fadawa oga jimoh jiya da dare. Kuma ya turo mai photunan daurin auren a yau ya gani shike nan yanzu shike nan abinda ya fara fada lokaci guda. Wanda ba wani abu bane illa dabian su na yarbawa daya tsaya mashi a rai kuma ya rikeshi a gaskiya. Cewan da malamin shi yayi mai arzikin mu yana hade dashi idan muna tare zaiga arzikin shi yana bunkasa zaiga komai yasa a gaba zai sameshi a saukake zai zama mai albarka. Da farko bai dauki hakan gaskiya ba sai zuwan mu kaduna yin wanan aikin da kuma irin cigaban da yaga yana samu a yan shekarun nan . Sai ya dauki wanan zancen da gaskiya ya rikeshi a rai saidai bai taba fadawa kowa wanan zancen ba har ranan da ya samu labarin barina aiki dasu a lokacin hankalinshi ya fara tashi yazo kuma ya samu wai bana kasan tun lokacin hankalin shi ya fara tashi. Yanzu kuma ga felix yazo mai da wanan zancen yasan na salwanta daga gareshi ke nan na fita hannun shi haka yasa yana kashe wayan ya mike ya bar abincin dake gaban shi. Alaja da tadan fara saukowa ta bishi da kallo don ganin yadda lokaci daya ya shiga cikin rudani kuma gashi ya ambaci sunana a wayan. A lokacin ta dan mere bakin ta tana gyara zama sai kuma taga ya mike rai bace yabar falon Aisha ce tace dashi a, a brother why are you living now ? Tana fadi tana kallon abincin daya tashi ya bari a wurin ga mamakinta ko juyowa baiyi ba a lokacin balle tasa ran samun amsa a wurin shi dukko da hakan ba halin shi bane. Sai hakan bai kwanta mata a raiba mikewa tayi tabi bayan shi har dakin kwanan shi zaune ta hangoshi a bakin gado ya dukar da kai kasa kamar yana tunane mai zurfi hankalishi a tashe. Takowa tayi har zuwa bakin gadon ta samu wuri ta zauna a kusa dashi na tsawon dan lokaci kafin ta dauki hannunta ta dora a nasa tana fadin . Meke faruwane dakaine haka brother ta tambaya tana kallon fuskan shi hannun nata ya dan rike da karfi kafin ya dago kai yana kallonta da idanuwan shi da suka rine sukai ja don tashin hankali. Da sauri tace subbanallahi brother tell me please what is going on ko sahiba din ce ta kara jefa mai tambaya cikin tambaya. Murmushin dole ya dan kakaro a fuskanshi kafin yace sahiba ta tafi ta tafi daga gareni yanzu har abada Alaja taji dadi yanzu shike nan Aisha . Nasan daba don wanan matsalan nata da Alaja ba ba abinda zaisa sahiba aure a yanzu at dis time tayi surprise din mutane haka lokaci guda. Wai da gaske kakeyi miss Sahiba tayi aure at dis time da kafi kowa bukatan ta tare dakai kuma tayi ma hakan lokaci guda ? Idanuwan shi ya runtse yana fadin you can live now bana bukatan dogon magana a yanzu zata kara magana yace please Aisha live me alone. Jin hakan yasa ta mike tsam ta bar mashi dakin ko kallon Alaja dake zaune saman kujera mai zaman mutum ukku ta mimike tana waya tazo ta wuce ta. A zuwa lokacin yar nata laifin ta tagani don gani take itace taja komai a lokacin har hakan ya faru da dan uwanta ya rasani. Bin bayan yar tayi don tasan hakan sukan hade mata kai idan ta taba mutum dayan su sai dayan shima ya nuna bacin ranshi ga hakan shiyasa bata son wani matsala irin haka a tsakanin su. Bata san meyasa ba Sun kasa fahintar gata take son masu ko yaushe akan me zata yarda ya auro mata yar tallakawa a zuri,an ta. Sam bata yarda da hankalinta ta rabi talauci talakka banda wahala meke cikin hada halaka dashi banda tsiya don ko yayane dole dashi zasuti amfani su tofo suma. Da ace yarinyar dan wani hamshakine ko mahaifinta baida mukami zata iya yarda danta ya auri yarinyar don sahiba ba inda take da matsala banda na rashin background. Gwaggo harice zaune gefen daddy ranta a bace daddy din yai shiru yana kallon ta kafin ya furta kai yaran nan sun girma amma basu san sun girma ba su. Yanzu kema din ga irin abinda suka aikatawa jinan su na bace bace kina son ki aikata hakan a gabana da alama goyon bayan danki kike son nuna min don dole akwai abinda yasa modibbo ya fada mai hakan shima. Dama nasan haka zaka fada a karshe ba zaka dauki maganan da muhinmanci ba ai amma dama ai sai kuma tayi shiru. Kallonta yadan yi kafin ya mayar da jikinshi saman kujera ya dan shafo goshin shi yana murzawa kafin ya mika hannu ya dauki waya. Danshi ya kira yace a takaice kazo yanzu kome kakeyi ka barshi kazo yanzun nan daga bangaren modibbo din yake tambaya lafiya dai daddy ? Lafiya ke nan kazo yanzun nan da sauri ya mike don cika umurnin mahaifin nasa cikin yan mintuna ya isa gidan saidai tun daga nisa ya hango motan gwaggo hari a waje alaman tana gidan itama a lokacin. Tambayan kanshi yayi meke faruwa hakane wai ko a kan zancen auren sahiba din ne sukaji hankalinsu suma ya tashi da hakan. Da sallama ya turo kofan falon ya kai kallon shi ga iyayyen nasa biyu dake zaune a lokacin yanayin su ya kalla ya gano ba lafiya a wani bangare. Daddy lafiya ya fada tunkan ya zauna samu wuri ka zauna ya fada yana nuna mashi da hannun shi ya kalli wurin yakai zaune a hankali ya kara maimaita tambayan shi wanan karon gun gwaggon nasa. Dake zaune tana cika tana batsewa don yadda take jin kanta lokacin jin tambayan daya jefo mata yasa ta dan harareshi tana fadin. Kaji mun mara kunya sakon daka bayar ne ya sameni yasa nazo gun mahaufin ka tunda nika rainani a yanzu har zaka iya fadawa boy wanan maganan ido da ido. A, a gwaggo Allah ya baki hakkuri amma shi mustapha din ai ya fada maki dalilin fadin hakan danayi ko ? Me zai fada min bayan wanda kake ganin yanzun wuyan ka yayi kauri kai ka isa zagin mu a yanzu akan Sahiban banza wace , , , , A, a hari me kuma ya kawo zacen sahiba a yanzu nan
Chapter 290 · 0% Book details