← Book details Ana Dara Ga Dare Yayi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 74 OF 337

Sashe 74

Ana Dara Ga Dare Yayi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Baya nayi tangal tangal zan fadi Allah ya kareni na cire jakar dake goye a bayana na kalleta ina huci nace why u de push me like dat ? I push you , why the you beat her ? you want to kill her or what ? Me i no go kill any body, na ur daughter de abuse me, na yin i beat her , whu u no ask her wetin she do for me. Wanan yar iskan mai suffan kafirai sai nayi maganin ki gidan nan zaki shiga taitayin ki dani wallahi. Na ce me i no hear u ask ur daughter first wetin she for me daga bayana naji ana fadin hey daughter why do you beat her she is your sistee now. Hjy karima tace can dai gasu gada Allah ya tsari diyana da hada jini da wa yan nan matsiyatan da aka kwaso muna a gida. Haba dai hjy karima zaki raba tsakanin su ne suma din ai yan uwan sune na jini daya. Hannu ta daga tana fadin hjy ya isa haka ni dai na fadi a daina hada min diya da kalan dagi idan kuma ta kara dukan min ya sai nayi mata bugun a kawo ruwa a gidan in rama mata. Na nuna kai na tare da daga hannu na nayi round dashi na kada ina fadin god forbid wallahi omale, every day she de call us with cin arziki walahi talayi if she repeat dat neme for us again i go break dat her tieni leg before we come back. Sam ban kula da kowa na gidan yana waje a lokacin sun fito ba gaba dayan su sai umman mu data sha magani take barcine bata san da hakan ba. Sahiba naji muryan ya Abubakar ya fada a tsawace yasa na dan dago na kalli inda yake tsaye shida daddy din suna sauraren mu nace . Nace broda na dis woman come push me for notin, nd she is abusue me, bcos her daughter de call us wit cin arzki, nayim i beat her, she come dey cry, her mama come dey block de road for, i come de inter nayin de woman push me back, Karima ba yarinyar nan hanya ta wuce daddy ya fada yana kallon ta ido da ido tace au kama mara mata baya ke nan tayi iskancin data koyo acen ke nan ? Bata hanya ta wuce nace dake ko kuwa ta wani irin jan hannun yar ta suka shige tana fadin wallahi da sake don ba zan yarda da wanan iskancin ba. Juyawa nayi wurin daddy na dan rusuna nace tank u uncle ya daga hannu yana fadin dont faith next time nace yes sir nashige ciki Amar ma yabi bayana. Kai ya Abubakar ya girgiza yana fadin wanan baku san ko waye ita ba a wurin dabamci da kowa ya kama kanshi da ita a gidan nan . Yarinyar da gaba daya lagos kaf tasan shi sai ta zagaye shi da kafa fada a wurin ta kamar shan ruwa ne ita. Daddy daya juya yake fadin dole tayi tarbiya sai namiji duk kokarin uwar ba zata iya bata tarbiyan da namiji zai iya bata ba ai. Da sannu da lalami zata koya a nan insha Allahu wata rana hakan zai zama tarihi a gareta sai ka fara shirin koyar da ita hakan a yanzu. Hjy Addah kan mutuwan tsaye tayi a wurin tana kallon ikon Allah ga yar dan uwanta dake tujara haka a gaban kowa duk dani ina ganin ai nayi masu mutunci tunda na tsaya nayi warning din ta ban makale mata a jiki ba. Mun shiga mun samu umma a kwance falo muka tsaya na debe uniform din dake jikina wando da riga sai dan hijab din da ya zama mun alkakai don debeshi nakeyi idan mun fita tunda ban saba saka hijjab in dade haka ba sai idan zanyi sallah nake sakawa . Abinci na zubawa Amar ya zauna yana ci sai ga Amira ta shigo dakin namu da takardan ta a hannu tana assigment din da aka basu. Kwanciya yarinyar tayi a kasa ties ta kifa ciki ba wanda yai mata magana a cikin mu har lokacin nima dai a karshe hankalina sai ya dauku ga tunanen kalman da hjy karima ta fada game da mu da zata shiga gida. A fuskana yarinyar ta manna min littafin nata tana inyi mata in koya mata mana sai yarinyat ta ban tausayi na shiga koya mata tana ganewa. Nemanta akeyi a cikin gida ta ko ina duk uwar ta tayarwa mutane da hankali daddy da ya Abubakar dake alwala a waje har baya sukaje wurin tankin ruwa aka duba ciki babu yarinyar uwar ta kara tayar da hankalinta sosai. Daga karshe sai ga yarta ta bude kofan mu ta gamu zaune tare muna cin abinci gs littafi a gefen mu muna assignment din a ciki. Juyawa tayi ta koma da gudu ta na fadin mami ga Amira can daki ita da yan cin arziki suna cin abinci ana mata assignment din ta a cikin zabura uwar tace ina ? Daddy yaja wani irin tsoki yana fadin shirmen banza shirmen wofi kinbi kin tayarwa mutane da hankali haka kince kin duba cikin gida ko ina. Har ya juya zai bar wurin ya juyo tare da kiran sunan yarinyar da humaira idan naji kin sake kiran yaran nan da yancin arziki a gidan nan sai na bata maki rai. Arzikin da uwarki ke fadin anzo ci a wurin ubanwa na same shi kije ki tambaya wanda duk ya fada maki da kikirasu da hakan ni ubanki nace arzikin su nake ci har ku a gidan nan yanzu. Wurin gaba daya yayi tsit kowa na kallon daddy din da mamaki jin abinda ya fada tundai ita hjy karima din daddy yaci gaba da fadin. Da arzkin uban su na samu aikin da nayi a baya da nasa kuma har na fara business din da nakeyi yanzu don haka ke dasu fada min waye dan cin arziki a cikin ku yanzu ? Don haka wa yan nan yaran sun wuce a raina su a gidan nan musan maku da mahaifin ku ya daukeku kamar diyan cikin shi da ya haifa son yai min duk wani abu da dan uwa zaiwa dan uwan sa a rayuwa ke Addah kin sani idan su basu sani ba ai. Don haka ku girmamin yaya don ko shi ke raye na barku haka zai muka baku maraici da rashina a duniyan nan nasani. Daga haka suka bar wurin zuwa sallah ya Abubakar ya bin shi a baya zuwa masalaci unguwar da suke sallah. Jikin kowa yayi sanyi haka suka kwasa suka koma cikin gida kowa da zancen daya tsaya mai a zuciya shi suka shige part din su. A part din hjy Addah Nabila ce ke fadin yau wanan yarinyar ta mun daidai jifa yadda tayiwa anty a gidan nan. Sauran ma suka dauka da hakan muma ai tayi bala,in ban mamaki ke bakiji abinda yaya ya fada ba cewa yar geto ce ita ta iya dabanci kamar tsiya. Hjy ce daga kofa take fadin meye abin burgewa ga yiwa babba rashin kunya irin wanan amma mommy ai ita akan gaskiya ta fadi magana ba tsoro dole anty ta koma baya tayi shiru. Ina zata iya da wanan yar tsatsaye take fa dagani saura kiris ta iya sheke koma waye ya taba ta . Wai mami mai daddy ke nufi da cewan da yayi yaran nan suke da arziki hjy ta juya tana fadin kya iya zuwa kin tambayeshi a waje . Tafice ta barsu suna magana a kai kona fadin abinda ya fahinta kan zancen mahaifin nasu har suka gaji suka watse zuwa sallah. A dakin mu bayan mun gama umma tace muyi sallah la,asar yayi na idar na fito na samu Amira din tayi barci daykata nayi na dora saman kujera saboda sanyin ties na kwanta a kasa din ni sai barci. Anty ta shigo dakin da kanta ta duba don jin yarinyar shiru da tayi ta samu munyi barci sallaman ta da umma taji yasa ta ta fito falon daga ciki uwar daka tana amsa mata. Wanan nazo duba ta nuna yar nata a cikin murmushi umma ke fadin tayi barci sun gama karatu da yar uwan barci kuma ya dauke su zata dauketa umma tace aiki barta idan ta falka sai a kawo ta. Anty din bata so hakan ba son bala,in haushin mu da take ji a lokacin ta juya ta tafi bata ce komai ba umma ta tsaya tana kallon ta cikin mamaki. Kafin ta juya zuwa cikin dakin sai gab da magariba ne muka falka wanka nayi wa yarinyar nima nayi na shafa mata mai sai na riko hannun ta zuwa part din su duk ban taba shiga part din kowa a gidan ba. Don mun kasa sake jiki da kowa damama ni shi Amar ko banza haka yake baida sakewa ko kadan da mutane kullun yana daki ne. Nayi sallama tare da fadin gata nan barci tayi a aurin taje yin assignment a lokacin ina fadan haka na juya na bar part din na dawo namu. A ranan daddy sunyi fada sosai da anty a kan mu tace wai ya kunyatata a gaban iyalin shi yace a kan yaran nan idan kince zaki matsa masu a gidan nan zan iya maki abinda yafi wanan din ma nan sukai ta musayan yawu dashi har ya gaji ya kyaleta. Washe garine umma taji abinda ya faru a wurin hjy data shigo su gaisa umma tace a bata hakkuri sahiba fada ke gareta itama wanan halin yana damunta dani ai. Na fito na samu hjy da umma a falin a cikin shirin makaranta na suka har kasa na gaida hjy din kamar yadda umma tace mu rika gaidasu. Bayan ta karba ne ta fara min fada kan abinda nayi a jiya din tana fadi ita sin ai matar mahaifin mune udan ina haka shima ba zaiji dadin hakan ba ai. Shiru nayi banyi magana ba saidata gama na mike tare da fadin thank you ma na kalli umma ina fadin zan tafi umma ta juye baki a cikin yarbanci tana min fada akan kada na
Chapter 74 · 0% Book details